← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 197

Sashe 78

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Salma ke ƙara yaba tsaruwar part ɗin yayin da take tafiya, tana zuwa ta ga rumfar irin ta shaƙatawa ce da kujerun zama, ciki ta shiga ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun ta ɗaga ido tana kallon cikin rumfar wadda itama ta burge ta, Deen na komawa ciki without wasting much time ya watsa ruwa ya canza kaya, bata daɗe zaune ba ya fito, ƙamshin turaren da ta ji ya ziyarci cikin hancinta ne ya sa ta juyowa ta hango shi ya nufo rumfar jikinsa sanye da jallabiya mai gajeran hannu, gyara zamanta ta yi ta sauke idonta ƙasa, bayan ya ƙaraso ya ja kujera ɗaya ta 6angaren da ke kallonta tare da ɗaura wayoyin da ya riƙo guda biyu a saman table din tsakankanin kujerun da suke zaune, zama ya yi ya jingina bayansa da kujeran, a hankali ta ɗago suka haɗa idanu ta ɗan yi murmushi, calmly ya ce, "How is school?" A nutse ta amsa mashi da Alhamdulillah kafin ta ce masa, "Ina wuni." Kai kawai ya ɗaga mata, shiru ta biyo baya Salma ta sauke idanunta ƙasa don bata iya jure kallon shi cikin ido, "Ya kuka?" Kaman daga sama ta ji ya yi maganar, da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi ta ga idanunsa na akanta da ɗan murmushi akan face ɗinsa, kunya ce ta kama ta ta ɗaga hannunta guda da har lokacin akwai zanen lalle ta ɗan rufe fuskarta, bayan ta cire tana ɗan murmushi ta ce, "Ai na bari." Shiru bai ce komai ba yana dai ta kallonta kawai, ɗayan hannunta da tun bayan da ta baro gida yake a cikin gyale ta fiddo, abun da ta riƙo ta miƙa masa ya kai idanunsa kan hannun nata, ta ce, "Ga shi, jiya na jira in baka sai baka fito ba, amman na wanke shi saboda na bata shi da ƙwalla." Ɗago idonsa ya yi ya kalle ta, kaman ba zai ce komai ba bayan ɗan lokaci ya ce, "Keep it, ki ci gaba da using da shi don na ga kaman kuka bai yi maki wuya." Ɗan waro ido ta yi da sauri ta ce, "A'a, kawai jiya na shiga damuwa ne sosai shi ya sa." Still da ɗan murmushi akan face ɗinsa bai dai ce komai ba, sai da ta ƙara ce masa gashi sannan ya ce ta ɗauka ya bata, sauke idonta ta yi a hankali ta ce ta gode, wayarsa ce ɗaya ta fara ringing, bayan ya ga mai kiran ya kai hannu ya ɗauka tare da kai ta kunne, ɗan saurarawa ya yi kafin ya furta, "Yea...we're together." Daga haka ya cire wayan, gyara zaman shi ya yi a nutse ya ce mata ta ji yana nemanta ko? Ta ɗaga masa kai alamar eh, a nutse ya soma yi mata bayanin dalilin kiran nata kamar yadda ya yi ma hajiya, ta natsu tana ta kallon shi sai ka ce yana biya mata karatu, ɗan murmushi ne akan fuskarta bayan ya gama magana ta ce shike nan zata sanar ma innarsu ɗin idan ta koma, yana kallonta ya tambayi ita nata aikin da yake son bata tana ganin ba zai affecting karatunta ba? Ɗan girgiza masa kai ta yi ta ce, "A'a, ai ba wani aiki bane mai ɗaukan lokaci sosai, zan iya." Kai ya jinjina kafin ya ce idan ta koma gida ta yi ma mom ɗin nata magana a bincika idan da waɗanda za su yi sai ta sanar masa don bai da lokaci sosai, Salma ta ce to, "Do you have a phone?" Ta ji ya tambaye ta, ɗan girgiza masa kai ta yi alamar a'a, ya ce, "Why? Ko baki so?" Tana murmushi ta ce, "Ina so, kawai dai ban isa riƙewa ba sai na gama makaranta." Shiru ya yi yana kallonta a ransa ya ɗan ji mamakin maganar tata, tambayarta ya yi ajin ta nawa ta bashi amsa da biyar, ya tambayi tama kusa gama school din ke nan, ta ce eh next year, ya gane sa'ar ƙanwarsa ce Leemarh saidai ita yana tunanin tun da ma ta fara secondary school take da waya, ya ce, "But at your age kin isa riƙe phone, kuma zai taimaka maki wurin karatun ki." Ɗan kikkafta ido ta shiga yi tana murmushi ba tare da ta ce komai, ya tambaye ta ko gida ne aka hana ta amfani da shi, ta ɗan girgiza kai ta ce, "A'a, ni ce na fi son sai na gama school, saboda ban son ta rinƙa ɗauke mani hankali ta hana ni karatu." Nodding kansa ya yi alamar ya fahimta, sai kuma ya ce mata amman ita ce zata tsara yadda ba zai rinƙa ɗauke mata hankalin ba, shiru ta yi bata ce komai ba, "Yanzu ba wani phone da zamu iya communicating kan maganan da muka yi?" Da sauri ta ce masa a'a akwai ta innarsu da take yawan amfani da, shiru ya ɗan yi kafin ya ce ban da shi ba wani? Ta ce akwai ta yayanta Sagir, ɗan