Sashe 72
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Aliyu shima irin group ɗin jininsu ɗaya. Ba tare da ɗaukar lokaci mai tsawo ba su Sagir suka zo a saman mashin ɗin Aliyu, bayan an duba jininsu zai yi aka ɗiba aka saka ma Habu, daga baya su Sagir suka tafi Salma kuma ta zauna da shi. Bayan komawar su Sagir ya je ya sanar ma innarsu Habu halin da ake ciki don bata da waya, ba a ɗau lokaci ba suka isa asibitin ita da baban Habu, bayan ganin ɗan nasu nan suka shiga yi ma Salma godiya suna saka mata albarka tana ce masu ba komai, bayan an kira sallar la'asar baban Habu ya tafi yin salla, da zai dawo ya taho ma Salma da chin-chin da ledan zobo guda biyu, da murmushi ya ce mata, "Ƴata Salma ga wannan ki ɗan ta6a ba yawa dai." Tana murmushi ta ce masa ba komai ai bata ma jin yunwa, matsa mata ya yi saida ta amsa, cin-cin ɗin bai wuce biyu ta ci ba da zobo ɗaya, ta miƙa ma Innarsu Habu sauran ta ce ta ci, "A'a Salma, baki ganin daga gida nike ke kau kin sha zama, don Allah ki ci." Ta faɗa tana murmushi, magiya Salma ta shiga yi mata kan ta amsa ta ci ta ce itama bata jin yunwa tana gama cin abinci ta kawo Habu, amsa ta yi da Salma ta matsa mata, dama baiwar Allah yunwa nata nanuƙarta saboda ba su ci abincin rana ba, babansu Habun bai daɗe da ya samo abun da za su dafa ya kai masu, lokacin ne kuma su Sagir suka je suka sanar da su halin da ake ciki, haka ta taho ba tare da an gama abincin ba, bayan ɗan lokaci baban su Habu ya tambayi Salma abun da aka kashe a asibitin, tana murmushi ta ce masa ai innarsu ce ta bada kuɗin kyauta ta kawo sa, ba yadda bai yi ba ta faɗa masa kuɗin da aka kashe ta ƙiya, ta nuna masa ragowar kuɗin dake a hannunta ta ce masa bama a kashe duka kuɗin ba akwai saura, jiki a sanyaye ya yi mata godiya, dama ƙarfin hali ne kawai ba wai yana da kuɗin ba kawai ya sa ran duk inda zai samo kuɗin zai nemo. Saura kaɗan ledan jinin da aka saka ta farko ta ƙare kawai suka ga Habu ya fara wata irin jijjiga, a ruɗe gaba ɗaya suka zagaye gadon suna tatta6a shi tare da kiran sunansa, Salma da ta gama ruɗewa ta ruga da gudu ta je ta faɗa ma wata nurse, bada daɗewa ba suka dawo tare da likita ya nufi gadon Habu da sauri, bincikar sa ya fara yi tare da yi masu tambayoyi suna bashi amsa, tambayoyi ya shiga yi ma Salma game da jinin da aka saka masa tana bashi amsa a ruɗe, ɗibar jinin da aka saka ma Habu likitan ya yi tare da ɗayar ledan da ba a kai ga saka masa ba ya ba nurse tare da faɗi mata abun da yake son ta yi ta amsa da sauri ta bar wurin.....Rafka sallama Imrana ya yi a bakin falon hajiya kan shi ɗauke da robar awara, hajiya dake zaune a cikin falon ta juyo tana amsawa ya shiga ciki, daga gefe ya tsaya yana gaishe da ita ta amsa da murmushi ya ce, "An ce ga awaran." Ta ce to tare da nuna masa kitchen ta ce ya kai ciki ya ce ma Balaraba ta juye ya amsa da to tare da juyawa, lokacin da Imrana ya dawo bayan an juyo ya yi daidai da shigowar Deen cikin falon daga ƙofar waje, bin Deen ya yi da ido kamar idanun nasa za su faɗo har ya ƙaraso ciki ya wuce kujera ya zauna, da rawar jiki Imrana ya gaishe shi ya ɗaga masa kai ba tare da ya kalle sa ba, gaba ɗaya hankalin Imrana ya koma kan Deen ya kasa janye idanunsa yayin da Deen ɗin ya ɗauki remote yana canza channel, maganar da hajiya ta yi masa ta tambaye shi an juye awaran ita ta sa ya maido