← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 197

Sashe 3

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali ƙarar jirgin ta fara raguwa, yayin da yake neman tsayawa, bayan da jirgin ya tsaya sai da aka ɗan dauki lokaci kafin ƙopar shi ta fara sauka a hankali tana buɗewa, jim bayan ɗan lokaci a nutse wani matashin saurayi ya sako kai waje daga cikin jirgin, dakatawa ya yi a bakin ƙopar jirgin ya ɗan ɗaga kansa tare da lumshe idanunsa ta cikin baƙin gilashin fuskarsa, wai aka ce komai daɗin wuri gida daban ne, a hankali ya buɗe idanunsa wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali yake ji na ziyartarsa. A yanayin halitta, matashin saurayin dogo ne amman ba irin tsawon da ya wuce misali ba, fatar shi fara ce tas irin farin nan mai tafiya bai ɗaya, daga fatar tasa zaka fahimci hutu ya zauna masa sosai yadda take sumul, yana da kyawun fuska wadda da idanu sun kalla zasu shaida hakan, kwantaccen sajen dake zagaye da fuskarsa ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tasa, duk da gashin baida cika sosai wanda hakan ya sa ana iya ganin ɗan lotsawar da gemun shi ya yi wato yana da chin dimple, sumar kansa da gani tana da tsawo yadda aka yi baya da ita ta kawo har saman wuyansa baƙa wuluk da ita sai sheƙi take alamar ta sha gyara, a jikinsa yana sanye da tailored suit farare ƙal, maƙale a jikin wuyan kayan bow tie ne kalar green mai ɗan duhu haka a jikin aljihunan jacket ɗin kayan nan ma an yi adon kalar green, daga jikin ƙasan zagayen hannun kayan nan ma akwai ratsin green, ƙafafunsa na sanye da haɗaɗɗun rufaffun fararen takalma, haka wutsiyar hannunsa na ɗaure da rantsattsar farar agogo, saman kan agogon sai sheƙi yake yana ɗaukar ido tare da bada launin green.

Shin wanene wannan matashin mai cikar halitta da ya gaji da haÉ—uwa?

NURADDEEN IBRAHIM AMBASSADOR ke nan, wanda fitacce kuma ƙwararran ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai ne dake buga wasa a babbar ƙungiyar ƙwallon kafa ta IMPERIAL LONDON FC (ILFC) dake a England. Asalin tushen shi ƙasar Nigeria ne duk da ba anan aka haife sa ba, mahaifinsa Alhaji Ibrahim Nuraddeen ɗan asalin jahar Katsina ne haifaffen garin Funtua. Kakansa marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador ɗan asalin garin Funtua ne wanda tushen family ɗin su babban family ne da suka yi gadon arziƙi a garin. A lokacin da Alhaji Nuradden na raye ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje wato Ministry of Foreign Affairs inda ya yi aiki a wasu ƙasashe da dama har ya kai matakin ambasada kafin ya yi ritaya. Yaran Alhaji Nuradden da ya haifa biyar amma ukku ne yanzu ke raye a duniya, Alhaji Sa'ad shine babban ɗan shi wanda yanzu haka yana zaune a garin Funtua tare da iyalinsa. Alhaji Sa'ad ya gaji mahaifinsa ta bangaren aiki in da shima ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje har zuwa yin ritayarsa, yanzu yana harkar kasuwanci da kuma noma wanda dama gadon family ɗin su ne. Mahaifinsu wato Alhaji Nuradden Ambassador lokacin da yake raye babban manomi ne da ya mallaki manya da ƙananun gonaki a sassa daban-daban a cikin ƙasar nan, suna da ma'aikata da dama dake aiki a ƙarƙashin su, yayin da wasu gonakin nasu kuma ake yin hayar su. A duk shekara ba ƙaramin noma ake yi a gonakin nasu ba, akwai gonakin da irin su auduga kawai ake nomawa da waɗanda ake noma sauran abubuwa daban-daban, kuma musamman akwai manyan kamfanoni da ke siye amfanin da aka noma da zarar an gama wanda ba ƙananun kuɗi suke samu ba. Bayan noma kuma suna yin kiwo a manyan gidajen gonakin da suka mallaka.

Alhaji Sa'ad yana da yara shidda, Fahad shine babban É—ansa wanda yanzu haka likita ne dake aiki a Zaria, daga shi sai Sadeeya tana karatu a ABU Zaria, akwai Ibrahim suna ce masa Khalil sai Abubakar Sadeeq da Fatima suna ce mata Binafa sai auta Muhammad Ayden.

Alhaji Ibrahim shine na biyu wanda yanzu haka É—an majalissar tarayya ne dake zaune a garin Abuja shi da matarsa Hajiya Jameela suna da yara guda biyar, Nuraddeen wanda ya ci sunan kakansu shine babba sai Omar da Haleema suna ce mata Leemarh don sunan kakarsu ta wurin uwa aka saka mata wato mahaifiyar Hajiya Jameela, sai Sa'ad wanda ya ci sunan yayan mahaifinsu suna ce mashi Sultan sai autar su Fateema wadda ta ci sunan kakarsu ta wurin uba suna ce da ita Batool.

