Sashe 137
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun iso gidan aunty Kubra ta saka Sagir ya fita ya buɗe masu gate, ta kutsa motar cikin gidan, Salma data fito ta bi gidan da kallo don ba shine gidan da ta san auntynta a ciki ba, Sagir ya kulle gate ya nufo su shima yana kallon gidan wanda ƙaramin estate ne mai ɗauke da gidaje biyu, boot aunty Kubra ta buɗe ita da Sagir suka fiddo da kayan su, koda Salma ta zo zata ɗauka hana ta ta yi ita ta kama trolley ɗin ta shi kuma Sagir ta ce ya ɗauko jakarsa da ƙatuwan ledan, da ɗayan hannunta ta kama na Salma suka nufi cikin gidan inda part ɗinta yake, bayan sun shiga cikin falo nan ma Salma ta bi shi da kallo, aunty Kubra tana murmushi ta ce, "Baby kin ga gidan da nike yanzu ba wanda kika sani ba." Salma ta ɗaga kai ta ce, "Amman yana da kyau." aunty Kubra ta ce, "Eh ba laifi, 2 bedroom ne sai kitchen da store." Salma ta ɗaga kai, aunty Kubra ta tambayi Sagir kayan sa ya ce mata jakar hannunsa ce, nuna masa ɗayan bedroom ɗin ta yi ta ce ya kai ciki nan ne ɗakin da zai zauna, kallon ledan da ya ajiye ta yi zata ɗauka da trolley ɗin hannunta ta kai ɗakinta wanda anan Salma zata zauna, Salma ta ce mata tsarabar ta ce a cikin ledan hakan ya sa ta ajiye ta a nan tana faɗin ta gode bari ta fito ta ga tsaraban da aka yi mata, Salma ta bita ɗakin tana fadin bari ta yi salla suka shiga tare, shima Sagir sai da ya yi salla sannan ya fito, a nan cikin falon saman carpet aunty Kubra ta baje masu kayan abincin da ta haɗa masu, ita kuma tana zaune tana duba uban kayan tsaraban da aka yo mata fuskarta cike da jin daɗi tana ta yabawa, wayarta dake a gefe ta fara yin ringing, bayan ta yi picking call ɗin ta kai kunne, daga ɗayan 6angaren innarsu Salma ta amsa mata sallamarta kafin ta ce, "Kubra sun iso kuwa? Inata kiran wayar Sagir a kashe ita kuma Salma wayar tana ta yin ringing amman bata ɗagawa" Yanayin muryarta akwai alamun damuwa, Aunty Kubra da idanunta ke akan su Salma tana ɗan faffaɗan murmushi ta ce, "Har yanzu basu ƙaraso ba yaya Fiddausy, kuma yadda kike ji nima hakan ne idan na kira." Cike da damuwa innarsu ta ce, "To Allah Ya sa dai lafiya, wllh baki ji ba har hankalina ya fara tashi." Jin da gaske a yanayin muryarta akwai alamun damuwa ya sa Aunty Kubra yin dariya ta ce, "Wasa nike maki yaya Fiddausy kin gan su nan tuni ma suka iso ga su suna cin abinci, shi Sageer wayarsa ta mutu ga ta can ya saka caji, ita kuma baby tata tana can cikin jakarta a ɗaki." Tana jin yarda innar tasu ta saki ajiyar zuciya tare da furta Alhamdulillah, aunty Kubra na dariya ta ce, "Su yaya Fiddausy mai ƴaƴa wato har hankalinki ya tashi." Innarsu ta yi dariya ta ce, "Ba dole hankalina ya tashi ba Kubra abu har da ƴar zuƙeƙiyar budurwar ɗiyata." Dariya sosai aunty Kubra ta saka, Sagir da ya tura abinci baki duk suna jin abun da innarsu ke faɗi saboda a speaker aunty Kubra ta saka kiran cikin ɗaga murya ya ce, "Wato innarmu damuwarki akan ta ne ko, ni kuma ko oho in kin rasa ni." Daga cikin wayar innarsu tana dariya ta ce, "Ba haka bane Sagiruna, saboda ita kaɗai ce yar macen tawa na faɗi hakan amman ba ina nufin kai ban damu da kai ba." Sagir ya ce, "Uhmm, ni ai da yake akwai wasu ke nan ko." Tana dariya ta ce a'a shima ta damu da shi, aunty Kubra ta ce wai haka take fama da kishin Sagir akan baby, innarsu ta ce uhm ai don ma ba tare suke ba da ta ga abu sai ka ce wata kishiyarsa, yar hira suka ƙara yi kafin suka yi sallama. Ba ƙaramin daɗin kasancewar su Sageer aunty Kubra ke ji ba, koda yaushe ta je aiki ta dawo zata iske gidan tsaf sun gyara mata shi har abinci Salma ta yi, sai dai ta ci ta huta, cikin ranakun da ba aikin rana take ba ko kuma tana off haka zata ɗauke su a mota su fita zaga gari har ta yo masu siyayyar kayan ƙwalama, sai da Sageer ya samu filin da yake zuwa yana buga ball a unguwar, sosai ya yi farin jini wurin waɗanda suke yin ball ɗin tare da sauran mutane ƴan kallo ba kamar da suka ji yana a cikin sabon team ɗin Deen Jr na Funtua. Satin Sageer biyu ya shirya komawa Funtua, kafin ya tafi aunty Kubra ta ɗauke su suka je kasuwa ta yi masa siyayya mai yawa har da su innarsu da su imrana duk sai da ta siya masu abubuwa, ranar da zai tafi a motar aunty Kubra tare da Salma suka raka shi tasha, sosai aunty Kubra ta yi masa godiya