Sashe 24
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ashe ba daÉ—i? Kai ma ai ka iya ja ma mutun rai idan yana son abu a wurin ka ko?" Wani kallo mai cike da takaici yake mata, ita kuwa sai wani jujjuya ido take tana yamutsa baki,
"Wani abu kika nuna mani kina so na ja maki rai? Bana tunanin akwai abun da zaki buƙata a wurina ba tare da na yi maki ba..." Tarar numfashinsa ta yi, "Ai dama ban ce baka yi ba, amman wani lokacin sai ka ja ma mutum rai saboda yana nema a wurin ka, sai ran mutum ya gama 6aci.." Ta ƙarasa idon ta na kallon gefe ta ɗaure fuska, shiru ya yi yana ta kallonta ya ɗan ƙanƙance idanu, wannan halin nata na kawo tata buƙatar a lokacin da ya buƙaci hakkinsa ya tsane shi wllh.
"Yanzu miye kike so?" Ya tambaya bayan ya sauke yar ajiyar zuciya,
"Ka san mi na tambaye ka ai, maganar kuɗin da na yi maka zan tura ma Ammi." Wani kallon takaici yake wurga mata, wani lokacin har mamakin irin son kuɗinta yake, a koda yaushe cikin kawo masa buƙatun kuɗi take, duk da yana bata kuɗaɗe ba yan kaɗan ba, ban daAa kuma Deen da shima tana samun kuɗi a wurinsa bana wasa ba.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "In don wannan ne ai kin san zan baki tun da duk kika kawo mani wata buƙata da ta shafe su ina yin bakin ƙoƙari na, na ce ki ɗan jira ni kaɗan, yanzu babu isassun kuɗi ne a wuri na, cikin satin nan na tura ma injiniya da suke mana aikin gidanmu na Funtua kuɗi, aikin gidan yana da cin kuɗi sosai saboda gidan da kika nuna kina so ne ake yi duk don in faranta maki." Yamutsa fuska ta yi, "Amman dai ai baka cewa kwata-kwata baka da kuɗi, ko rabi ne sai ka bani." Kallonta yake yayin da ransa ke suya, ta saba haka nan ta kawo mashi buƙatar danginta ta kuma sa rigima idan ya nuna baya da hali, ba zata bar hankalin shi ya kwanta ba har sai ya yi mata abun take so, Allah kaɗai ya san adadin buƙatun kuɗin da ya yi ma danginta tun daga kan iyayenta zuwa ƙannanta. Sanin idan fa bai yi mata yadda take so ba to shima ba zai samu yadda yake so ba ya sa shi ce mata su tafi part ɗinshi zai tura mata rabin wayan shi na can, tare suka sauka daga saman gadon suka tafi tana ta cika tana batsewa, ni kam dai mai rubutun na ce 'A Juri Zuwa Rafi...'. Allah Ya kyauta Ya raba mu da son zuciya.
LONDON
Belgravia, (unguwar da aka fi sanin ta masu arziƙi a London...)
Gida ne bene hawa biyu na alfarma, yana da faɗi tare da ginin zamani mai ɗauke da gilasai. Ginin gidan na da manyan tagogi da aka yi da gilasai masu nuni da tsari na zamani tamkar ginin kamfani. Kana shiga cikin gidan zaka tsinci kanka a cikin wani falo mai girma zubin na turawa cike da alfarma. Bangon gaba ɗaya fari ne mai sheƙi, an ƙawata bangon ta hanyar ɗora masa manyan zane-zanen fasaha na zamani. Ƙasan falon an rufe shi da Persian rug na Turai mai kauri da tsananin taushi a ƙafa wanda yake yin ɗan ƙyalli idan aka yi tafiya a kai. Kujerun cikin falon ɗuma-ɗuman leathers ne wato na fata kalar baƙi da ratsin golden mai haske, suna da tsananin taushi ko a ido. A saman falon akwai babbar fitila (chandelier) mai ƙyalli, girmanta tamkar zata rufto ma mutum, wadda aka yi da gilashin lu'ulu'u masu haske, tana kwaranya haske ta kuma bai wa falon kyan gani fiye da yadda ake tsammani, akwai kuma wasu ƙananun fitilun a can sama. A gefe ɗaya na falon an sa babbar talabijin mai siffar bango (wall screen) wadda a girma ta wuce inci ɗari, da sauran kayan sauti masu bada sautin gaske da ke sa mutum ya ji kamar yana a cikin cinema. Daga hannun dama kuwa akwai na'urar kula da gida (smart home system) da aka ɗaura a kan bango tana sarrafa fitilu, talabijin, sauti da ma kofar shigowa, duk ta hanyar danna madanni ko amfani da murya. Daga ƙasan tagogin falon