← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 197

Sashe 12

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyaɗa kai Salma da ta leƙo da kanta ta yi alamar atoh, cikin 6acin rai Sageer ya ce, "Amman dai ai ban koya mata ta rinƙa yi ma na gaba da ita rashin kunya ba ko?"

"A'a, ai Salma bata yi ma na gaba da ita rashin kunya, ku ma don kawai ta ɗauke ku kamar abokanta ne shiyasa take maku hakan matsayin wasa, kuma hada ƙarin bata da ƴan'uwa mata sai ku."

Daga bayan Innar Salma ta furta, "Hakane innarmu..." Harara Sageer din ya watso mata ta saka dariya, shi dai Auwalun bai ma ƙara bi ta kan su ba ya ci gaba da cin abincin shi, dama shi ba kamar Sageer yake ba bai cika hayaniya ba sai ta kama, Sageer ne dai sarkin zuciya abu kaɗan ya fara hargowa, ko cikin abokansa baya ɗaukar rainin wayo yanzu ya dambace da mutum gashi yana da ƴar ƙirar ƙarfi a jikinshi saboda yawan ƙwallon da yake yi.

Suna cikin haka aka yi sallama daga bakin ƙofa duk suka kai idanunsu wurin, wani babban mutum ne ya shigo wanda a shekaru ba zai gaza yin arba'in da biyar ba. Malam Bashir ke nan wanda shine jigon wannan iyali, da shi da matar tashi duk ba wani manyanta suka yi ba da yake irin auran wurin nan ne suka yi, mahaifiyarsu tana gama makarantar sakandare ta aure shi lokacin duka bai fi shekaru ashirin da ukku ba, lokacin da ya auri innarsu wato Fiddausy shima ya kammala karatun shi na sakandare, saidai bai ci gaba da karatu ba sai sana'ar kafintancin da yake yi wadda ta kasance gadon gidansu ce, suna da babban gareji da suke yin sana'ar shi da ƴan'uwanshi da kuma mahaifinshi wato kakan su Sageer kafin Allah ya yi mashi rasuwa, da wannan sana'ar da har yanzu ita yake yi yana da ɗan rufin asirin shi da yake kula da iyalinsa kuma daidai gwargwado yana ƙoƙari wurin sauke hakkokin su da ke kan shi.

Hannunshi ruƙe da babbar leda ya shigo cikin gidan, jikinsa sanye da ƙananun kaya riga mai dogon hannuwa da ma6allai da wando irin na magidanta, amsa mashi sallamar shi suka yi ya ƙaraso cikin gidan, kallon saitin da suke ya yi innarsu na murmushi ta ce mashi sannu da zuwa ya amsa, fitowa Salma ta yi ta nufe shi da sauri, a gaban shi ta tsaya tana murmushi ta ce, "Sannu da zuwa babana." Shima murmushin ya yi ya amsa mata, "Yauwa mamana. Ya gidan? Mike faruwa na gan ku kun yi tsaye cirko-cirko?" Satar kallon Sageer da ya ƙaraso wurin tare da innarsu ta yi tana murmushi, maida idanunsa ya yi kan innarsu Salma dake mashi sannu da dawowa, amsawa ya yi tare da kallon Sageer da shima ya ce mashi sannu da zuwa, ganin yadda ya ɗaure fuska kamar bai ta6a yin dariya ba yasa baban nasu tambayar innar mike faruwa,

"Ba komai, kawai Æ´an diramar gidan namu ne suka fara." Yana jin haka ya gane Salma da Sageer take nufi don ya san sune koda yaushe cikin rigima suke ko don suna mabiyi da mabiyi,

