← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 197

Sashe 182

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren magrib Deen ya isa Funtua, kaitsaye gidan hajiyar Ambasada ya nufa ba sabon gidan su ba, sosai hajiya ta nuna farin cikin zuwan nasa don bata san da zai zo ba, bayan yayi sallar magrib ya ci abinci, ɗakinsa da yake zama a bangaren hajiya ya wuce don ya huta, a lokacin ne suka yi waya da Salma ya sanar mata ya isa lafiya, don lokacin da yake hanya sau kusan ukku tana kiransa tana mashi ya hanya, a shagwa6e ta bayyana masa cewa gata nan tana ta kewansa ya rarrashe ta tare da tabbatar mata da sun kusa kasancewa tare na har abada, a lokacin ne bayan sun gama yin wayan shauƙi ya kwashe shi har ya yi posting hotonta a shafin sa na Ig. Bayan sallar isha Deen na kishingiɗe a saman gado yana latsa wayarsa, lokacin kiran mom ɗinsa ya shigo, jimm ya yi yana ta kallon kiran, a jikinsa ya ji kiran bana alkhairi bane, kaman ba zai ɗaga ba, can lokacin kiran ya kusa katsewa ya ɗan rufe ido ya buɗe tare da ɗaga kiran...ko amsa sallama da gaisuwar da ya yi mata bata yi ba, cikin ɗaga murya ta ce, "Deen! who is that girl you posted a picture of on Ig? Miye tsakanin ka da ita?" Deen ya ɗan yi shiru kafin a hankali ya ce mata sunanta Salma a Funtua take...ba tare da ta bari ya ƙarasa ba a ƙagare ta ce, "I didn't ask you all dat, mi ke tsakanin ka da ita nike son ji." Deen ya ɗan lumshe ido tare da yin shiru kaman mai shakkar faɗi mata, har sai da a ɗan fusace ta ce, "Deen are you there?" Ya ɗan sauke boyayyan ajiyar zuciya, in a low voice ya ce, "I'm in love with her...." Sagir na shiga ɗakinsu ya nufi wayarsa da ya jona caji, bayan ya ciro yana dubawa ya ga missed calls ɗin aunty Kubra, da sauri ya shiga kiranta yana a tsaye, aunty da Salma na zaune a falo sun baje abubuwan ciye ciyen da aka kawo masu har da cake ɗin suna ta party abun su, Salma ta kai hannu gefenta saman kujera ta ɗauko wayarta jin tana ringing, aunty da ke kallonta ganin ta saki faffaɗan murmushi ta tambaye ta waye, "Sageer ne." Ta bata amsa, da sauri aunty ta miƙo hannu ta ce ta bata wayar, aunty ta daga kiran ta kai kunne, kafin ta ce wani abu daga ɗaya bangaren da sauri Sageer ya ce, "Salma..." Aunty ta bashi amsa da ba ita bace, jin muryar aunty ya gaishe da ita ta amsa, tambayar ta ina Salma ya yi, aunty ta ce, "Wacece haka." ƴar dariya Sageer ya yi sanin aunty na da barkwanci ya yi tunanin wasa take masa, ya ce mata, "Salma ƙanwata dake nan wurin ki." Aunty ta ta6e baki ta ce ita bata san wata Salma ba, Sagir na ƴar dariya a ƙagare ya ce, "Aunty don Allah tana ina, wani abu nike son tambayar ta." Aunty ta ce, "Ai baka shirya yin magana da ita ba." Magiya Sagir ya fara yi mata kan ta bashi Salma, duk a tunanin shi kawai cikin barkancin ta ne take masa haka, aunty ta fahimci bai gane inda maganarta ta nufa ba, ta ce masa, "Baka ga abun da ke yawo a social media ba ne?" Sagir ya zaro ido da sauri ya ce, "Na gani, ai abun da ya sa na kira ke nan in tambaye ta, aunty da gaske ita ce Deen ya ɗaura a Ig." Aunty na murmushi ta bashi amsa da ita ce, muryarsa cike da mamaki ya tambayi aunty mike tsakanin ta da shi, aunty ta ce mi yake tunanin zai sa shi saka ta a shafin sa, Sageer ya ce, "Aunty ke nan da gaske soyayya suke?" Ta ce masa kamar haka, a ƙagauce cike da mamaki ya ce mata amma ya aka yi ta fara soyayya da shi, aunty ta ce, "Oho, nima ban sani ba." Da sauri ya ce, "Aunty don Allah tana ina, ki bata in yi magana da ita." aunty da ta kai abu baki tana taunawa ta ce, "Ita wa?" Ya ce mata Salma, "Ashe baka shirya yin magana da ita ba, ai idan maye ya ci ya manta to uwar ɗa bata mantawa, idan ka ga na bata ka yi magana da ita sai ka tabbatar da alwashin da ka sha kanta." Nan take Sageer ya gane inda maganar tata ta dosa, dariya sosai ya saka ya ce ta manta da wannan kawai don Allah ta bata, aunty ta ce, "Karyar iskanci kake Sageer, Allah idan ka ga na bata sai ka ambace ta da yadda ka sha alwashin zaka rinƙa kiranta, Sagir nata dariya ya ce to ta bata, aunty ta ce , "In ba wa?" Cikin dariya ya ce, "Yaya Salma." Aunty ta saka dariya haka Salma da duk tana sauraran su itama dariya ta ke, aunty ta miƙa mata wayan, itama ta ɗauki tata dake a gafe ta miƙe ta nufi ɗaki don yin magana da innarsu Salma.....Sageer na gama yin