da addu'an Allah Ya kai shi lafiya, Salma na dariya ta ce, "Man Sagir Allah Ya tsare hanya sai na dawo." Ya yi mata wani kallo mai kaman harara ya ce, "Dama ki zauna a nan kowa ma ya huta." Aunty Kubra dake yin dariya ta ce, "Cika baki kawai, ka dai san ni hakan nike so ai, amman ba zaku bar min ita ba, nan lokacin da take wurina kafi kowa azalzalar mutane kan ta koma." Sagir na dariya jikinsa sanye da sababbin jeans da t-shirt a cikin kayan da aunty Kubra ta saya masa har takalman kafansa duk sababbi ne, ya ce, "Allah aunty Kubra yanzu idan kina son ta zauna mun bar maki." Aunty Kubra ta ce, "Saurin mi kake yi, in sha Allah next year by now muna tare." Sallama suka yi da juna don an fara sanarwar fasinjoji su shiga cikin mota za a tafi, Salma nata ɗaga masa hannu har ya shige cikin mota, sai da suka ga tashin su sannan suma suka shiga mota suka tafi. Leemarh tana ta shan hutun ta a Funtua gidan su Fahad, wani lokacin tana zuwa gidan hajiya ta kwana ko ita da Binafa, sosai ƴan gidan su Fahad ke jin daɗin kasancewarta a gidan ba kamar yadda ta sakar ma yaran jiki sosai ta maida Binafa kamar wata ƙawarta, shaƙuwa sosai ce ke ƙara shiga tsakaninta da yaya Fahad, har ta kai wani lokacin bata cin abinci sai ya dawo daga aiki su ci tare, wasu lokuttan idan ya dawo da wuri haka zai ɗauke ta da dare su fita su zaga gari ya siya mata abubuwan ƙwalama, part ɗin shi ma ita ce ke gyara masa, koda yaushe ya dawo haka zai iske shi fes yana ta ƙamshi, har ƙananan kayansa take wanke masa a washing machine idan sun bushe ta goge masa, duk da yana ce mata ta daina wahalan hakan amman ta ƙi bari sai dai ya yi mata godiya da nuna jin daɗin abubuwan da take masa, ko a wurin aiki lokaci bayan lokaci take kiran sa ta yi masa ya aiki, hakan ya sa shima da ya samu lokaci sai ya kira ta ya ji ya take, ku san koda yaushe idan zai dawo daga aiki sai ya dawo mata da wani abu matsayin tsaraba, ku san dai soyayya suke da juna ba tare da sun furta ba, hatta ƴan gidan sun fahimci shaƙuwar su har mom ɗin su. Da yamma suna zaune a falo gaba ɗaya waɗanda ke a gidan ban da Sadeeya da Khaleel da suke makaranta, duk idanunsu na akan babbar tv ɗin falon suna kallon indian drama har da momy, sallamar da suka ji an yi ta sa suka kai idanunsu wurin ƙofan shigowa, lokaci guda Leemarh ta saki ƙayataccen murmushi ganin wanda ya shigo, miƙewa ta yi ta nufe shi jikinta sanye da riga iya gwiwa da wandon ta da ya matse daga ƙasa kanta ta saka hula, daga gabansa ta tsaya tana murmushi ta ce, "Sannu da dawowa ya Fahad." Shima murmushi ne akan fuskarsa ya amsa mata tare da yi mata ya gida, ɗan juyawa ta yi kafin ta maido idonta kan shi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Duk wani iri nike ji ba daɗi saboda baka nan." Still da murmushi akan fuskarsa ya yi mata wani kallo ya ce to gashi ya dawo, hannu ta kai ta amshi yar jakar hannunsa suka ƙarasa cikin falon, duk su Binafa suka yi masa sannu da dawowa ya amsa, a kujeran gefe ya zauna ya kalli mom ɗinsa ya gaishe da ita, tana murmushi ta amsa ta yi masa ya aiki, Leemarh dake tsaye ta kalle shi ta ce, "Na shirya maka abinci?" Yana kallonta ya ce mata ta bari sai ɗan anjima baya jin yunwa yanzu, miƙewa ya yi ya miƙo hannu zai amshi jakar tana murmushi ta ce bari ta kai mashi sama ya ce ta basshi ba sai ta yi wahala ba tun da saman zai je, mom dai ta ɗauke idanunta daga kan su tana ɗan murmushi don zuwa yanzu ta fara zargin shaƙuwar tasu da wani abu, bayan ya amshi jakar ya bude, fiddo wata farar leda ya yi mai tambari a jiki ya miƙa mata, ta amsa tana murmushi tare da yi masa godiya, ya nufi bene ya haye zuwa part ɗinsa, buɗe ledan Leemarh ta yi ta fiddo abubuwan da ke ciki, su tuwan madara, peanuts, gullisuwa, popcorn da sauran tarkace dai wanda dama yana kawo mata su, buɗewa ta yi suka fara ci har da momy don ko ta ce baza ta ci ba haka zata matsa mata sai ta ci, shiyasa yanzu da ta bata abu take amsa ta yi godiya, suna cin abubuwan suna yin kallo, after some minutes Fahad ya sauko cikin falon da alama wanka ya yi ya saka jallabiya mai gajeran hannu sai ƙamshi yake saki, Leemarh ta ɗaga ido tana kallon sa da murmushi har ya ƙaraso ya zauna, miƙewa ta yi ta kai mashi sauran abubuwan ta ce gashi shima ya ci, tuwon madara guda biyu kawai ya ɗauka ya ce mata ya