← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 197

Sashe 26

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gama Basma ta kwashe mugs ɗin da suka yi amfani ta je ta saka a wani injin dake a wurin wanda ke wanke maka kayan da aka yi amfani fess, ta maida su wurin ajiye su sannan ta dawo, Maleek ya ce ma Sapnah su je su raka baby part ɗinta ta amsa da ok, kafin su tafi ta hanyar wannan glass table ɗin ya rage hasken gaba ɗaya cikin falon zuwa mai duhu ya kuma gyara duka labulayen falon, abun dai kamar siddabaru! Kamar lokacin da za su zo yanzu ma saka Basma tsakiya suka yi suka kama mata hannu, lokacin da suka fara hawa matattakalar benen sai ma suka ɗaga ta sama ba tare da tana taka steps ɗin ba, Basma nata ƴar dariya suma duk ita ce akan fuskokinsu har suka haye da ita sama, kana ganinsu ka ga happy family, ɗakinta dake a saman benen suka kaita wanda shima yake da zubi irin na zamani, an tsara shi da tsadaddun furniture daidai da matashiyar budurwa, har saman gadonta da ya sha lallausar shimfiɗa suka kai ta tare da kwantar da ita, gaba ɗayansu suka yi mata addu'oi kafin duk suka sumbace ta a goshi suka yi mata sai da safe, tana murmushi ta furta, "Gud nyt mom, gud nyt dad, I luv u so muchhh." Hannunta Maleek ya kama ya sumbaci bayan shi ya furta, "We luv u too, our happiness." Ya ɗan kanne mata ido, sai da ya rage mata hasken ɗakin daga mai haske zuwa mai duhu kafin suka fita suna yi ma juna bye-bye, tana ganin sun tafi ta ɗago ta kai hannunta saman side drawer ta ɗauko wayarta don ta duba ta ga ko Deen yana online. Su Maleek na fitowa daga ɗakin nata ya duƙa ya ce ma Sapnah ta hau, dama duk zai ɗauke ta ya fi goya ta, don a cewarsa ƙirar jikinta ta saka ta yin nauyi, tana dariya ta kuwa haye bayan nashi, a tunaninta za su koma ƙasa ne sai ta ga ya wuce da ita part ɗinsa dake a nan saman benen don duk suna da part a nan, har Deen ma a nan saman part ɗinsa yake a gidan. A can hawan ƙarshe kuma ba ɗakuna bane, anan akwai Home Cinema wato babban wurin yin kallo kamar gidan kallo, an saka babban screen a jikin bango da manyan kayan sauti, akwai kujeru masu motsi dake ɗauke da wurin ɗaura kofin abun sha, akwai kuma Entertainment Zone wanda ɗan madaidaicin wuri ne don yin game, bayan su akwai kuma Mini Lounge inda ke da mini bar an saka glass shelves masu ɗauke da drinks kala-kala, Sai Relaxation Spot wanda area ɗin balcony ne aka yi ma ado ta hanyar zagaye sa da glass, akwai kujeru da table masu matuƙar jan hankali da fulawoyi masu tsari. Musamman akwai glass elevator da ke kai mutum can sama ba tare da an sha wahalar taka matattakala ba. Tabbas gidan Maleek ya amsa gidan mammalakin kamfanin fasaha, abu mafi ƙayatarwa shi ne yadda aka haɗa duk na’urorin gidan da smart home system, ta yadda ake iya sarrafa su ta amfani da murya ko kuma ta wayar hannu.

Ganin sun nufi part ɗinsa, Sapnah ta tambaye shi ba aikin zai je ya ci gaba da yi ba, ya ce mata bai son shiga haƙƙinta su je ya sakata ta yi bacci idan ya tashi da dare zai ci gaba, ba ƙaramin daɗin hakan ta ji ba ta lafe a bayansa sai ka ce wata ƙaramar yarinya, koda yake gaba ɗayansu basu ɗaukar kansu a masu shekaru wurin nuna ma juna soyayya, a koda yaushe soyayyar su ga junansu sabuntuwa take yi kamar dai yadda ma'aurata turawa suke, yawan shekaru baya hana su nuna ma juna soyayya.

Maleek mutum ne mai tsananin bawa iyalinsa kulawa tare da ƙoƙarin sauke masu hakkokin su duk da kasancewar sa mutum da yake yawan kasancewa busy. Sai dai ba iyakar iyalinsa kawai yake kyautata mawa ba, shi mutum ne mai tsananin alkhairi ga mutanen dake kewaye da shi, waɗanda ya sani da ma waɗanda bai sani ba alkhairinsa na isar masu, kamfaninsa na ɗaya daga cikin manyan kamfuna dake bada gudunmawa da tallafi a ƙasar, haka ma a Nigeria, yana ɗaya daga cikin mutanen da ake neman tallafi a wurinsu idan buƙatar hakan ta taso, kamar 6angaren gina makarantu, masallatai, hanyoyi da sauransu. Da zarar ƙafarsa ta dira a garinsa wato Kano, mutanen unguwarsu suke cika da farin ciki sanin cewa suna cikin alkhairi dumu-dumu, sannan duk da kasancewarsa mai tsananin arziƙi da yawan uzururruka hakan bai hana sa kula da addininsa, yana da ruƙo da addini sosai, a duk daren duniya indai yana da ƙoshin lafiya sai ya yi ibadu, a ganinsa in dai zai rinƙa tashi yana yin aiyukan da suka shafi aikin sa to ba shi da uzurin da zai hana sa yin ibada, wani lokacin sai ya gama yin ibadunsa sannan ya dasa da aiki, ko kuma bayan ya gama yin aikin, haka iyalinsa ma yana matuƙar ƙoƙari wurin saka ido kan abun da ya shafi ibadarsu.

