Sashe 148
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Leemarh ta fito cikin falon tana sanye da atamfa mai kyau ta yafa gyale, hannunta ɗaya tana janye da trolley Binafa na biye da ita da wata jaka, cikin falon gidan suka ƙaraso duk ƴan gidan suna a nan zaune har da Fahad, mommy ta kalle ta da murmushi ta ce, "Daughter an gama shiryawa?" Leemarh da duk ta yi sukuku da ita saboda tafiyar da zata yi cikin sanyin jiki ta ɗaga mata kai, Khaleel da suka zo weekend ya kalle ta yana murmushi ya ce, "Sis Leemarh sai kuma yaushe?" Ta kalle shi a sanyaye ta ce in aka yi wani hutun in sha Allah, ya jinjina mata kai, "Ya Leemarh za mu yi missing ɗin ki wllh." Ta kai idonta kan Sadeeq da ya yi maganar ta ɗan yi murmushi kawai, Sadeeya ce ta shigo cikin falon ta nufo su, gaban Leemarh ta zo tana murmushi ta miƙa mata ƴar babbar ledan data ruƙo ta ce, "Sis Leemarh ga wannan kya yi amfani da su." Leemarh ta amsa ta yi mata godiya, Fahad da shine zai maida ta Abuja ya ce, "Shike nan zamu iya tafiya?" Mommy ta ce bari a sanar ma daddyn su za su tafi, Sadeeq ne ya tafi sanar masa, bada jimawa ba suka dawo tare da daddy yana sanye da jallabiya, daga gefen Leemarh ya tsaya yana murmushi ya dafa shoulder ɗinta ya ce, "Daughter za a yi mana halin baƙo?" Ta ɗaga ido ta kalle shi ta yi ɗan murmushi kawai, "Allah Ya tsare Ya kai ku lafiya. Mun gode kwarai Allah Ya bada ladan zumunci." A hankali ta amsa da Amin, "Za a sake zuwa mana wani hutun ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh, kallon Fahad daddy ya yi ya ce ya tashi su je lokaci na tafiya, Fahad ya miƙe ya zo ya kama trolley ɗin da ta fito da shi, Khaleel ya ɗauki wani box da ke anan falo, Sadeeya ta ɗauki jakar da Binafa ta fito da ita, gaba ɗayansu suka rako su harabar gidan, Fahad ya bude boot ya saka trolley ɗin duk sauran kayan ma aka saka, daddy ya kira Fahad daga gefe ya kai hannu cikin aljihun jallabiyar jikinsa, kuɗi masu yawa ya fiddo ya miƙa ma Fahad suka ɗan yi magana kafin ya koma wurin motan ya buɗe driver seat, Mommy ta kalli Leemarh tana murmushi ta ce, "To daughter Allah Ya kiyaye hanya Ya kai ku lafiya. Mun gode sosai, za mu yi missing naki." Leemarh ta matsa ta faɗa jikin mommy tana ƙoƙarin hana ƙwallan da suka taho mata zubowa, momy na murmushi take ɗan shafa bayanta, bayan ta ɗago haka ta bi sauran matan suka rungume juna, Sadeeq ma suka ɗan rungume juna, Khaleel ya kama hannunta yana murmushi ya yi mata Allah Ya tsare, Fahad dake tsaye ya dafa motan yana kallon su, ɗan murmushi ne akan face ɗinsa, a zuciyarsa yana raya ya san idan suka yi aure ba ƙaramar fahimtar juna za a samu ba tsakaninta da family ɗinsa, ta 6angaren su baya hango za a samu wata matsala, jiki a sanyaye Leemarh ta nufi motar, tsayawa ta yi daga gaban kofar ta juya tana kallon su ta ɗaga masu hannu, suma duk suka ɗago mata har da daddy, tuni Binafa ta fara yin hawaye, ta so a tafi da ita to sai dai shi Fahad ɗin idan ya maida ta gobe idan Allah Ya kaimu zai taho ya tsaya wurin aiki, bayan ta shiga cikin motar shima Fahad ya shiga daga haka ya tashi motar, suna ta ɗaga ma juna hannu yayin da motar ta tunkari gate har suka fice, a hankali Leemarh ta kai hannu tana goge ƙwallan da suka zubo mata, Fahad ya ɗaga ido yana kallonta ta cikin madubi. Bayan sun baro gidansu Fahad gidan hajiya suka wuce, duk da jiya da dare ya kai Leemarh ɗin ta yi mata sallama amma hajiyar ta ce kafin su tafi yau su biyo, lokacin da suka shiga cikin falon ba kowa, Fahad ne ya nufi ɗakinta don ya yi mata magana, tare suka fito hajiya ta nufo Leemarh da ke a tsaye, daga gabanta ta tsaya tana murmushi ta ce, "Haleematu baƙo zai yi halinsa?" Kai Leemarh ta ɗan jinjina mata, "To Allah ubangiji Ya tsare hanya Ya kai ku lafiya." nan ma kai Leemarh ta ɗaga mata don ji take da ta yi magana kuka zai taho mata, Balaraba hajiya ta ƙwala ma kira ta fito ta nufo su, hajiya ta ce, "Ƴar hutun mu ce zata tafi." Balaraba ta kalli Leemarh da ɗan murmushi ta ce, "Allah Ya tsare Haleematu Ya kai ku lafiya." a hankali ta amsa mata, hajiya ta ce ta je ɗakinta ta dauko akwati na nan gefen gado, bayan Balaraba ta kawo akwatin ta ce zata ɗauko ma Leemarh abu, kicin ta nufa bada jimawa ba ta dawo tana rike da wani