← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 197

Sashe 98

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mutane, wasu suna waƙen goyon bayan clubs ɗin da ake wasan da su, wasu suna sakar ma club ɗin adawar su habaice habaice, gaba ɗaya Deen ne tauraron wasan har waɗanda basa goyon bayan club ɗin da yake ma wasan sai faman washe baki suke ba tare da sun san suna yi ba, ainihin ƙwarewa a ƙwallon ƙafa mutane ke a gani a wurin Deen, muryoyin mutane sun karaɗe stadium ɗin da faɗin sunan Deen Jr, tuni videos da hotunan wasan suka karaɗe kafofin sada zumunta, mutane nata comment wasu suna jin tamkar su yi tsuntsuwa su gan su a wurin. Lokacin sallar magrib aka dakata da wasan, sai bayan da aka gama sallar issha aka kuma dasa wanda suka kai har ƙarfe goma na dare kafin aka gama. Farko yadda aka tsara tournament ɗin na kwana ɗaya ne, amman yanzu dole ya zama na kwana biyu kuma an ƙara lokuttan bugawa saboda gasan ba zai kammalu cikin kwana ɗaya ba. A matuƙar gajiye Deen ya koma ɗakinsa na hotel bayan an maida shi, wanka ya fara yi sannan ya yi sallar shafa'i da wutiri, da ƙyar ya fita falo ya ɗan ci abincin da aka kawo masa ba da yawa ba, ya so ya ɗan zauna a nan ya duba tarin saƙonnin da yake da tare da missed calls da ya tarar a wayansa da niyyar abincin da ya ci ya bi masa jiki, sai dai ya gaji sosai kawai so yake ya ji sa a kwance hakan ya sa shi wucewa cikin ɗaki, already kayan bacci ne a jikinsa ya nufi gado idanunsa na lumshewa. Salma zaune a ɗakinta bayan ta yi shirin kwanciya, tunani ne iri-iri ke mata yawo a cikin zuciya, tun bayan da ta gama kallon vedios na wasan Deen a Kano da ke ta yawo a social media ta ji tana son ta yi waya da shi, sai dai wata zuciyar na hana ta yin hakan duba da jiya ta kira shi bai ɗauka ba kuma bai biyo kiran ba, don haka yanzu ma ko ta kira hakan ne zai sake faruwa, wannan tunanin ya sa ta fasa kiran nasa ta haye gado ta kwanta, ko da ta kwanta ta kasa yin bacci kuma son kiran Deen ɗin ya ƙi fita daga ranta, hannu ta kai a hankali ta ɗauko wayarta ta latsa power haske ya kawo, ƙura ma hotonta tare da innarsu dake a wallpaper ɗinta ido ta yi tana kokonton ko ta kira, bayan ɗan lokaci ta kai hannu gabanta na ɗan faɗuwa ta danna masa kira, Deen bai daɗe da kwanciya ba wayarsa ta fara ringing, a hankali ya buɗe idanunsa da bacci ya fara cin ƙarfin su sun ɗan yi ja, kallon wayar da ke ta yin ringing ya yi bacin da ya ci karfinsa ne ya sa bai saka ta a silent ba, a hankali ya kai hannu ya ɗauko ta da niyyar ya saka ta a silent ɗin, bin lambar da ake kiran da ita ya yi da kallo ya gane ita ce aka kira sa har sau biyu jiya da daddare, ɗan jim ya yi kamar yana tunani a haka har kiran ya tsinke, jiki a sanyaye Salma ta bi wayan da kallo bayan kiran ya yanke, zuciyarta na jaddada mata ai dama ta ce ko ta kira ba zai ɗauka ba, ajiye wayan ta yi a cikin ranta ta yanke wataƙil ba kowane kira yake ɗauka ba, ƙilan shi ne zai rinƙa kiranta, tunani ta yi ko ta yi masa magana ta whatsApp, har zata yi hakan sai kuma ta fasa ganin dare ya yi ta yanke gobe idan Allah Ya kaimu sai ta yi mashi, bayan kiran ya yanke Deen ya ji yana son sanin wanda ke kiransa da lambar, a kasalance ya maida ma lambar kira, Salma har ta rufe idanuwanta jin ƙarar wayarta ya sa ta yi saurin buɗe su, mamaki ne ya kama ta ganin Deen ne ke kira, da sauri ta tashi zaune gabanta na ɗan faɗuwa ta kai hannu ta ɗauki wayan, kamar mai jin tsoron yin picking a ɗarare ta ɗauki kiran, shiru ta yi bayan ta kara ta a kunne ƙirjinta na ci gaba da ɗan bugawa, sam ta kasa yin magana sai ɗan motsa baki take kamar mai ƙoƙarin tattaro abun da zata faɗa, "Hello, Assalam alaikum..." Ta ji daddaɗar muryarsa a cikin kunnanta, har sai da ta ɗan rufe ido murmushi ya bayyana a kan fuskarta, a hankali ta ce, "Wa'alaikumus salam. Ina yini.." Jim ya ɗan yi ba tare da ya amsa ba, tunani ta fara yi ko bai gane ta ba ne ko kuma bai ji ta ba, hakan ya sa ta ɗan ɗaga murya ta sake cewa, "Yaya Deen ina yini." Daga ɗayan 6angaren ta ji ya furta, "Salmerhh.." Bata san lokacin da ta saki faffaɗan murmushin jin daɗin ya gane ta ba, a hankali ta amsa masa da na'am,
Chapter 98 · 0% Book details