ABUJA

A zazzaune suke a dining area suna yin breakfast, gaba ɗaya sun shirya dad ɗinsu na sanye da ƴan cikin manyan kaya na light blue ɗin shadda, babbar rigar su na can part ɗinsa sai ya gama in zai tafi aiki zai saka, a sauran kujerun su Leemarh ne da ƙannanta duk sun shirya cikin uniform don tafiya school, babu Omar a ciki don shi ba in da za shi ba da wuri zai yi breakfast ɗin ba, mom ɗinsu ma na zaune jikinta sanye da baƙar abaya mai buɗaɗɗan hannu ta yafa ƙaramin mayafin rigar a saman kanta, itama lokacin zata karya don zata fita da wuri ne zata je yin wani uzuri. Dama kuɗin da ta amsa jiya a wurin daddynsu ƙarya take ba wani Ammin su da zata tura mawa don buƙatar kanta ne ta amsa, ba a daɗe da ta sa ya bata miliyoyin kuɗi ba wai zata ƙara ma zinaranta girma, shiyasa yanzu ta fake da Ammin su na da buƙata.

A natse suke cin abincin an shaƙe tebur ɗin da kayan breakfast kala-kala, wanda duk cin su baza su iya cinye su duka ba, Leemarh tana cin abincin amman hankalinta na kan Fahad ta ƙosa ta saka shi a idanunta saboda ba da su suke yin breakfast ɗin ba, saboda an san ya yi wuri da yawa shiyasa ba a yi masu maganar su fito su yi breakfast ɗin ba, daga gefen su masu aiki biyu ne a tsaye suna serving nasu abun da kowa ke so.

Leemarh ce ta fara miƙewa ta ce ta ƙoshi, tana barin wurin ta nufin hanyar bene tana sanye da ɗan gajeran skirt da iyakar shi gwiwa na kayan makaranta, sai doguwar farar safa data kawo har bakin inda skirt ɗin ya tsaya, ƙafafunta na sanye da rufaffun baƙaƙen takalma na makaranta masu ɗan karen kyau, kanta na sanye da ƴar hijab himar sosai kayan suka yi mata kyau sai faman sakin kamshi take, lokacin da ta isa bakin bedroom ɗin ta tsaya ta yi sallama, sai dai kusan sau biyar tana yi shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta yanke ta leƙa ta gani ko basu tashi bane, bin ɗakin ta yi da kallo da ɗan alamun mamaki lokacin da ta hango gadon wayam ba kowa, sai dai alamun ba a daɗe da tashi daga sama ba don zanen gadon da duvet ɗin a ɗan yamutse suke, ƙarasa shiga ta yi tana tafiya a hankali kamar mai yin sanɗa tana bin cikin bedroom ɗin da kallo, a tsakiyar ɗakin ta tsaya tana yin ƴan waige-waige ko zata hango wani cikin su, har can ciki wurin closet ta duba amman bata gan su ba, har bakin toilet ta tsaya tare da ɗan yin knocking nan ma shiru bata ji alamun mutum ba, hanyar fita ta nufa a cikin ranta tana mamakin to ina suka tafi da sassafen nan, bayan ta fito falo har ta nufi ƙofar fita ranta ya bata to ko suna a sashen baƙi? Yin wannan tunanin ya sa ta juya da sauri ta nufi ɗayar ƙofar da zata sada ka da bayan gidan wanda ta nan ya fi kusa da sashen baƙin, lokacin da ta je a rufe ta iske part ɗin alamar ba kowa a ciki, komawa ta yi cikin gidan tana ta tunanin ina suka tafi, bayan ta shigo ciki hanyar dining area ta nufa har lokacin suna a zazzaune basu ƙarasa yin breakfast ɗin ba,

"Mom, wai ina su ya Deen da ya Fahad suke?" Ta tambaya bayan ta tsaya daga gefen mom ɗinsu, ba tare da ta kalle ta ba hannunta riƙe da tea cup tana sipping ta ce Deen ba yana a part ɗinsa ba,

"To ai yanzu daga can nike amman ban iske kowa ba, har cikin bedroom na shiga nan ma wayam ba su nan." Dakatawa mom ɗin ta yi ta kai idanunta kan ta, "To ina Deen ɗin zai tafi da sassafe?" Hannu Leemarh ta yarfa mata alamar itama bata sani ba, shiru mom ɗin ta yi alamar tunani, a ranta ta ayyana ko saboda maganar da ta yi ma Deen ya sa shi jan Fahad suka koma bangaren baƙi, kallon Leemarh ta yi ta ce tana jin Deen ɗin yana a part din baƙi, yadda take ba Leemarh amsa sam bata sakawa da Fahad sai ka ce ba su biyu ta tambaya ba,
Chapter 26 · 0% Book details