← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 197

Sashe 76

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_

_ZAINAB BATURE_

27

Washe gari misalin ƙarfe sha ɗaya na safe bayan hajiya ta gama yin breakfast suka fito don tafiya yin gaisuwa tare da Balaraba kamar yadda ta ce ma Salma, har da Deen za a je, bayan sun fito ya tambayi hajiya za su je da mota ne ta ce kamar ba sai sun hau mota ba tun da an ce maƙwabtan su Salma ne duk da ita bata ma san gidan su Salman ba ta dai san a unguwar suke, dama asali ta dalilin Balaraba ta san su Salma na yin awara har take sawa suna yi mata, tambayar Balaraba ta yi ko gidansu Salma da nisa ta ce mata a'a kusa ne da an fita tsallaken hanya, bayan sun fito su officers suka shiga gaishe da hajiya tare da Deen, bayan sun gama gaisawa suka tambayi unguwa za su je nan hajiya ta sanar masu nan tsallake gidan gaisuwa za su je, Officers guda biyu ne suka bi bayansu don yi masu rakiya, tun da suka fito mutane ke ta zuwa suna gaishe da hajiya ita da Deen har suka ƙarasa cikin layin su Salma, da yake gidan rasuwa ne suna shiga layin suka gane gidan dama kuma ga mutane masoyan Deen da suka rufa masu baya, mutanen dake zaune wurin amsar gaisuwan suna ganin su duk suka miƙe suka shiga gaishe da su suna yi masu sannu da zuwa, da fara'a hajiya ke amsawa haka ma Deen fuskarsa a sake yake amsa ma mutane gaisuwar da suke yi masa, hajiya ta tambayi mahaifin yaron mai rasuwa aka nuna mata baban Habu, gaisuwa ta yi masa haka ma Deen da Balaraba, hajiya ta ce zasu shiga su yi ma mahaifiyar yaron gaisuwa, da sauri baban Habu ya shige gaba, dama tun kafin su shigo wasu daga cikin yaran gidan tuni sun kai rahoton zuwan nasu, a nan waje Deen ya tsaya da jami'an da suka yo masu rakiya hajiya da Balaraba suka bi bayan baban Habu, lokacin da suka shiga a tsakar gida suka iske matan gidan da ƴan gaisuwa duk sun fito suna tsaye, cikin girmamawa suka shiga yi ma hajiya sannu da zuwa suna gaishe da su, duk da sun san hajiya mutuniyar kirki ce mai taimakon mutane ba su yi zaton ganin ta gidan da sunan ta zo gaisuwa ba, koda a ka yi mata tayin shiga ɗaki cewa ta yi a'a daga nan waje ma ya isa, da sauri baban Habu ya nufi dakinsa ya ɗauko wata yar babbar darduma ya zo ya shimfiɗa masu daga gefen ɗakunan, hajiya kawai ta zauna ita Balaraba a tsaye ta tsaya, bayan an nuna ma hajiya innarsu Habu dake tsugunne gefe ta yi mata gaisuwa tare da bata haƙurin rashin da ta yi, cikin girmamawa kan ta a ƙasa take amsa ma hajiya, bayan ta gama mata gaisuwan ta sanar da su yadda akai ta samu labarin rasuwan, maida kallonta ta yi kan baban Habu dake a tsugunne shima ta ƙara masa gaisuwa cike da girmamawa yake amsawa ta ɗaura da cewa, "Abu idan Allah Ya ƙaddaro ba makawa sai ya faru, amman idan al'amari ya tsananta sai a zo a nemi taimako, ni ina zaune ba sanin abubuwan dake faruwa nike yi ba sai idan an zo an sanar mani, ko yaya ne dai idan an zo an sanar ba a rasa abun yi ba." Cike da dattako take yin magana, kan baban Habu a ƙasa ya ce mata lokacin da ya ga jikin nasa ya tsananta sannan ga ƴan uwansa guda biyu suma duk a kwance sai da ya je da niyyar neman taimako a wurinta sau biyu, sai dai bai samu ganawa da ita ba saboda jama'a da suka yi yawa, ƙarshe dole ya haƙura ya siya masu magani da abun da yake da shi, kai hajiya ta jinjina daga yanayin fuskarta zaka fahimci bata ji daɗin hakan ba, ta ce masa da yake Deeni ya zo shiyasa jama'a suke yin yawa kowa da buƙatar da ta kawo shi, ƴan tambayoyi ta yi masa game da aikinsa da ya ajiye yana bata amsa a nutse, addu'ar Allah Ya ƙara rufa asiri ta yi ta ce In sha Allahu za a ga abun da za a yi, kallon Balaraba ta yi ta ce mata ta amshi lambar wayarsa daga haka ta miƙe, duk mutane suka rufo mata baya don yi mata rakiya, har ƙofar gida wasu suka biyo ta don su ga Deen, tana fitowa shima ya miƙe a lokacin mutanen dake tare da shi sun ƙara yawa har da su Sagir da sauran matasa ƴan sabon club ɗin sa, mutanen da ke zaman amsar gaisuwan ma bayan ta fito duk suka miƙe suna yi mata sallama da godiya, sai da baban su Habu ya rako ta har wurin gidan su Salma hajiya ta juya ta ce masa ya koma shi da ke amsar gaisuwa, kai a ƙasa ya yi mata godiya kafin ya juya, kallon Balaraba ta yi da ɗan murmushi ta tambaye ta ina ne gidan su Salma lokacin suna a saitin gidan, bayan Balaraba ta nuna mata ta ce bari su shiga yau a gaisa, Sagir na ganin gidan su suka nufa ya yi saurin riga su shiga don ya sanar da zuwan su, ganin Deen zai wuce hajiya ta tambaye sa gida zai tafi ya ce mata eh sai ta dawo, da murmushi ta ce shi ba zai zo su je tare ba ya yi godiyar hidimar awara da ake masa, ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba suka nufi gidan, a bakin kofar gidan jami'an da suka rako su suka tsaya tare da dakatar da mutanen da suke tare da su a nan, hajiya na shiga cikin gidan da sallama innarsu Salma da ta fito ta amsa cikin fara'a tana mata sannu da zuwa, gidan nasu fes da shi tamkar a zuba abinci a saman simintin tsakar gidan a ci yadda ya yi tas, dama duk safiya kafin Salma ta tafi makaranta take share gidan ƙwal sai innarsu ta ƙarasa sauran gyaran gidan, gaba ɗaya tsakar gidan ya karaɗe da ƙamshin tsintsiyar ƙamshi mai daɗi, "Sannun ku da zuwa hajiya, maraba..." Baban su Salma da bai kai ga fita ba ya shiga faɗa bayan ya fito daga cikin ɗaki, tana murmushi take amsa masu, innarsu Salma ta nuna masu ɗaki ta ce su shiga, hajiya ta ce, "A'a nan ma ya isa, dama daga gidan gaisuwa muke na tambayi Balaraba gidan na ce bari a shigo a gaisa mu yi godiyar hidiman awara da ake yi mana." Innarsu Salma dake ta fara'a ta ce ai ba komai, baban su Salma ne ya fito daga ɗakinsa da sauri yana riƙe da tabarma babba ya shimfiɗa a cikin baranda ya ce ma hajiya ga wuri tana ta tsayuwa, nufar cikin barandar ta yi tana faɗin dole dai sai ta zauna ke nan yana ta murmushi ya ce yadda za a gaisa sosai, kafin ta zauna ta kalli hanyar waje ta sanar da su tare suke da Deen, baban su Salma ya nufi hanyar zauren da sauri, sai ga su sun shigo tare har da Sagir dake ta faman washe baki kamar bakin nasa zai yage, ganin abun yake kamar mafarki Deen Jr yau a cikin gidan su, wanda idan da wani ya faɗa masa hakan abu ne da zai yuwu tabbas zai ƙaryata da babbar murya, a bakin barandar Balaraba ta tsaya shi kuma Deen ya ƙarasa kusa da hajiya ya zauna, innarsu Salma da ta tsugunna can gefe tana ta kallonsa don wannan ne karo na farko da ta ta6a ganinsa ido da ido, daga gefe shima baban su Salma ya duƙa yana gaishe da hajiya, Deen da tun da ya shigo kansa na a ƙasa ya ɗago yana amsa masu gaisuwar da suke masu a nutse,