Aunty Murja ita ce ta ukku, Malamar Jami'a ce tana aure a garin Kano tana da yara ukku, biyu mata sai namiji É—aya.

Hajiya Binta ita ce matar marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador wadda yanzu haka take zaune a cikin garin Funtua, ta kasance dattijuwa mai matuƙar kirki da karamci, tana da mutunci sannan ga alheri musamman ga mutanen da take rayuwa da su, ta kasance a koda yaushe burinta ta saka farin ciki a cikin zukatan al'umma musamman marasa ƙarfi, mutanen gari suna yi mata laƙabi da Hajiyar Ambasada haka ƴan cikin unguwar da take suna kiran gidanta da gidan Hajiyar Ambasada.

Dangane da yadda Deen ya zamo ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai kuwa, akwai ƙanwar mahaifiyarsa mai suna Aunty Safnah da suke zaune a London ita da mijinta Maleek sai ɗiyarsu guda ɗaya Basma wadda ita kaɗai ce Allah ya basu. Maleek ya kasance babban abokin mahaifin Deen wato Alhaji Ibrahim, ta sanadiyar abotar su ne har ya haɗu da ƙanwar Hajiya Jameela ya aureta. Maleek ya kasance ƙwararren injiniyan fasaha da ya mallaki babban kamfani a birnin London, tun bayan da Deen ya kammala karatunsa na ƙaramar secondary anan Nigeria ya koma wurin su da zama, bayan saka shi a makaranta don ƙarasa karatunsa na secondary, lokacin malamansu suka fahimci yana da baiwar ƙwallo, don yadda yake bada himma a kan ƙwallo baya ba karatu himma, hakan ya sa malamin su na wasanni ya fara magana kan idan aka goya mashi baya zai zama babban ɗan kwallo har suka tuntu6i mahaifinsa mai ruƙonsa wato Maleek, bayan ya tuntubi Deen don jin ra'ayinsa, ya nuna masa yana son zama ɗan ƙwallo, hakan yasa Maleek ya tsaya masa da taimakon malamin nasu aka maida shi makarantar koyon ƙwallo, cikin lokaci ƙankani ya fara samun ƙwarewa sosai. Tun yana buga kwallo a junior team har ya koma yana bugawa a senior team, yana a shekara 17 ya yi signing da babbar kungiya ta farko da ya fara buga ma wasa a nan London, daga baya ya koma wasu kungiyoyi biyu har kawo kungiyar da yake buga ma wasa a yanzu, wadda Tsohuwar ƙungiya ce kuma sananna. Laƙabin da ake yi ma ƴan kungiyar shine The Imperials ko The Lions of London, suna da babban filin wasa mai ɗaukar dubbanin mutane mai suna Imperial Crown Stadium. Yanayin launin rigarsu ta gida wato jersey shine fari da ratsin golden wanda ke nuna daraja da iko, rigarsu ta waje kuma tana da launin baki da ja, sai kalar rigarsu ta ukku mai launin shuɗi mai duhu. Kungiyar Imperial London FC ta samu manyan nasarori masu tarin yawa daga manyan gasannin ƙwallo, an san su kuma da yin kasafin kudi mai tsada wajen sayen fitattun ƴan wasa daga ko'ina cikin duniya. Sannan club din na da salon suna mai ɗauke da alamar ƙarfi, mulki, da tarihi, irin wanda ke da alaƙa da masarautar Birtaniya.

Ba ƙaramar shahara Deen ya yi ba a harkar ƙwallo don ya iya ta sosai ya san duk wasu dubarun cin ƙwallo, mutane na kiran sa da ɗan baiwa, da wuya ka ga an yi wasa da ƙungiyarsu bata ci ba saboda ta haɗa zaratan yan ƙwallo, hakan ya sa ƙungiyarsu tana ɗaya daga cikin wadanda ake jin shakka. A shekaru Deen ba wani babba bane don bai wuce 26 ba, sai dai in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun sosai saboda ƙirar jikin shi irin ta zaratan ƴan kwallo ce.

Wannan ke nan game da fitaccen jarumin ɗan ƙwallo, wanda a duniyar ƙwallo aka fi sani da DEEN JR. Wasu kuma suna kiran shi da NUREE JR.

Cigaban labari.....

Maida idanunsa ya yi kan mutanen da suka zo tarbarsa, a hankali ya saki wani ƙayataccen murmushi tare da gyara zaman jacket ɗin shi kafin a nutse ya fara taka matattakalar jirgin yana saukkowa cikin aji, daga yanayin shigar kayan jikin shi zaka fahimci ya yi shigar ne don nuna girmamawa da kuma ƙauna ga ƙasar shi don kayan na ɗauke da kalolin tutar ƙasar Najeriya ne wato kore da fari. Daga yanayin yadda kayan suka amshi jikinsa zaka fahimci musamman shi aka ƙera ma kayan kuma ba ƙaramin kyau shigar ta yi masa ba.
Chapter 3 · 0% Book details