← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 197

Sashe 34

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun akan hanyar komawar Alhaji gida ya gama yanke shawarar matakin da zai ɗauka kan hakan, bayan ya isa gidan a falon shi ya kira Hajiya Aisha, tun da ta kalli fuskarshi ta fahimci akwai damuwa tare da bacin rai tattare da shi, ta shiga tambayar shi abun da ke faruwa, duk abun da suka tattauna da malam Liman ya sanar mata, anan ya ce mata ya gama yanke shawarar matakin da zai dauka, shine zai maida Safiyya ƙasar Turkey can wajen yayanshi dake zaune acan yana aiki da kasuwanci, sam hajiya bata ja da shawarar da ya yanken ba, don tun farko dama can ya so ya tura Soffyn ta yi karatu ita ce ta roƙe shi kan ya ƙyale ta ta yi karatun ta anan ta nuna bata son ta yi nesa da ita, to shima da yake bai cika son yaranshi su yi nesa da gida ba hakan yasa a lokacin ya ƙyale ta, fatan Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi ta yi ya amsa da Amin. A daren ranar ya kira Soffy ya sanar da ita kan ta fara shirin tafiya Instanbul a can zata ci gaba da karatu, ta ji ba daɗi amman bata shiga damuwa ba sosai saboda gidan yayan mahaifin nata dake can tamkar gida yake a wurinta, shima yana da yara har da sa'ar ta da suke ƙawaye, sannan kuma akwai ɗan shi Lukman da suke cikin yin soyayya da juna. Lokacin da Jameela ta ji zancen tafiyar Soffy ba ƙaramar damuwa ta shiga ba, saboda ba ƙaramin amfanuwa take da ƙawancen da suke ba, sannan kuma sun saba sosai da juna don tun suna yara suke tare, a lokacin ta ji inama ta bita ƙasar wajen itama sai ta ci gaba da karatunta na shiririta a can, sai dai ta san hakan ya fi ƙarfinta don ko cikin samarinta bata tunanin akwai wanda zai iya ɗaukar mata nauyin hakan, dama honorouble ne mai sakar mata bakin aljihu yadda ya kamata, to shima a lokacin ya ɗan ja mata baya tun da ya ce mata baya son tana kula samari sai shi kaɗai amman ta ƙi bin umarnin shi.

Bayan tafiyar Soffy haka Jameela ta ci gaba da shiririta a wurin karatun ta don saima abun da ya ci gaba. Ana haka ne su Ibrahim wato mahaifin Deen suka zo biki Kano, a lokacin bikin yayan abokinshi Maleek mai suna Saleem, wanda asali suma Maleek ƴan Funtua ne amman a kano iyayen su suke zaune, sai dai basu cika zama a Kanon ba suma sun fi zama a ƙasashen waje saboda irin aikin iyayensu ɗaya, dalilin ma da ya haɗa iyayen nasu kenan har suke abota suma kuma yaran nasu suka zama abokai, kusan duk sun zauna a ƙasashe guda kuma tare suka yi karatu tun suna yara, hakan ne ya sa Ibrahim bashi da babban abokin da ya wuce Maleek, shima Sa'ad abokin Saleem ne wanda suka zo bikin shi.

A ranar da za a yi dinner party lokacin Jameela ta zo duk da gayyar soɗi ta zo don bata haɗa komai da masu bikin ba, wata ƙawarta ce ƴar jami'arsu ita ce ƴar'uwar su amaryar shine ta biyo ta, a wurin dinner ɗin idan ka ga Jameela bazaka ta6a yin tunanin cewa bata haɗa komai da masu bikin ba, yadda ta ci uban gayu zaka ce bikin nasu ne don har da su anko ta yi har ma tafi ƙawartata da ta biyo iya yi, ba ƙaramin jan hankalin samari ta yi ba a wurin kamar dai a kowane biki da take zuwa. Tun da Ibrahim ya ɗaura idanun shi akanta ya ji ya kamu da tsananin son ta, sai da ya yi yadda ya samu yin magana da ita tana ta faman yauƙi kai ka ce ɗiyar uban wani ce, ba tare da 6ata lokaci ba ya bayyana mata shi dai ya ganta kuma ya ji ya kamu da sonta, a nan ya bayyana mata kan shi da kuma alaƙar shi da masu bikin, ai fa tana jin cewa ba zaune suke a ƙasar nan ba ya ja hankalinta har ta saurare shi sosai musamman da ta ga tare yake da ƙanin angon wato Maleek, kuma dama ta fahimci angon ɗan masu arziƙi ne daga yanayin shi da dangin shi. Bayan gama dinner din ya amshi lambarta ya ce washe gari zai zo gidansu su gaisa da iyayenta, gudun ya je ya ga gidan su yasa ta ce mashi ya bari ai zata zo wurin bikin gobe sai su haɗu, duk yadda suka so su maida ta gida bayan gama dinner ɗin sai da ta zille masu.