"Ai na ce shima ya shigo ya yi godiya anata masa hidiman awara." Hajiya ta faɗa idonta akan Deen tana murmushi, "A haba ai ba komai wllh, mu ma muna ta ganin abun arziƙi. Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara girma da ɗaukaka." Babansu Salma ya faɗa da fara'a, itama innar tasu ta ce ai ba komai ta yi ma Deen godiya, shi dai bai cewa komai sai ɗan murmushi dake a kan fuskarsa yana yi yana sauke idanunsa, "Ina Salma, ina ce dai ta warware ko? jiya da ta je tana ta kuka lokacin da ta sanar mani da rasuwan yaron." Hajiya ta faɗa, innarsu Salma ta ce, "Eh wllh haka tai ta faman kuka wai ita gani take don ta kai shi asibiti ne ya rasu, har sai da zazza6i ya kama ta, amman ta samu sauƙi har ta tafi makaranta ma." Hajiya dake murmushi ta ce ina ruwan Salma ai abu mai kyau ta yi lokacinsa ne ya yi, tambayar jikin nata da sauƙi sosai har ta tafi makaranta hajiya ta yi, baban su ya ce, "Ta samu sauƙi sosai, dama jiyan saboda kukan da ta sha ne sai kanta ya fara ciwo daga baya sai zazzabi ya rufe ta, bayan ta sha magani ta samu sauƙi, yau da safe har ta tafi makaranta, sai da aka ce mata ta bari ta ƙara warwarewa ta ce ta samu sauƙi, da yake Salma akwai son karatu ba ƙaramin dalili ne ke hana ta zuwa makaranta ba." Ya ƙarasa da murmushi, kai hajiya ta jinjina ta ce Allah Ya sa ma karatun albarka, duk suka amsa da Amin,
Chapter 76 · 0% Book details