package, miƙa ma Leemarh ta yi tana murmushi ta ce, "Haleematu ga snacks da na yi maki kya ci a hanya." Leemarh ta amsa ta ce ta gode, nuna ma Fahad akwatin hajiya ta yi ta ce ya ɗaukar mata, hajiya na riƙe da hannun Leemarh suka fito Balaraba na biye da su, hajiya ta ce, "Haleematu sai an ƙara zuwa mana wani hutun ko?" Kai ta jinjina mata sai kuma ta yi saurin faɗawa jikinta jin kuka ya taho mata, hannu hajiya ta sa tana ɗan bubbuga bayanta tana murmushi tare da rarrashinta tana faɗin ta kwantar da hankalinta ai ba ta gama zuwa hutun ba ke nan, da ƙyar ta saki hajiya ta shiga mota, suna ta ɗaga ma juna hannu a haka suka fito daga gidan. Tun da suka hau hanya Leemarh was so silent, ta jingina kanta a jikin kujera tana ta kallon gefen hanya, lokaci lokaci Fahad ke ɗaga ido ya kallo ta ta mirror ko kuma ya ɗan juya, bai tanka mata ba ganin yanayinta saboda ya riga ya san abun da ke damunta, tun ana saura kwanaki zata tafi take faɗa masa game da yadda zata yi missing ɗin su musamman shi, bayan sun yi nisa a tafiya ganin shirun nata ya yi yawa calmly ya kira ta ta juya ta kalle shi, da ɗan murmushi ya ce, "Ya aka yi ne?" Shiru ta yi tana kallon shi, bayan ya juyo sun haɗa ido ta ɗan girgiza masa kai ta ce ba komai daga haka ta juya ta ci gaba da kallon hanya. Lokacin da suka iso Kaduna lokacin sallar azahar ya fara shiga hakan ya sa Fahad ya tsaya wurin wani masallaci ya ce mata bari ya yi salla ta ɗaga masa kai, after some minutes ya dawo ya buɗe driver seat ya tsaya ba tare da ya shiga ba ya ce mata ko itama zata yi sallan ya ga akwai 6angaren mata, slowly ta girgiza masa kai ta ce bazata yi ba, shiru ya yi yana kallonta nan take kuma ya gane bata yin sallan ne, shiga ya yi ciki ya zauna yana ƙoƙarin kunna motan ya ce bari su samu wani eatery sai su ci abinci, kallon shi Leemarh ta yi a sanyaye ta ce, "Ni ba wani yunwa nike ji ba." Fahad ya juya ya kalle ta ya ce, "Amman dai ai ba har mu je Abuja ba zaki ci komai ba." Ta ce to ai ga snacks da aunty Balaraba ta bata ko shi sai ta ci, ɗan jinjina kai ya yi ya ce ok bari to a samu lemu sai ta haɗa, bayan sun fara tafiya ta kalle shi ta ce to shi ba zai ci abincin ba, idanunsa akan hanya ya ce lafiya lau shima sai ta samma shi snacks ɗin ya ishe shi. Tun da Leemarh ta ga sun kusa isa Abuja yanayinta ya ƙara sauyawa, damuwa ta bayyana akan fuskarta, haka nan take jin bata son komawa, Fahad dake kallonta akai akai ta mirror har ya gane damuwar da ta ƙara bayyana akan fuskarta, ɗan kallonta ya yi ya kira sunanta ta juya ta kalle shi, calmy ya ce, "What's wrong?" Kai ta ɗan girgiza masa ba tare da ta ce komai, ta langa6ar da kanta tana kallon gefe, bayan ɗan lokaci ta yi saurin juyowa ta kai idanunta kan hannun Fahad da ta ji ya kama nata hannun da ta ɗaura akan lap ɗinta, bin hannun nashi ta yi da kallo ya yin da ƙirjinta ke ɗan bugawa, don tun da ta zama budurwa ya daina ta6a ta ba kamar lokacin da take yarinya ba, ɗan kallon shi ta yi idonsa na akan hanya yana driving da hannu guda, sauke idonta ta yi tana ta kallon hannun nashi, after a while still yana riƙe da hannun nata ta ji muryar shi ya ce, "Idan kuka samu wani hutun da gaske zaki ƙara zuwa?" kallon shi ta yi a ranta tana jin rashin tabbacin hakan saboda yadda ya faru tsakaninta da mom ɗinta kafin ta zo wannan hutun, amman tana jin komai zai faru idan aka ƙara yi masu hutu nan zata zo, a hankali ta ɗaga masa kai ta ce eh, shiru ya ɗan yi sai kuma ta ji ya tambaye ta hutu nawa za su ƙara samu kafin su yi graduation, ta bashi amsa da biyu ya ɗaga kai idanunsa akan hanya, "Zaki iya dawowa Funtua da zama?" Da sauri Leemarh ta kalle shi jin tambayar da ya yi mata, juyowa ya yi suka haɗa ido ya ce, "I mean....dawowa na har abada" Kallon shi tai ta yi ya maida idonsa kan hanya, ɗan kallonta ya yi ya ɗage mata gira, slowly ta jinjina masa kai alamar eh, sakin hannunta ya yi ya ci gaba da driving ba tare da ya ce komai ba, maida kanta ta yi gefe ta ɗan yi murmushi don ta fahimci inda maganar tashi ta dosa, hakan kuma ya sa ta ɗan rage jin damuwar dake a ranta, nan take ta ji inama zata iya janyo lokacin....
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
48
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
48