"Mamana mi ya haɗa ki da yayan naki.?" Dariya ta kama yi tana kallon Sageer da har lokacin ya ƙi ya saki fuska, ganin ta ƙi bashi amsa ya kalli Sageer ya tambayi mi ya haɗa su, cikin 6acin rai ya ce, "Wllh baba yarinyar nan ta raina mu, kuma in muka zo zamu hukunta ta inna ta hana, don ta ga kuna goya mata baya kuna hana a ɗauki mataki a kanta ya sa take ma mutane rashin kunyar da ta gadama." Ya ƙarasa yana hura hanci,

Ƴar dariya baban ya yi jin har da shi ake zargi cikin wanda ke goya ma Salma bayan abun da take yi,

"Mamana faɗa mun abun da kika yi masa." Ya faɗa yana kallon Salma da ɗan murmushi, itama murmushin take ta ce, "Wai daga na yi waƙa, kuma ni da wasa nike..." A fusace Sageer ya ce, "To mu abokan wasan ki ne? In ni kin raina ni kina ɗaukana tsaran ki duk da na baki shekaru shi Auwalun tsaran ki ne? Baba, wannan ƴar iskar waƙar take mana tana cewa wai ko ita kande ƙanwar maza duk tafi mazan wayau...ko a gidan ubanwa ta fi mu wayau, yarinyar da inda ba don na taimaka mata ba da yanzu a sakarya ta taso wllh." Gaba ɗaya suka saka dariya har Auwalu dake can gefe saida ya ɗan dara,

"Mamana mi ya sa kike tsokanar su?" ÆŠan kikkafta idanu ta shiga yi tana murmushi ta ce ita da wasa take yi masu.

"Tun da sun nuna basu so ki daina kin ji, koda zaki yi masu wasan ki rinƙa yi masu wanda baza su ga kin yi masu rashin kunya ba, banson ana cewa mamana bata da kunya." Tana yar dariya ta ce, "To babana na daina daga yau." Ya furta yauwa, harara Sageer ya wurga mata ya ce da dai wata ba ita ba, baban nasu ya ce tun da dai ta ce ta bari yasan bazata ƙara ba,

"Ka dawo an ƙi bari ka shiga ciki ma ka huta." Innarsu ta faɗa tana murmushi, amsa mata ya yi da to ya zai yi dole ya tsaya ya kashe wutar da mamanshi ta kunna, nufar wurin ɗakunan suka yi Salma na ruƙe da ledar da ya shigo da shi, yana ƙoƙarin shiga cikin barandar ya kalli Auwalu ya ce, "Auwalu an dawo daga makarantar?" Kai ya ɗaga cikin girmamawa ya ce, "Eh baba, sannu da dawowa."

"Yauwa, to ba a haƙuri a ajiye wayar sai an gama cin abincin a lallatsa, ko kuwa sai ka je ka tura a cikin hanci." Ya faɗa yana ƙoƙarin tsallake tudunkar barandar, duk su Salma suka ɗan yi dariyar maganar tashi, tabarma innarsu ta ɗaukko daga cikin ɗaki ta zo ta shimfida mashi a cikin barandar, bayan Salma ta ajiye ledan, can ƙarshen barandar daga gefen kicin ta nufa, a saman wani tebur dake ɗauke da kwandunan kayan wanke-wanke ta tsaya, bayan ta ɗauki wani ɗan babban farantin roba mai kyau ta wuce cikin kicin, bada jimawa ba ta fito ta ɗauro wata kula da sauran abubuwan dake ɗauke da mahaɗin abincin a sama, gaban baban nasu ta je ta ajiye kafin ta miƙe ta koma ta ɗauko plate da cokali ta kawo mashi, sake miƙewa ta yi ta je ta kawo ruwa, bayan ta ajiye tana murmushi ta ce, "Bismilla babana ga abincinka nan, bari na zuba maka." Jinjina kai ya yi da murmushi, zuba mashi komai ta yi bayan ta gama ta ce to ga shi nan ya ci, godiya ya yi mata tare da saka albarka a nutse ya fara ci.

