← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 197

Sashe 31

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Jameela sun kasance ƴan Kano duk da asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane daga Nijar suke, ahalin su sun kasance nau'in mutanen da ake kira da sadakar yalla, wanda suke wani rukuni daga cikin mutanen da ake kira buzaye. asalin garin kakanninsu a Nijar ya kasance ɗan karamin gari a hamada, inda rayuwa take matuƙar wahala, sun shigo Najeriya cikin ayari da ya ƙunshi dangi da kuma wasu ƴan garin su don samun sauƙin rayuwa. A lokacin iya yayan mahaifin su Jameela mai suna Amadu kawai suka haifa, daga baya a nan Kano aka haifi mahaifinsu Jameela wato Abdullah, sai ƙanwarsa wadda ita ce kuma ta ƙarshe a ɗakin su babansu mai suna Maryam. Mahaifiyar su Jameela wato Haleema ta kasance yar'uwar babansu ce, matsayin ɗiyar ƙanin babanshi ce, kuma har da iyayen nata aka zo garin Kano. Itama Haleema a nan Kano aka haife ta kuma ita kaɗai iyayenta suka haifa, mahaifiyarta na da cikinta Allah ya yi ma mahaifinta rasuwa sanadin mota da ta buge shi, bayan watanni da haihuwarta itama mahaifiyar tata ta rasu, hakan yasa rainon ta ya dawo hannun mahaifiyar baban su Jameela. Farkon zuwan kakannin su Kano, sun kasance basu da taƙamaiman matsugunni, daga baya suka fara aikin gadi a wuraren da ake manyan gine-gine ana basu wurin zama. Amadu yayan babansu Jameela ya kasance jajirtacce mai ƙoƙarin neman na kai, tun yana ɗan matashi yake bin kasuwanni yana yin aikin yaron shago da dakon kaya, daga baya ya fara yin sana'oi irin su sayar da turare, ƴan kunne, zabba da sauran su, sa6anin mahaifin su Jameela da ya taso a malalaci saidai komai Amadu ya yi masa. Sosai Allah Ya buɗa ma Amadu har ya siya ma iyayensu ɗan madaidaicin gida gaba ɗaya suka koma, ya kuma saka mahaifin su Jameela a makaranta tare da ƙanwarsu sai mahaifiyar su Jameela da iyayen su ke riƙo wadda kusan sa'ar Maryam ce. Daga baya Amadu ya auri wata bahaushiyar yarinya da suke soyayya yar nan Kano mai suna Hafsa, wadda da ƙyar iyayenta suka yarda ta aure shi saboda asalin sa. Ƙanwar su Maryam na aji ukku na sakandire wani alhaji ya fito neman aurenta aka bashi musamman ganin yana da kuɗi, a lokacin ne shima Abdullah ya bayyana ma iyayensu cewa yana son auren Haleema, farko ta nemi bijire ma auren shi saboda tana ganin Maryam ta samu babban mutumi mai kuɗi, shi kuma ta raina ma girmansa gashi bai da komai ya ƙi kuma tsayawa ya yi sana'a, duk in da ya fara aiki ba a ɗaukar lokaci ake sallamarsa saboda maular tsiya ga rashin gaskiya, ga kuma shaye-shaye da ya fara sakamakon biye ma abokan banza. Duk da Haleema ta nuna bata son auren Abdullah, haka iyayen shi suka tursasa mata har da su gorin rainon ta da suka yi, tana ji tana gani aka yi mata auren dole da shi, suka tare a ɗakinsa dake a gidan, ita kuwa Maryam gidan da aka kaita mai kyau har da gate. Farko Haleema ƙin amince ma Abdullah ta yi, sai da ta kai sai ya haɗa mata da bugu sannan abu ke shiga tsakanin su, da ta yi mashi laifi sai ya kai ƙarar ta wurin iyayensu a yi ta mata faɗa, a haka ta samu cikin Jameela ba wata kulawa da take samu ta buƙatun mai ciki daga wurin shi, sauƙin ta Amadu da ke taimaka mata, dama duk shine ke ɗaukar dawainiyar su, wanda a lokacin babbar mota yake ja yana kai kaya da ɗaukowa daga kudu, ta 6angaren Maryam ma tana taimaka masu bakin gwargwado. Lokacin da cikin Haleema ya kai wata tara ta haifo santaleliyar ɗiyarta, tun a asibiti ake ta santin kyawun Jameela, haka ma mutanen unguwa musamman jin yadda ake zuzuta kyawun jaririyar wasu ke zuwa barka, tun da Allah Ya sa Haleema ta ɗaura ido kan kyakkyawar jaririyar tata wata irin ƙaunar yarinyar ta shiga zuciyarta, wannan dalilin ne kuma ya sa ta yada duk wasu makaman ƙiyayyar da take ma Abdullah ta saki jiki suka ci gaba da rayuwa irin ta ma'aurata. Ba irin ƙoƙarin da Amadu bai yi ba wurin ganin ya ɗaura Abdullah hanyar da zai gyara rayuwarsa ya kama kwakkwarar sana'a ba kamar da ya fara aje iyali, sai ya yi kaman ya canza sai kuma ya koma gidan jiya. Bayan wasu shekaru kakannin su Jameela duk suka rasu, lokacin Maryam sun bar Kano sun koma Lagos da zama kuma tana ci gaba da taimakon su musamman da kuɗi.