akwai na'urar ɗumama iska da na'urar sanyaya iska, wanda suke aiki da kansu idan yanayi ya sauya. Duk in da ka kalla a cikin falon, zaka ga alamar zamani, daga na'urar ƙara haske (smart lighting) wacce take canza launi da dare, zuwa na'urar magana (voice assistant) da take iya amsa tambayoyi cikin harshen turanci. Tabbas gidan ya amsa sunan aljannar duniya, ko da gidan yake a Turai kana gani ka san bana ƙaramin mai arziƙi bane. Akwai bangaren cin abinci wato dining area dake cike da alfarma da fasaha, haka akwai bangaren karatu wato study corner mai ɗan girma, akwai babbar shelf mai ɗauke da littattafai, nan ma bangaren an ƙawata shi da abubuwan fasaha irin su smart speaker dake amsa tambayoyi tana kula da smart home devices, kamar kunna fitilu ko sauran na'urorin lantarki, sauraran kiɗa, podcasts ko audiobooks, saita tunatarwa kamar alarm, kira da kuma aika saƙonnin murya. Zaune a saman kujerar fata mai mazaunin mutum biyu dake cikin ɗakin karatun, Maleek ne jikinsa sanye da farar jallabiya ƙal, idanunsa na a cikin farin gilashin screen, kana ganinsa ka ga mutum mai lafiyayyen jiki wanda ba zaka iya tantance ainihin shekarunsa ba, ƴar hurhurar dake a gashin gemunsa da kuma saman kansa ke ƙara bayyana manyantakarsa, fuskarsa na da cika mai nuni da kwanciyar hankali da arziki da kuma tsananin ƙwarjini, a saman teburin da ke gaban sa manyan litattafai ne tare da laptop sai wata fitilar karatu mai kyau, daga gefe wireless charging pad ne da ake ɗaura waya a sama ta yi caji, ya dukufa yana duba wani babban littafin fasaha, lokaci bayan lokaci yake ɗan dakatawa tare da kai hannunsa ya ɗan tatta6a kwamfuta ɗin kafin ya ɗaura da duba littafin.
Shigowa ta yi cikin babban falon tana sanye da riga da wando na bacci masu santsi kalar ruwan madara sai sakin kamshi mai ratsa zuciya take, ta rufe kanta da madaidaicin farin gyale da ya ɗan zame gaban kanta mai ɗauke da baƙar suma mai santsi ya bayyana, kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da ita ɗin kyakkyawa ce ta gaske, tun daga fuskarta zuwa dirin jikinta masu ɗaukar hankali ne, bin cikin falon ta yi da kallo kamar tana neman wani abu, hanyar da zata kai ta study corner ta nufa tana yin tafiya dake bayyana nutsuwarta, tana zuwa bakin ɗakin idanunta suka yi tozali da wanda take nema, wani ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta mai ɗauke da jan labba tamkar ta shafa jan baki sai dai kuma haka halittar su take, nufar shi ta yi tana yin tafiya a hankali kamar sanɗa yadda ba zata yi sautin da zai gane ta shigo ba, ta bayan shi ta zagaya tana zuwa ta kai hannuwanta ta saƙalo su ta kafaɗarsa tare da ɗaura kanta a gefen wuyansa, a nutse ya ɗago da fuskarsa mai cike da haiba yana murmushi ya kallo ta ta gefe, cikin sigar jan hankali ta kashe mashi ido tare da furta, "Sanyin idaniyar Sapnah kana nan ke nan, ka bar ni ni kaɗai." Ɗan lumshe ido ya yi yayin da ɗumin bakinta mai tattare da daddaɗan ƙamshin mouth spray ɗin da ta fesa ya bugi fuskarsa, a hankali ya furta, "Baki yi bacci ba?" ƙoƙarin zagayowa ta yi ta dawo ta gabansa, a saman cinyoyinsa ya yi mata masauki suna kallon juna cikin ido fuskokinsu tamkar zasu haɗe ta bashi amsa da, "Ta ya zan iya yin bacci mai saka ni in yi baccin baya kusa da ni." Yar dariya ya yi, slowly ya matso da bakinsa ya yi kissing reddish lips ɗinta ta lumshe ido, "I'm sorry, ina wani bincike ne mai muhimmanci da muke buƙatar sa da gaggawa." Ta ɗan kashe masa ido tare da furta, "Don't worry honey, kana da amincewar Sapnah a koda yaushe." Ya lumshe mata ido can ƙasan maƙoshi ya furta, "Thank you mah luv." Ta kai bakinta ta sumbaci kuncinsa kafin ta sauka daga jikinsa ta zauna gefensa ta ce ya ci gaba da aikin.