magana da Salma jiki na rawa ya fito waje ya koma wurin su Aliyu, cikin washe baki yake tabbatar masu da abun da suka gani gaskiya ne soyayya Deen yake da Salma har ma sun yi zancen aure, suma duk suka cika da mamaki haɗe da farin ciki, Sageer da ya kasa rufe baki yana ta dariya cike da zolaya ya ce ma Aliyu, "Kai baka yin kishi ne, an ce budurwar ka na soyayya da wani har za su yi aure amman kake farin ciki." Aliyu da ke dariya ya ce, "Hauka ma ke nan nike da zan yi kishi, an gaya maka ana kishi da irin su Deen ne, koda a ce soyayya tsakani na da ita ta yi ƙarfi ya ce yana sonta, to zan goya bayan ta koma wurin shi ne balle ma dama ba wani shiga na samu yi a wurin ta ba." Gaba ɗaya suka babbake da dariya, Ibrahim ya ce, "Gara kar ka bari kanka ya yi murfi qur'an, ko banza kai ma ka dangwali arziki." Aliyu ya ce ai shine, Sageer dai fuskarsa ta kasa 6oye farin cikin da yake ciki, sai faman jinjina kai yake shi kaɗai ya san mi yake hange idan al'amarin ya kasance, can ya ɗaga hannuwa sama yana faɗin, "Allah Amin...Ya Allah Amin al'amarin nan ya tabbata su yi aure." Duk sauran suka amsa da amin.....Bayan aunty Kubra ta kira innarsu Salma kiran ya shiga, innar ta su ta ɗauka suka gaisa, aunty ta tambayi duk ya suke kafin ta ce, "Kira na yi don in yi maku albishir." Innarsu Salma ta ce, "To Allah Ya sa mu ji alkhairi." Nan aunty ta shiga yi mata bayani tiryan tiryan tsakanin Salma da Deen, mamaki ya sa innarsu kasa yin magana na ɗan lokaci, da tsananin mamaki ta furta, "Wai Kubra da gaske kike wannan maganar? Shi jikan hajiyan ambasada ɗin ne yake son Salma?" Aunty ta ce, "Wllh yaya Fiddausy yadda kika ji na faɗa maki, abun da ya sa tun farko ban sanar maku ba na bari ne in ga abun ya kankama tukunna, to yanzu zancen da nike maki ma daga nan da ya zo nan Funtua ya wuto, kuma saboda maganar auren su zai zo kamar yadda ya ce mata." Innarsu Salma was completely Speechless, jin abun take kamar mafarki sai faman jinjina maganar take a cikin rai, "Don haka sai ku kasance a cikin shiri." A sanyaye innar ta ce to, aunty ta ce, "Yaya Fiddausy ya na ji muryarki kamar baki farin ciki." Innar su Salma ta yi dariya ta ce, "Ina farin ciki mana Kubra, kawai abun ne...sai nike ganin kaman shi ɗin ai ya fi ƙarfin Salma nesa ba kusa ba." Aunty ta ce, "A wurin mu dama haka zamu gani, amman a wurin ubangiji duk ɗaya suke, don haka fatan alkhairi zamu yi." Innarsu Salma ta ce, "Haka ne to Allah Ya tabbatar mana da alkhairin." Aunty ta amsa da Ameen, Da ɗan shakku Innarsu Salma ta sake cewa, "Amman Kubra kina ganin danginsa za su amince, ba kamar da akwai maganar aure tsakaninsa da ƴar uwarsa?" Aunty ta ce, "To ai ya ce gaba ɗaya zai haɗa ya aure su, don haka mu yi addu'a kawai yaya." Innarsu Salma ta ce to, lokaci guda ta yi murmushi tunowa da alwashin da Sageer ya ɗauka a baya, ta ce, "Sageer kuwa ya san da maganar?" Aunty ta yi saurin cewa,"Ya sani, yanzun nan muka gama waya da shi, cike da zumuɗi ya kira baby yana son tabbatar da maganar soyayyan ta su da ya gani a social media, kin san wai shi har ya manta da alwashin da ya sha, ai kuwa na ce wllh ƙaryarsa ta sha ƙarya, sai da ya kira ta da yaya sannan na bata wayar." Innarsu Salma ta yi dariya kafin ta ce, "Ni lokacin koda na saka baki a maganar nike nuna masa zai iya ganin ya kamu da son ta, kawai na yi maganar ne a zuwan wasa ba wai don ina tunanin hakan zai yuwu ba." Aunty ta ce, "Gashi kuma kin ga ya yuwun, ai abu irin wannan mutum bai cika baki tun da komai na Allah ne." Innarsu Salma ta ce hakane, "Yanzu dai yaya sai ku zama cikin shiri, ki sanar ma baban su Sageer girma ya zo za a fara aurarwa." Inna na dariya ta ce to shike nan zata sanar masa, tambayar ina Salma innar ta yi, aunty ta ce, "Gata can a falo na baro ta suna magana da Sageer, kin ga cikin ma yin party muke da abubuwan daɗi da surukin namu ya kawo mana, har nike cewa Allah sarki nesa bata maganin kusa, da kuma kun ta6a abun arzikin surukin namu...yaya baki ga fa uban hidiman da ya yi mata ba, ubansun kaya ba ƴan nan ba, bari dama duk mun ɗauki hoton kayan, zan turo ma Sageer ku gani." Fuskar Innarsu Salma cike da farin ciki ta amsa da to, bayan sun ɗan ƙara yin magana suka yi sallama. Suna gama yin waya ta shiga kiran babansu Salma, tsananin mamaki ya shiga bayan
Chapter 182 · 0% Book details