← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 197

Sashe 142

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Leemarh ba sai ta sa wata ƙawarta da ta iya kitso sosai ta yi ma Leemarh yadda duk mai son ganinta sai dai ya zo ɗakin su ya ganta, sai da ana yin kitson ne ta samu suka yi hira har take tambayarta Binafa ta ce da sun zo tare, Leemarh ta ce itama ta so su zo tare amman saboda islamiyya kuma exams suke shiyasa ba su zo ba, haka akai ta kawo ma Leemarh abinci kala kala daga ɗakunan students, Sadeeya da ta yi niyyar yi mata girki sai dai ta fasa. Wuraren sallar la'asar su Khaleel suka dawo, tun yana can Sadeeya ta sanar da shi zuwan Leemarh kuma ya ga hotunanta da wasu students mata suka ɗaɗɗaura, kai tsaye hostel din su Sadeeya ya nufa ya kira Leemarh, lokacin har an gama mata kitson, shima hostel ɗin su ya nufa da ita aikuwa nan students maza suka yi mata dafifi a gaban hostel sai ka ce ita ce Deen ɗin, tun abun na ba Leemarh nishaɗi har ta fara gajiya, da kanta ta ce ma Khaleel ya maida ta wurin yaya Sadeeya. Misalin ƙarfe shidda Fahad ya zo ɗaukar ta, ƴan hostel ɗin su Sadeeya kusan fin goma suka yo mata rakiya, bayan sun ƙaraso wurin motar Fahad, Sadeeya ta buɗe back seat ta sassaka ledojin uwayen kyaututtukan da aka tara ma Leemarh, sallama suka yi da Sadeeya ta ce ai next weekend tana nan zuwa gida, suma ƙawayen Sadeeya suka yi sallama da ita ta yi masu godiya, tun da ta shiga cikin mota Fahad ya zuba mata ido yana kallon kitson da aka yaryara mata, har da na gaba ya zubo har zuwa wuya sannan kuma aka lanƙwashi shi aka haɗe dana baya aka kulle da ribbon ya sauka bayanta, Sadeeya ta leƙo suka yi sallama da Fahad ta yi masa godiya, kamo hannun Leemarh ta yi tana sake yin sallama da ita lokacin Fahad ya tashi motar, suna ta ɗaga ma juna hannu har da ƙawayenta a haka suka tafi. Bayan sun hau hanya sosai Fahad ya kalle ta suka haɗa ido, calmly ya ce, "Kitson ya yi kyau sosai." Murmushinta ya faɗaɗa ta ce, "Har da irin shi zaka koya ka rinƙa yi mini." Idonsa akan hanya yana murmushi ya ce, "To ai ban san irin style ɗin ba." Hannu ta kai ta zame kallabinta ta ce gashi ya gani, ya juyo yana kallon kitson da ya saƙu raɗam tsagar ta fita sosai farar fatar kanta ta fito, da sauri Fahad ya maida idanunsa kan hanya jin sitiyari na neman ƙwace masa, ya ce, "Kin ga zaki ja in sa mu yi accident saboda kyan kitson." Ƴar dariya Leemarh ta yi ta ce da gaske ya yi kyau, ya ɗan jinjina kai idanunsa a hanya ya ce sosai, "To da gaske kake zaka koya kitson ka rinƙa yi mani?" Ya ɗaga ido ya kalle ta suka haɗa ido ta cikin mirror, slowly ya jinjina mata kai tare da ɗan lumshe ido, murmushi ta yi ta sauke idanunta ƙasa. Bayan sun iso Funtua gidan hajiya Leemarh ta ce masa su biya ta gaishe da ita, a can ma hajiya sosai ta yaba da kitson Leemarh har ta ce mata ta rinƙa daurewa ana mata don ya ƙara mata kyau sosai, sai bayan sallar issha suka baro gidan suka nufi gidan su Fahad....
Chapter 142 · 0% Book details