Sashe 7
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Fahad, ya Hajiya fa? Wllh ina ta so in je don na kwana biyu ban leƙa ta ba sai dai ta waya, amman kwanan nan zan yi ƙoƙari in sha Allahu in samu in je dai." Tun kafin Fahad ya ce wani abu mom ta yi karaf ta ce, "To ai rashin zuwan ba laifin ka bane, kowa ya san yanayin aikin ka, ɗan siyasa dama ina ya ga wani isasshen lokacin da zai rinƙa yin tafiya a duk lokacin da ya so, kuma itama Hajiyar ba ta so a rinƙa ganinta ba ko yaushe, tun da ai har nuna kana son ta dawo nan ka yi amman ta ƙi amincewa, don haka ka ga sai dai ta rinƙa yin haƙuri sai lokacin da ta ganka kawai." Ta ƙarashe maganar tare da maida bayanta ta jingina da jikin kujera, yadda ta yi maganar ko a jikinta saima ta ɗauki waya tana latsawa, Fahad da Deen kuwa gaba ɗaya wutar su ce ta ɗauke jin kalamanta, shi ma dad ɗin shiru ya yi bai ce komai ba, wani abu ne ya tokare wuyan Fahad jin yadda Daddyn ya yi shiru, duk da dama bai yi zaton zai ce mata wani abu ba, saboda ba yau ta fara danƙara magana irin haka ba ba tare da ya tsawatar mata ba, ƙiri-ƙiri take nuna bata son danginsa su ra6e su, ta fi son ya rinƙa hidimta ma danginta kawai. Kowa na danginsu ya san bata son suna ra6ar shi sai ka ce ba ƴan'uwansa ba, abun takaicin ma hatta mahaifiyarsa bata ƙyale ba, ji dai yanzu maganar da ta faɗa, a cikin ran Fahad ayyanawa yake da a ce mahaifiyarsa ce ta yi maganar nan tabbas sai ta gane kuskurenta a wurin abbansu, amman shi duk irin abubuwan wulaƙanci da cin kashin da take ma danginsa ya zuba mata ido, yadda take cin karenta babu babbaka ba tare da ya iya yin wani katabus ba akai abun na basu mamaki, ko don tana da kyau ne ya sa ya ƙyale ta take abun da ta ga dama? Amma in haka ne, ai itama mahaifiyar su Fahad tana da kyau don bafullatana ce kuma jinin sarauta amman hakan bai sa abbansu ya bata damar da zata wulaƙanta na shi ba, dama kuma mahaifiyarsu Hajiya Amina mutuniyar kirki ce bata da halin wulaƙanta mutane. In ba don alaƙar aure ta haɗa Hajiya Jameela da nasu ba wllh bata kai matsayin da za ta taka wani daga cikin ahalin su ba ba tare da ta gane kuskurenta ba, matar da ahalinta duk talakawa ne kawai kyawun sura da Allah ya yi masu ne ya rufa masu asiri suke auran masu kuɗi, dama kuma iyayensu mukwaɗaita ne mugun son abun duniya gare su, hakan ya sa suka maida ƴaƴannasu jari.
