← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 197

Sashe 120

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa falon mom Jameela ta yi ta zauna kan kujeran da ta tashi idanunta akan Nailah da ke yin waya, cikin ɗan haɗe rai ta furta, "Kawai sai in ta zama a hotel room kada na fito na sha iska?" Ɗan saurarawa ta yi kafin ta sake cewa, "Oh ke nan zargi kake wurin wani na je baka yarda da ina gidan sis ɗina ba." Ta ɗan yi shiru tana ƙara haɗe rai, can ta cire wayan tana faɗin, "Ka ji mani mutum da shegen kishin tsiya sai ka ce aure na yake, don ka zo da ni shike nan ban da ƴancin kaina, bai san ni ba haka nike ba, duk kuɗin namiji bai isa ya ce zai juya ni ba." Ta yi maganar tana pressing phone ɗin ta, ɗago kai ta yi ta kalli mom Jameela da ke tambayar ta ya aka yi ne, "Mutumin da na zo tare da shi ne, wai ya koma hotel din bai same ni ba shine zai wani tutsiye ni, har da wani wai akan mi zan fita ban sanar masa ba, sai ka ce irin ya biya sadaki na. Ni fa har da irin wannan abun ya sa har yanzu ko sha'awar aure bana yi, don bana jin zan iya tsayawa namiji ya rinƙa nuna mani iko." mom Jameela ta ɗan ta6e baki kafin ta tambaye ta ba shine ya kawo ta nan gidan ba ke nan, ta ce mata a'a, after some minutes sai ga kira ya shigo wayarta ta duba, ba tare da ta ɗauka ba ta ɗago ta kalli mom Jameela ta ce, "Shine ya zo ɗauka na." Miƙewa ta yi tana gyara rigarta, mom Jameela da itama ta miƙe tana kallonta da murmushi ta ce mata zata sake zuwa kafin ta bar garin, ta ce mata bata sani ba sai yadda ta kama, amman ko don ta ga su Leemarh za ta yi ƙoƙari ta dawo idan basu wuce ba, tare suka nufi hanyar barin falon, lokacin da suka fito motar mutumin da ya zo ɗaukar nata na a cikin harabar don yana sanar da su officer ita ya zo ɗauka suka bar shi ya shigo, bin motar mom Jameela ta yi da kallo wadda wata haɗaɗɗiyar baƙar jeep ce sai sheƙi take, gilashin motar tinted ne hakan ya sa ba a ganin wanda ke ciki, mom Jameela da ta ji tana son ganin mutumin, bayan sun tsaya daga gaban motar ta ce mata, "Baki yi masa magana mu gaisa." Ta furta ok tare da juyawa ta kai hannu ta ɗan ƙwanƙwasa glass, na gaban motar ne aka ɗan sauke, ta leƙa ta ɗan yi magana kafin ta juyo, ƙofar 6angaren driver aka buɗe mutumin ya fito, babban mutum ne don zai yi sa'an mijin mom Jameela koma ya ɗan ɗara shi shekaru kaɗan, kana ganinsa ka ga attajiri tun daga kan shigar da ya yi, ya sha manyan kayan farar shadda idan ka gansa kaman duka ke nan, tun daga kan hulansa da takalminsa da agogon hannunsa kana gani ka san za su yi tsada, mom Jameela na ta kallonsa a ranta tana raya, "Dube sa kaman na Allah..." Gefen Nailah ya tsaya da fara'a ya gaishe da mom Jameela ta amsa masa da ɗan murmushi, Nailah ta yi masa wani kallo kalan na waɗanda suka jiƙu da duniyanci ta furta, "Ko har yanzu ɗin baka yarda da inda na zo ba?" Ya wani bita da wani mayen kallo yana sakar mata murmushi ya ce, "Ai na yarda dama." Da yanayin hausarsa ba irin ta nan ba, ta ɗan jefa masa harara, ya yi ƴar dariya ya ce, "I'm sorry beauty, na koma room ne da muradin son in gan ki, sai na iske you weren’t there.", kuma bamu yi zaki je wani wuri ba." Ta ɗan ta6e baki kawai, mom Jameela ta ɗan kauda kai a ranta ta raya, "Yawancin maza dai duk munafukai ne, matarsa ko matansa na can Allah kaɗai ya san halin da suke ciki a gidansa." Ya sake ce mata, "Zamu iya tafiya? I have got a suprise for you when we get there." Ta ɗaga gira ta ce na minene, yana mata murmushi tamkar zai jawo ta jikinsa ya ce mata ta bari sai sun koma hotel zata gani, yadda yake mata magana ko kunyar mom Jameela baya ji, ko da yake Nailah ta riga ta bayyana masa daga wane irin kalan gida ta fito, kallon mom Jameela ta yi ta ce, "Aunty Jameela sai mun yi magana. Pls ki gaishe mani da su daughter Leemarh, ban ji daɗi da ban gan su ba." mom Jameela ta furta ok, sai kuma ta yi saurin cewa, "Yauwa na tuna, ina son baki saƙo wurin Aunty Shafa maganar ankon nan kada ta ɗauko da ni, don gaskiya bani da halin yin sa yanzu, ankon sun yi kuɗi almost 10m, ni kuma yanzu ba wani isassun kuɗi a wurina just last week na yi order kayan business ɗina as I told you." A kaikaice Nailah ta sakar mata wani kallon baki tsoron Allah aunty Jameela, sai kuma ta ɗan yi guntun murmushi ta furta, "To ki tambayi daddy mana, ba daɗi ace kowa zai yi ankon amman ban da ke." Ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Kawai na ga yakamata mutum na saka tunani, shine ya ƙara mani kuɗin da na yi order ɗin kayan, kuma yanzu sai in ƙara bijiro masa da wata buƙatar ai sai mutum ya ga ka raina ƙoƙarinsa. Ki bari kawai, I will see what I can do, idan kuma Allah Ya sa kayan sun iso kafin bikin na san zan samu ciniki sai in yi." Nailah ta gyaɗa kai da murmushi ta ce ok sai sun yi magana, duk abun nan alhajin na tsaye yana sauraran su, mom Jameela ta yi masa sallama yana murmushi ya yi mata godiya, har zata juya kuma sai ta tsaya ta ce ma Nailah ta manta ko lemu ba a kawo ma baƙon nata ba ko za su shigo, da sauri cikin fara'a ya ce mata no problem akwai lemu ma a cikin mota, daga haka ta nufi komawa ciki ya bita da ido, juyowa ya yi ya kalli Nailah ya ce gaskiya komai na su ya yi kama, ta ɗaga masa gira ta ce ita ce elder sis ɗin su. Bayan mom Jameela ta koma ciki, tana niyyar zama saman kujera ta ga Nailah ta shigo, fasa zaman ta yi ta nufe ta tana tambayar ta yi mantuwa ne? Dariya ce akan fuskar Nailah ta ce, "Wllh aunty Jameela kin fini bala'e wurin son kuɗi, you're the real lashe money, wato ke kina ganinsa har kin ga business." Itama dariya ce akan fuskarta ta ce, "Kin san ni ai bani wasa da dama ko kaɗan." Nailah ta ɗan girgiza kai ta ce, "To kin sayar, ya tura mani kuɗi a baki." Mom Jameela ta ɗan wara ido ta ce, "Are you serious?" Nailah ta ɗaga mata gira, "Har nawa?" Mom Jameela ta tambaya, Nailah ta ce, "Nawa kika ambata kuɗin ankon a gabansa." Ɗan jimm alamar tunani mom Jameela ta yi can ta ƙara wara ido da mamaki ta furta, "10m!" Nailah ta ɗaga mata gira, Mom Jameela ta ce, "Kai, da alama dai mutumin nan ba ƙaramin mai kuɗi bane, da na sani ma fin hakan na ambata." Nailah ta yi ƴar guntuwar dariya ta ce, "Saboda son kai ko, ke kaɗai kike son a tattare kuɗin a ba ke nan." mom Jameela ta sa dariya, Nailah ta sake cewa, "Kin ga yana jira na, ce masa na yi mantuwa na yi, dama don in zo in faɗa maki, sannan 50-50 za a yi, don haka zan turo maki 5m." Wani kallo mom Jameela ta yi mata, "Kamar ya 5m? Ba kin ce 10m ya bada a bani ba?" Nailah ta ɗage gira ta ce, "Yea, amman kin san ai bake kaɗai zaki samu kuɗin ba, tun da ni na kawo maki business ɗin dole nima na ɗauki share ɗina." mom Jameela ta 6ata fuska ta ce to amman tun da shi ita ya ba sai ta bata duka ita sai ta bata abun da ta yi niyya, Nailah ta ɗan girgiza mata kai ta ce dole yadda ta ce za a yi, idan kuma bata so shike nan zata yi amfani da duka kuɗin, sanin halinta ya sa mom Jameela ta ce, "Shike nan, amman dai ba maganar wanccan kuɗin da kika buƙata a wurina." Ta wani jefa mata kallo mai kaman harara ta ce, "No, wanda na buƙata daban, ina kuma jira. Idan kuma ya yi maki in riƙe 5m ɗin da zan turo maki ki ciko mani sauran, let me know." Daga haka ta juya ta nufi hanyar fita, mom Jameela ta bita da kallo, idan ka ganta zaka yi tunanin ta yi BBL ne yadda ƙugunta da mazaunanta suka fita sosai, amman kuma ba wani aikin hakan da aka ta6a yi mata, a cikin rai mom Jameela ta yanke kawai zata yi ma Sapna magana ta turo mata kuɗi sai ta cika mata ba sai ta amsa 5m ɗin ba, dama kawai ƙyashin ta fitar da kuɗinta ta ba Nailah ɗin take amman ba wani wai bata da kuɗi. Fahad zaune a falon daddynsa saman carpet yana rubutu a saman wasu takardu, ɗagowa ya yi ya miƙa ma daddynsa takardar da ya gama yin rubutun, alhaji Sa'ad dake zaune saman kujera idanunsa sanye da gilashi ya kar6i takardan yana dubawa, bayan ɗan lokaci ya ajiye ta a gefensa ya furta, "Komai ya yi daidai." Fahad ya jinjina kai, shiru suka yi na ɗan lokaci kafin alhaji Sa'ad ya yi ɗan gyaran murya ya fara magana, "Kwanaki can baya mun yi magana da kai kan yakamata ka fito da mata ka yi aure, ka ce zaka yi hakan, gashi yanzu almost a year da yin maganar amman shiru." Fahad ya ɗago suka haɗa ido da dad ɗin nasa, slowly ya maida kansa ƙasa, "Ka yi shiru." Daddyn ya sake faɗa, ba tare da Fahad ya ɗago ba ya ce, "Ban tsayar bane daddy." alhaji Sa'ad ya ce, "Why?" Still kansa na ƙasa ya ka sa bashi amsa, daddy ya ce, "Nasan dai ai baza ka ce
Chapter 120 · 0% Book details