"Yanzu dai Salma kin hana in rinƙa samun ladan kawo ma baban ku abinci, kullum yana dawowa ke ce zaki sauri ki kawo masa." Innarsu ta faɗa da sigar wasa, Salma na dariya ta ce ai itama ladan take so ta samu kuma itama ba tana samun ladan a wasu abubuwan ba, ko jiya da daddare ai ta yi mashi gugan kayan shi ko,

"Ba wani neman lada, neman suna dai kawai." Sageer ya faÉ—a yana harararta,

"Kai ka ta6a ganin inda uwa ta yi neman suna a wurin ɗanta?" Babansu da ya dakata da cin abincin ya faɗa, kafin Sageer ya ce wani abu wani ɗan matashin yaro wanda zai kai shekara sha biyar da alama shi yake bi ma Salma ya fito daga can ɗakin dake ƙarshe ya ƙaraso wurin, tsugunnawa ya yi ya ce, "Sannu da dawowa baba." Da murmushi ya amsa mashi, "Yauwa Imrana, dama kana gidan?"

Kai ya É—aga, "Eh, ina can ina yin Assignment ne ban san ka dawo ba, sai daga baya na jiyo muryar ka." Kai baban ya jinjina ya ce Allah Ya bada sa'a suka amsa da Amin.

"Ina Hamza, da Usman autan baba? Su ban gan su ba."

"Duk suna can suna bacci, shi Hamza tun bayan da ya dawo daga makaranta ya ci abinci ya kama yin bacci, gashi ma lokacin islamiyya ya taho dole ya tashi." Kai baban ya jinjina ya ce ya kwaso gajiyar makaranta ne shiyasa yake bacci, hannu ya kai ya ɗauki cokalin ya ci gaba da cin abincin, miƙewa Imrana ya yi zai tafi, kallon shi Salma ta yi da murmushi ta ce, "Yau ba a gayyata ta yin assignment ɗin.?" Shima murmushi ya yi ɗan kyakkyawa da shi sak komai na mahaifiyarsu ya ɗauko har haskenta, amsa ya bata da assignment ɗin baida wuya ya ga zai iya yi shiyasa bai kawo mata ta nuna ma shi ba, kai ta ɗaga mashi ya wuce.

"Salma da Allah tashi ki je ki wanke mani kayan lokaci na ƙurewa gashi har so nike su bushe."

Yamutsa fuska ta yi, "Allah Sageer ko na wanke su ba lalle har su bushe ba, gara ma kayan, amman wancan murtikekiyar safar bazata bushe ba, kamata ya yi ma a jiƙa ta ta kwana don ta yi dauɗa sosai har wari take yi." Ce mata ya yi to ta je ta wanke mashi kayan sai ta jiƙa safar yana da wata da bata yi datti sosai ba sai ya saka.

"Kowa yana zaune yana hutawa miyasa zaka takura mata ka saka ta wanki a cikin ranar nan." Babansu da ya dakata ya faÉ—a,

"Ai daman wankin take cikin yi na bata ta haÉ—a."

Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce ma baban nasu wllh haka yake takura mata ko da ba wankin take ba sai ya kawo kayan ƙwallon shi ya ce sai ta wanke mashi, harararta Sageer ɗin ya yi ya ce a da kafin a rinƙa kai kayanta wanki bashi ke wahalar wanke mata ba...

"Ke nan ba don Allah ka yi ba?" Innarsu ta faɗa tana ƴar dariya. "Don Allah na yi, amman dai dole a rama ma kura aniyarta." Ganin ta ƙi tashi ta je ta yi wankin ya kai hannu zai buge ta ta miƙe da sauri, innarsu ta ce mashi shi yake ja take mashi abu kuma ya zo yana faɗin ta yi mashi rashin kunya, wucewa Salmar ta yi don ta je ta ƙarasa yin wankin.....

_Bossladieswriters_

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_By Zainab Bature_
Chapter 12 · 0% Book details