Sashe 116
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
....Mom Jameela na fitowa bakin part ɗinta idanunta suka sauka akan baƙuwar, ɗan guntun murmushin gefen fuska ta yi ganin wacce dama ta yi zaton zata gani daga bayanin da chef Alima ta yi mata, cikin falon ta nufo tana sanye da doguwar riga ta ɗaure gyalen ta a kai, bayan ta ƙaraso cikin falon, a kujerar kusa da ta baƙuwar ta zauna idon ta akan ta ta furta, "Nailah manyan gari, yau an shigo Abj ke nan?" Gira ta ɗaga mata idanunta akan wayarta, "Yau kika shigo ne?" Ta girgiza mata kai kafin a taƙaice ta ce, "Jiya." Idanun mom Jameela akanta ta ce, "Ok, ya su ammi, ko ba daga Kano kike ba?" Sai lokacin ta ɗago ta bata amsa da daga can take suna lafiya, "Wani abu kika zo yi, ko kuwa mu aka kawo ma ziyara." Mom Jameela ta faɗa da ɗan murmushi, slowly ta girgiza mata kai ta bata amsa da tayo rakiya ne, kallon Rashidat da har lokacin ke a tsaye mom ta yi sai kuma ta maido idanunta kan Nailah ta ce halan laifi ta yi, ta ɗage gira ta ce, "Ask her." Maida idonta ta yi kan Rashidat ta tambayi mi ta yi, cikin rawar murya ta faɗa mata, mom ta kalli Nailah still da ɗan murmushi ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce, "Ki yi haƙuri baƙuwa ce bata san ki ba." Shiru kaman bata ji ta ba ta maida idanunta kan waya, saida mom ta sake mata magana sannan ta ɗan ɗaga hannu, mom ta ce ma Rashidat ta je ta kawo mata lemu da sauri ta amsa da, "Okey ma." Kitchen ta koma, lokacin da ta shiga chef Alima bata a ciki, sai da ta ɗan yi jimm bayan ta buɗe fridge tana tunanin lemun da zata kai gudun ta sake yin wani laifin, ƙarshe ta ɗauko babbar robar Fanta, a saman ɗan tray mai kyau ta ɗaura ta ɗauko glass cup mai kyau ta haɗa, bayan ta koma cikin falon, ɗan ƙaramin table dake a gefen kujerun ta ɗauko ta ɗaura tray ɗin, hannunta har ɗan rawa yake tana buɗewa, tsiyayawa ta yi a cikin kofin ya ɗan wuce rabin kofin sannan ta rufe robar ta ajiye, tsaye ta yi tana bin su da kallo ganin ba wanda ya bi ta kanta, a ɗan tsorace ta furta, "Ga lemun ajiya." Tamkar bada ita take ba, kallon Nailah mom Jameela ta yi ta ce mata ga lemu nan an zuba mata, sai da ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta ɗago idanunta ta kalli cup ɗin lemun, hannu ta kai ta ɗauka kawai sai gani suka yi ta watsa shi a jikin Rashidat, wata irin firgita Rashidat ta yi saboda sanyin lemun, rawa jikinta ya shiga yi ta shiga ja da baya tana yarfewa, da sauri mom Jameela ta kalli Nailah ganin abun da ta aikata sai dai bata ce mata komai ba, "Daga yau ki riƙe ko ni wacece, sannan kada ki sake kawo mani lemu kalar ƴan ƙauye!" Baiwar Allah jikinta na kerma ta ɗaga mata kai, "Kuna da La casera a gidan?" Ta tambayi mom Jameela ta ce mata kaman akwai, kallon Rashidat ta yi ta ce mata akwai La casera ɗin ta ce mata eh, "Je ki kawo mata." Ta juya da sauri ta nufi kitchen tana ɗan yarfe hannuwa, without wasting time ta kawo mata lemun, tana niyyar buɗewa ta zuba mata a wani glass cup da ta ɗauko, hannu Nailah ta ɗaga mata alamar kada ta buɗe, Rashidat ta ja baya ta tsaya kanta a ƙasa, "You can go." Nailah ta faɗa bayan ta kai hannu ta ɗauki lemun, "Thank you ajiya." Rashidat ta faɗa tare da juyawa da sauri ta tafi, tana komawa cikin kitchen ta iske Alima ta dawo dama baya ta je, tana ganinta ta nufe ta da sauri tana zuwa gabanta ta fashe da kuka, "Rashidat, what happened?" Cikin kuka ta shiga fada mata abun da Naila ta yi mata, Alima ta ta6e baki tare da kai hannu ta dafa shoulder ɗinta ta yi ƙasa da muryarta ta ce, "Kada hakan ya dame ki, haka halinta ya ke bata da kirki, ni kaina ta ta6a mari na." Da alamun mamaki Rashidat ta maimaita ta mare ta, Alima ta tabbatar mata da abun da ta faɗa, "Shike nan don bamu da kuɗi sai mu zama abun wulaƙantawa? Kuma ba kyauta suke biyan mu ba aiki muke yi masu." Dan murmushi Alima ta yi ta ce mata kada hakan ya dame ta, ta ɗauka wurin neman halak dama sai an sha wahala. Bayan Nailah ta buɗe lemun, yar purse ɗinta da ke ajiye a saman hannun kujera ta dauko ta buɗe ta, wani abu ta ciro kaman sachet ɗin magani ta ballo guda biyu, marfin lemun da ta buɗe ta cire ta saka abun, maida marfin lemun ta yi ta tufe ta dauka tare da ɗan girgiza shi, aje lemun ta yi ta maida sachet ɗin cikin purse, bayan ɗan lokaci ta buɗe lemun ta