Washe gari don ƙarfin hali sai gashi ta je gidan bikin, anan suka sake haɗuwa da Ibrahim har ya nuna ma yayanshi Sa'ad ita matsayin budurwar da ya yi, ya so ma ya kai ta ta gaisa da hajiyar su amman ta ƙiya ta nuna mashi ya yi wuri da yawa, har kusan magrib ta na nan, a motar Maleek suka ɗauke ta da za a tafi kai amarya. A ranar duk yadda ta so ta zille masu ta kasa, su suka ɗauke ta don maida ita gida, tana ta zullumin kada idan suka ga gidansu ya guje ta, wannan tunanin ya sa ta yanke ƙin kai su gidan su, a bakin gidan su Soffy ta sa suka ajiye ta ta ce masu anan take da zama amman ba nan ne ainihin gidan su ba, saida suka so ta shigar da su don su gaisa da mariƙan nata amman ta ƙiya, ta yi masu ƙaryar babanta mai ruƙonta baya barinta kula samari su bari daga baya zata yi masu hanyar da za su gaisa.

Bayan gama bikin da kwana biyu a ranar da za su koma Funtua ya buƙaci yana son su haɗu, a wani haɗaɗɗan wurin cin abinci ta yi masu mahaɗa, a nan ya sanar mata shi fa son ta yake da aure, idan ta amince yana komawa gida zai sanar da iyayen shi, ya ce mata so yake kafin su bar ƙasar a gama magana tsakanin iyayen su, tabbas ta ji tana son shi da aure musamman kuma saboda ya tafi da ita ƙasar waje kamar yadda ƙawarta Soffy ta tafi ta barta, lokaci guda ta ce ta amince zata aure shi.

Bayan komawar su Funtua ne ya yi ma hajiya maganarta tare da nuna mata hoton ta a wayar shi, ta tambaye shi game da iyayenta, ya ce bai san wanene mahaifinta ba amman ɗan'uwan mahaifinta ne ke ruƙonta, har ya sanar mata cewa yayan shi Sa'ad ya ganta har sun gaisa, a lokacin nuna mashi ta yi shi da yake son ci gaba da karatun shi kuma ya zai kawo batun aure, ba kunya ya nuna mata ya canza ra'ayi saboda yana son yarinyar idan ya aureta ya ci gaba da karatun, hajiya ta yi mamakin yadda ya kamu da son yarinyar lokaci guda, ta ce mashi ya bari zata yi magana da mahaifin su. Bayan sun tattauna da mahaifin nashi ne suka sanar da shi cewa sai sun fara yin bincike game da yarinyar kafin akai maganar aure. Lokacin da ya sanar da Jameela hakan hankalinta ya tashi har ta yanke faɗa mashi gaskiya cewa ita fa ɗiyar talakawa ce, ya bata amsa da shi ai ita yake so ba wani abu ba don haka ba ruwan shi da hakan, ta ji daɗi sosai don bata fatan a ce bata aure shi ba, ta samu Ammin su dama tuni ta sanar mata game da Ibrahim, cike da damuwa ta sanar mata yadda suka yi da shi na cewa za ai bincike akanta, ta ce ita tana tsoron su yi binciken a faɗi masu wani abu da zai sa su ƙi yarda a yi auren, Ammin ta so ta ja ra'ayinta kan ta haƙura da shi kawai, amman Jameela ta nuna ita gaskiya tana son shi da aure da kuma manufarta na auren shi, jin hakan ya sa Ammin tana sakin shu'umin murmushi ta ce mata kada ta damu su yi binciken tana tabbatar mata ko sun yi ba abun da za su ji da zai sa a fasa saidai ko don saboda su talakawa ne, sosai Jameela ta ji daɗi don ta san wacece Ammin su a 6angaren hatsabibanci ga bin bokaye, ko farin jinin samarin da suke da shi ba haka nan bane. Mahaifin su Maleek wato Alhaji Usman Karaɗuwa shi daddyn su Ibrahim ya tuntu6a da maganar ya ce yana son ya saka a yi masu bincike game da yarinyar, da yake abu ne na manya ba 6ata lokaci ya wakilta wani kan hakan, bayan an tambayi Jameela ta faɗi sunan unguwar da take da kuma mahaifinta.
Chapter 34 · 0% Book details