hankalinsa kan hajiyan ya ce mata eh, ta ce to ya ce ma innar tasu ta gode, yana niyyar tafiya hajiya ta ce, "Ina Salma, yau bata zo ba, ita ta saba zuwa kawo awaran." Dakatawa ya yi ya ce mata tana asibiti, tambayarsa hajiya ta yi wake bai lafiya ko ita, ya ce mata a'a ɗan maƙwabtansu ne ta tafi kaiwa, jinjina kai hajiya ta yi sai kuma ta tambaye shi mike damun yaron, ai kaman yana jira ya fara kora mata bayani tun daga kan zuwa da Habu ke yi gidansu ana bashi abinci har da yadda Salma ke haƙura da nata abincin ta bashi, kaf A to Z sai da ya zayyane ma hajiya yana yi yana kallon Deen, duk abun da yake faɗa Deen na saurare duk da sai ka ce hankalinsa baya akan sau don idanunsa na akan tv, cike da nuna jimami hajiya ta tambayi Imrana babansu baya aiki ne ko kasuwanci, ya faɗa mata tsohon ɗan sanda ne yadda ya ji an ce ba a biya shi kuɗin sallamar shi yadda ya kamata ba bayan ya ajiye aiki, har da sana'ar aca6a da yake yi a yanzu, girgiza kai hajiya ta hau yi da alamun rashin jin daɗin maganar, bayan ta furta, "Allah Ya kyauta." ta ce ma Imrana ya je idan Salma ta dawo ya ce tana kiranta tana son ta san halin da jikin yaron yake ciki, Imrana ya amsa da to kafin ya tafi, kallon Deen hajiya ta yi da alamun ƴar damuwa ta ce, "Al'amarin ƙasar nan tamu dai sai addu'a kawai, mutum ya ɗauki tsawon shekaru yana bauta ma ƙasar sa amman ƙarshe a kasa biyansa hakkinsa yadda ya dace, hakan ba ƙaramin naƙasu zai haifar ma ƙasa ba, don ƙarshe hakan zai iya ja mutane su fara gudun yin aikin gwamnati, ba kamar jami'an tsaro wanda rasa masu shiga aikin babbar barazana ce ga tsaron ƙasa. Ba da daɗewa ba dama na gani a labarai yadda tsofaffin ƴan sanda suka gudanar da zanga-zangar kai koken halin da suke ciki da yadda gwamnati ta manta da su, al'amarin dai sai dai a ce Allah Ya kyauta." Slowly Deen da ya juyo yana saurararta ya amsa da Amin. Tun bayan da likita ya tabbatar masu cewa Habu ya rasu Salma ke ta faman rizgar kuka, baiwar Allah ita gani take tamkar ita ce silar mutuwar ta shi tun da ita ta ɗauko shi ta kawo shi asibiti, duk da halin damuwa da iyayen Habu ke ciki na rasuwar ɗan nasu su ke ta faman rarrashin Salma, bayan an sallame su suka baro asibitin baban Habu na rungume da gawar ɗan nasa ita kuma innar Habu ta rungumo Salma ta gefe, har suka fito daga cikin asibitin kuka Salma ke ta yi tana tafiya da ƙyar, keke nepep baban su Habu ya tsayar masu suka shiga ya ba innar gawan Habu ya ce su yi gaba zai biyo su a mashin, bayan sun hau hanya Salma na kuka tana kallon fuskar Habu tamkar zata ƙira shi ya buɗe idanu, abubuwa da dama ne suka shiga dawo mata game da yaron, tuno ɗazun lokacin da zata kawo sa asibiti ta siya masa yoghurt har ya ce itama ta sha ta yi, ashe ita ce magana ta ƙarshe a tsakanin su, tuna hakan ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan, innarsu Habu da mai keken suna ta bata haƙuri, wayar innarsu dake a cikin aljihun doguwar rigar jikinta ce ta fara ringing, bayan ta ciro ta ɗauka tare da kaita kunne, tun kafin innar tasu ta ce wani abu ta jiyo shasshekar kukanta, da alamun ruɗewa ta ce, "Salma lafiya na ji kaman kina kuka? Ya jikin Habun? Yanzu nike son tahowa duba shi Sagir ya faɗa mani sun zo sun bayar da jini an saka masa..." Bata ƙarasa rufe baki ba cikin kuka Salma ta ce, "Innarmu Habu ya rasu...." Innar tasu ta saka dogon salati....