fara sipping a nutse, duk abun nan mom Jameela na zaune tana bin ta da ido, juyawa Nailah ta yi ta kalle ta da wani shu'umin murmushi ta ce, "Ko zaki sha ne?" Da sauri mom Jameela ta ce, "Wa! wannan ai naku ne manya." Naila ta yi mata wani kallo ta ce, "Au haba? Ni zaki ma pretending, kin manta na san har da auren ki kina using na su, ko sai na tuna maki lokacin da na zauna wurin ki lokacin da kika haifi Deen a Funtua, a gabana kike komai, kin ɗauka bani da wayau ban san komai ba. Kuma na san tun lokacin ba bari kika yi ba." Ta ƙarasa tare da ɗage mata gira, mom Jameela ta wani tamke fuska, Nailah ta shiga sakin wani murmushin rainin wayou, cikin haɗe rai mom Jameela ta ce, "Wannan kina magana ne akan can baya ba yanzu ba, na bari since, so bana son kina kawo maganar." Nailah ta ɗan ta6e baki tana ci gaba da shan lemun ta tana wani juya ido, kauda ido mom ta yi zuciyarta na tuno mata da can baya lokacin da take amfani da irin drugs ɗin da ta koyi sha a lokacin da ta fara karatu a Buk, kauda tunanin ta yi ta kalli Naila dake ta sipping lemun and pressing her phone at the same time, tambayarta mom Jameela ta yi akawo mata abinci ta ɗan girgiza mata kai ta ce ta ci kafin ta fito, "A ina kika sauka ne?" a taƙaice ta bata amsa da "Transcorp..." mom Jameela ta ce, "Ke da waye kuka zo." Kamar baza ta bata amsa ba, ta ce, "Wani ne, baƙo ne daga ƙasar Ghana ya zo Kano muka haɗu ya buƙaci na rako sa nan." Aunty Jameela da ta bita da idanu sam bata yi mamakin jin namiji ta rako ba don duk sun san barikinta take bugawa a fili, ba kasafai ma ta cika zama a gida ba can Kano, mom Jameela da ke kallonta ta ce halan mai arziƙi ne mutumin shiyasa har ta amince ta biyo shi, wani bazawarin murmushi ta saki ta ce, "Wato ni ga lashe money ko, koda yake gaskiya ne, zan amince na biyo sa ne ba tare da kaya a hannunsa ba, yana da arziƙi kam tun da ko ɗaki da ya kama 2m per day" Mom Jameela ta ɗan jinjina kai ba tare da ta yi ja akan hakan ba don ta san a Transcorp hilton hotel har ɗakin da ya fi hakan kuɗi a rana ɗaya akwai, shiru ta ɗan yi wani abu na mata yawo a rai, cikin son tabbatarwa tana kallonta ta ce, "I thought ma da Alhaji Muhmud kuka zo kamar yadda kika saba, Allah Ya sa dai baku tare yanzu." Nailah ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi yar dariya ta ce, "Rabuwa kuma! Ni da babyn nawa, yadda nike ji da man ɗin nan ai ban iya rabuwa da shi, yana daga cikin mazan da suka iya tafiyar da ni yadda nike so." Da wani expression da ya bayyana yar damuwa akan fuskar mom Jameela ta ce, "Amman dai Nailah wllh abun da kike baki kyautawa, yakamata ki rinƙa tunani kuma ki yi hallaci, mutanen nan wani irin alkhairi ne basu yi mana ba a rayuwa? A lokacin da abbanmu ke aiki a gidansa ba irin alkharin da basa yi mana shi da matarsa, amman a ce ki rasa da wanda zaki yi tarayya sai mijinta, abun takaicin ma kuma ta sani, haba!" Dakatawa Nailah ta yi da shan lemun ta jefa mata wani kallo ta ce, "To miye laifi na anan don na so mijinta, ko kuwa don yana mijinta sai ya haramta in yi tarayya da shi taƙamar ta yi mana wani alkhairi, ina itama cin arziƙi take, don haka nima sai a bar ni in ci rabo na." Wannan karon da ƴar fusata mom Jameela ta ce, "Amman ai bata hanyar da ya dace kike yin soyayyar da shi ba, ya fi ma a ce auren shi kika yi da irin wannan tarayyar da kike yi da shi." Nailah ta yamutsa fuska ta ce, "Duk wannan abun saboda yana baban ƙawarki ne, farko ba auren nashi na so yi ba ita matar tashi ta nemi yi ma mutane iskanci, shine ai muka nuna mata ita jaririya ce a bangaren, ba a auri mijin nata ba tun da hakan take so, amman kuma tana ganin ana juya shi ba yadda ta iya. Next week ma zamu tafi Dubai da shi." Ta kai maganar tana juya fararen idanunta tare da sipping lemunta, baƙin ciki da takaici ne ya turnuƙe mom Jameela, ba tun yanzu ba ta tsani tarayyar su biyun, gashi yanzu arziƙin alhaji Muhmud din ya fi na da sosai, ba karamar hidima yake ma Nailah din ba don har ƙasar waje ya fitar da ita ta yi karatu, sannan dalilin ta sam yanzu bai damu da matarsa ba hajiya Aisha, baƙin ciki kawai take ƙunsa dalilin tarayyar da Nailah ke yi da mijinta, saboda wannan dalilin ne ya sa ƙawancenta da Sophie ɗiyar alhaji Mahmud tuni ya lalace, kuma bata ga laifin ta ba da ta daina alaƙa da