Akwai wani makwabcin su mai suna Alhaji Mahmud, ya kasance attajirin mai kuɗi ne da ke yin kasuwanci ƙasashe daban-daban, lokacin da su Jameela suna yara mahaifin su ya ta6a yin aikin gadi a gidan Alhaji Mahmud ɗin, wanda gidan katafaren gida ne na gaske, daga baya ne Alhajin ya sallami mahaifin su Jameela saboda ya gaji da halin shi na maula, duk da albashin shi da ya tsare mashi yake bashi akan lokaci sannan da wasu alkhairan da yake mashi kamar na kayan abinci haka in salla ta yi har kuɗi yake bashi don ya yi ma yaran shi kayan salla amman hakan bai isa ba, duk wata matsalar shi sai ya kawo ma alhajin, ko iyalan shi ne basu da lafiya alhajin ne zai biya kudin asibiti ko magani, ganin gaba daya ya maido mashi nauyin iyalinshi da kuma yadda su Jameela suka mayar mashi da gida tamkar na su, a nan suke wuni su ci abinci wani lokacin har kwana, sau da yawa sai ya yi ma matarshi hajiya Aisha magana kan ta sallame su su koma gidansu sannan wani lokacin suke tafiya, waɗannan dalilan ne suka sa Alhaji ya sallami babansu daga yi mashi aikin gadin ya nuna mashi a yadda yake da iyali kamata ya yi ya nemi wata hanya da zai rinƙa samun isassun kuɗin da zai rinƙa ɗaukar nauyin iyalan shi, har da jari ya bashi don ya fara yin sana'a, sam baban su Jameela bai so hakan ba don ya saba da samun komai bati, ƙarshe dai ba wata sana'ar kirki da ya kama haka suka cinye kuɗin ya koma yin maulan da ya saba da kame-kamen sana'oi, aka ce zama da maɗaukin kanwa, itama matar tashi ta yi aikatau a wasu gidajen masu kuɗi, sai dai duk abu ɗaya ke sa bata daɗewa ake sallamarta, ita ban da maula da rashin gaskiya har da munafunci, ƙarshe ta koma yin sana'ar kitso, gidanta ya koma matattarar gulma da ɗaura mata kan gur6atacciyar hanya. Duk da mahaifin su Jameela ya bar aiki a gidan Alhaji Mahmud hakan bai sa sun daina zuwa ƙwaƙwa ba, ba kamar Jameela da take ƙawance da ɗiyar Alhajin wadda tsararta ce mai suna Safiyya suna kiranta da Soffy.

A haka su Jameela suka taso a wannan gidan, saidai iyayen su sun kasance ba irin iyayen nan bane masu bama tarbiyyar ƴaƴansu muhimmanci, hakan yasa suka sake su suna abun da suka gadama, rashin halin iyayensu yasa wasu daga cikin yayan suka raina ma arzikin iyayen suka zama masu kwaɗayi da hangen na wani, sun kasance irin waɗanda basu da gashin wanccan su ce sai sun yi kitson wance, hakan yasa suke liƙe ma yaran masu kuɗi ga yin samarin tsiya, da yake Allah Ya yi masu baiwar kyau, gaba ɗaya yaran gidan su ba munana bane saidai kyawun wani ya fi na wani, saboda kyawun dake gare su hakan yasa suke yin samari masu kuɗi ko yaran masu kuɗi, a wurin su suke samun kuɗaɗen da suke fantamawa suke yin rayuwa tamkar yaran masu hannu da shuni, wanda idan baka san su ba aka faɗa ma iyayen su talakawa ne har rantsewa kana iya yi cewa ƙarya ne aka faɗa maka, to da yake suma iyayen nasu masu shegen son abun duniya ne hakan yasa sam basa kwa6ar su kan yadda suke samo kuɗi, ba kamar da yake suma suna yagar rabon su kuma ana kawo masu kayan daɗi suna ci, gaba daya sun maida yaran nasu kamar jari har hure masu kunne suke yi kan yadda suke da kyawu kada su sake su rinƙa kula maza marasa kudi, har huɗuba suke masu idan aka ce ana son su da aure kada su amince su yi aure da wuri su bari sai sun gama cin ƙuruciyar su in ba haka ba da an aure su zasu daina samun duk alherin da maza ke yi masu su koma sai yadda aka yi da su.
Chapter 31 · 0% Book details