Deen ya lura da yanayin fuskar Fahad akwai alamun 6acin rai dama kuma ya san shi da zuciya, kamo hannunsa ya yi ya ce mashi su je ɗaki zai nuna mashi abu, hakan ma mom ɗin sai da ta tanka, ta ɗaga murya tana faɗin su da ya bari anan ba don shi suka zo part ɗin nasa ba ko su basu da muhimmanci ne, Dad ne ya ce mata ta ƙyale su ta san kamar abokai suke da juna za su buƙaci ke6ewa su tattauna tun da sun daɗe ba su haɗu ba, Deen bai tsaya saurarar ta ba ya ja Fahad ɗin suka shige cikin bedroom, dogon tsoki ta ja tare da miƙewa ta nufi hanyar barin falon tana tafiya cike da isa, duk suka bita da ido, su kan su yaranta sun fahimci tana nuna bambanci tsakanin danginta da na daddynsu in suka zo ko suka haɗu da su, ko Funtua sai a daɗe bata je ba sai in wata hidima ta kama itama sau da yawa sai daddyn ya matsa mata sannan ta je, akwai part ɗin su da suke sauka a gidan Hajiyar Ambasada, haka za tai ta wulaƙanci tana yi ma mutane kallon rashin arziki, ko zaman da suke yi a gidan Hajiyar ba so take ba saida tai ta yi ma daddyn mitar ya gina masu gidansu daban kamar yadda yayansa wato mahaifin Fahad shima yake da gidansa daban, da ya tambaye ta miye illar zaman su gida ɗaya da Hajiya, sai ta fake da cewa unguwar da gidan yake ta yi ƙauye da yawa ba kamar unguwar da gidansu Fahad yake ba a bakin babban titi ba hayaniya da cunkoso, kawai ta faɗa masa hakan ne amman saboda bata son yadda danginsu da mutane suke zuwa in suka je ne, wani lokacin bata samun damar yi masu wulaƙanci saboda Hajiya na taka mata burki, shi ya sa take son ya gina masu gida daban su rinƙa sauka yadda zata ji daɗin taka duk wanda ta ke so. Duk suka je sai ta yi ta mashi mitar ya gina masu gida, sai dai ya amsa mata da zai gina masu, har dai daga baya sai da ta yi nasarar saka shi ya fara yi masu ginin katafaren gida amman har yanzu ba a kammala ba.
Batool na ganin mom ɗinsu ta fita ta miƙe ta bi bayanta, Sultan da Omar ma duk suka miƙe suka fita, miƙewa shima dad ya yi zai tafi, ganin Leemah ta yi zaune bata da niyyar tashi ya ce mata ta tashi su je, tana yamutsa fuska ta ce mashi tana son su yi hira da ya Fahad ne, ce mata ya yi ta bari zuwa anjima in sun gama tattaunawa tun da anan zai kwana sai su yi hiran, fuskarta a yamutse ta tashi ta bi bayan shi suka fita.
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
_Bossladieswriters_
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
Page 3
.......Bayan sun shiga cikin bedroom ɗin Deen wanda shima babba ne, sam ɗakin baida hayaniya amman ya tsaru da tsadaddun furniture, tun daga kan yadda aka tsara ɗakin zuwa kayan dake ciki irin na turawa ne, akwai tafka tafkan glass windows a wurare daban daban na bangon ɗakin, girman windunan in mutum ya tsaya a jiki za a iya hango kusan gaba ɗaya jikinsa, a jikin windunan akwai labulaye masu kyau da inganci kalar ruwan madara, sauran kayan cikin ɗakin ma duk kalar ruwan madara ne, akwai gado king-size bed with stylish high-end bed frame with built-in headboard, sai bedside drawers a saman su haɗaɗɗun fitilu ne, akwai tebur ɗin gaban gado ɗunɗumeme, daga ƙasa wani irin lallausan carpet ne mai gwa6i yana da gashi-gashi masu ɗan tsawo shima kalar ruwan madara, can ɗan gaba da gadon akwai lounge chair daga bayanta akwai tafkekiyar window wadda kana zaune a kan kujerar wurin kana hango waje, akwai dressing table da kujerar shi can gefe ɗaya, sai walk-in closet da ke acan cikin ɗakin, yadda aka tsara closet ɗin wurin ya yi kamar wurin sayar da kaya wato boutique, banda wurin kayan sakawa akwai wuraren ajiye takalma, daga tsakiyar closet din akwai dresser da chest of drawers a ciki su agoguna ne da sauran kayan gayun maza.
A saman kujerar zama dake gaban gadon suka zauna, kowa ya yi shiru fuskar Deen tattare da damuwa yake kallon Fahad da ya jingina bayansa jikin kujerar ya É—an É—age kai yana kallon gefe guda, a hankali Deen ya kai hannunsa ya É—aura a saman hannun Fahad É—in dake ajiye saman cinyarsa, juyo da fuskarsa ya yi ya kalli Deen,
"I'm sorry Yaya Fahad.." Deen ya faÉ—a fuskarsa tattare da damuwa, É—an murmushi Fahad ya yi masa kawai,