maimaita sunan ya yi irin alamar kamar ya san mai sunan, tambayarta ya yi ta riƙe lamba ɗin shi ta ce eh, ya kai hannu ya ɗauki ɗayar wayarsa kafin ya miƙo mata ya ce ta saka lamba din Sagir, bayan ta saka ta bashi ya amsa ya yi saving, kiran shi aka yi waya ya ɗauka yana amsa kiran da turanci, ita dai Salma ta zuba masa ido don ya ɗan juyar da fuskar tasa, har yanzu tana jin mamakin wai shi ɗin bahaushe ne, yana cikin yin wayar ya ɗan janye ta daga kunnansa, ya kai ɗayan hannunsa kan ɗayar wayar wadda tun da ya ajiye ta bai ta6a ta ba, iya jikin wayar ma abun kallo ne glass din ta sai sheƙi yake, ba tare da ya ɗauki wayar ba ya ɗan buɗa tafin hannunsa a saman ta sai gashi ta kawo haske alamar ta buɗe kanta, mamaki ne ya kama Salma ganin yadda ya buɗe wayar wanda ita tun da take bata ta6a ganin an buɗe waya haka ba, ɗan daddana wayar ya yi na ɗan lokaci da alama abu yake dubawa, maida wayar da yake amsa kiran yayi kunne ya ci gaba da yin wayar da yake yi, idon Salma na akan wayar da ya gama ta6awa bayan ɗan lokaci ta yi duhu alamar ta rufe kanta, tana ta kallon wayar can ta ɗaga ido ta kallo Deen ta ga idanunsa na a gefe yana ci gaba da yin waya, a hankali ta kai hannunta itama ta buɗe tafin hannunta a ɗan saman wayan yadda ta ga ya yi, ganin bata kawo haske ba ya sa ta yi tunanin ko hannun nata ya yi nesa da screen ɗin wayar, hakan yasa ta ɗan ƙara matsawa da tafin hannun, ta shagala tana ta ƙoƙarin buɗe wayar kamar daga sama ta ji muryarsa ya ce, "It only unlocks with my Palm ID." A ɗan firgice ta ɗaga ido ta kalle shi suka haɗa idanu, kunya ce ta kama ta ta yi saurin janye hannunta tare da sauke idanunta ƙasa, tafin hannun nashi ta ga ya kai saman wayar ta buɗe, turo mata ita ya yi ta ɗaga ido ta kalle shi, ya ce mata gashi ya buɗe, da sauri ta ce a'a ba wani abu zata yi da ita ba kawai dama haka nan ta yi yadda ta ga ya yi, murmushi kawai ya yi bai ce komai ba ya ɗauke idanunsa yana latsa wayar dake a hannunsa, tana ta kallon screen ɗin wayar da ke ɗauke da hotonsa da kayan ƙwallo ya sa ƙafarsa zai buga ball ɗin, daga gani suna cikin yin wasa ne aka yi hoton, sosai hoton ya yi mata kyau, ɗagowa ta yi da niyyar yi masa magana amman ta kasa, kamar ya ji tana kallonsa ya janye idonsa daga kan wayar hannunsa ya kalle ta, daga yanayin ta ya fahimci da magana a bakinta, ɗage mata gira ya yi ba tare da ya ce komai ba, cikin kama kai ta ce, "Dama cewa zan yi zan iya kallon hotuna?" Yadda ta yi maganar ya so bashi dariya amman bai yi ba, kai ya ɗaga mata alamar eh, sai dai lokacin da ta kalli wayar har ta rufe kanta, hannu ta ga ya kawo ya buɗe ya ɗauka ya ɗan daddana kafin ya miƙo mata, tana amsa ta ga ya buɗe mata daidai gallery ɗin wayan, folder daban-daban ta gani ta shiga ta farko wadda ke ɗauke da sunan 'My Fam' tana shiga hoton farko da ta fara cin karo da na wata mata ne wadda sai da Salma ta ɗan tsorata da ganinta saboda tsantsar kyawunta, yanayin yadda ta yi kallo a jikin hoton ya bayyana kaifin idanuwanta, sai dai kana kallon fuskarta zaka shaida kammaninta sosai da Deen, bin hoton Salma ta yi da kallo na ɗan lokaci kafin ta ɗago a hankali ta kalli Deen, ta ce, "Is she ur mom?" Ɗago idonsa ya yi ta juya mashi hoton, ɗan murmushi ta ga ya yi ya ɗaga mata kai alamar eh, Salma ta ce, "Kun yi kama sosai." Calmly ya ce mata thank u, hoto na biyu tana buɗe shi ta gane mahaifinsa ne don ta san shi ɗan majalissar garin su ne, hoto na gaba ta buɗe wanda gaba ɗaya ƴan gidansu ne har da mom da dad din su hakan ya sa ta gane, hoton Leemarh ta buɗe wanda take ita kaɗai, bin hoton ta yi da kallo don ta yi mata kyau sosai kuma kana ganinta zaka ga kammanin Deen a tattare da ita, juya wayar ta yi ta ce mashi, "Ur sis right?" Kallon hoton ya yi ya ɗaga mata kai, ta ji ya ce, "Leemarh...she's ur age mate." Shiru ta yi tana kallonsa a ranta ta ɗan ji mamakin yadda ya ce su sa'anni ne." Daga yanayin fuskarta ya gane ta yi mamakin maganarsa, ya ce mata itama next year take gama sec school ɗinta, sai da ta ji haka ta gane ta ɗaga masa kai, kan hoton wani babban mutum ta zo ya yi shigar baƙaƙen suit yana zaune a cikin wani haɗaɗɗan office, mutumin yana da matuƙar ƙwarjini da haiba, sam jikinsa bai nuna yawan shekarunsa ba, daga gashin
Chapter 78 · 0% Book details