Sashe 10
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bakin gado ta nufa ta zauna dabas fuskarta a jagule kamar zata sa kuka, sam bata ji komai ba da mom ta kira Fahad da ɗan shaye-shaye, ba tun yau ba tana jin hakan saidai ita bata ta6a ganinsa ba yana shan wani abu da ya danganci haka, takaicinta ita ba ma soyayyar suke da shi ba, kawai dai tana jin wani abu a ranta game da shi wanda ta san son shi take amman shi bai ma san halin da take ciki ba. Gaba ɗaya mom ta lalata yanayin farin cikin da take aciki, ji take kamar ma ta cire kayan ta fasa fita, sai dai son ta yi hakan ya rinjaya a cikin zuciyarta. Ta ɗan ɗauki lokaci zaune tana ta ƙunci kafin daga bisani ta miƙe ta koma gaban madubin ta ɗan ƙara gyara fuskarta bayan ta gama ta ciro takalma flat kalar peach ta zura kafafunta ta nufi hanyar fita.
Kiran dad da ya shigo wayar Deen ya sanar da su cewa lokacin sallar la'asar ya yi su fito su tafi masallaci ya tashe su daga hirar da suke yi. Bayan sun dawo suna shigowa falo Deen ya ce ma Fahad su je dining room ya ci abinci, suna zuwa tsakiyar falon Leemah dake zaune tana jiran dawowar su ta nufo su, ganinta ya sa su tsayawa ta ƙaraso gaban su da ɗan murmushi ta yi masu sannu da dawowa, fuskar kowannan su da murmushi suka amsa mata.
"Leemah, an zama Æ´an mata." Deen ya faÉ—a da murmushi, hannuwanta ta sa ta rufe fuska alamar kunya, buÉ—e fuskar ta yi suka haÉ—a ido da Fahad dake É—an yin murmushi,
"Ya Fahad mu je ka ci abinci gashi can na kai maka dining, tun da ka zo baka ci komai ba." Ta faÉ—a tana É—an rausayar da kai.
"Good, dat's why i love u Leemah, kina da hankali da sanin yakamata." Deen ya faÉ—a,
"Amman É—azun dad cewa ya yi wai wani lokacin nike da hankalin." Ta tura baki, da alama bata ji daÉ—in maganar ba, kuma ba don komai ba sai don an faÉ—i hakan a gaban Fahad, satar kallon shi ta yi suka haÉ—a ido.
"Suna maki wasa ne ai."
Fahad ne ya faÉ—a idonsa a kanta, É—an murmushi ta yi ko ba komai ta ji daÉ—i da ya É—auka wasa suke, Deen dake ta kallon su yana É—an murmushi don ya so ya fahimci wani abu, ya ce ma Fahad su je Leemah ta yi serving na shi zai je part É—insa ya É—auko wayansa ya san yana
da tarin saƙonni, kuma yana son yin magana da manager ɗinsa, nufar dining room suka yi suna tafiya a jere shi da ita yayin da Deen ya nufi upstairs jikinsa sanye da farar jallabiyar da ya saka da za su je masallaci ya yi kaman balarabe...
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
_Bossladieswriters_
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 4
Bayan sun isa dining room, a ɗaya daga cikin kujerun ya zauna Leemah ta shiga yin serving na shi, bayan ta gama ta zagayo kujerar dake fuskantar tashi ta zauna, a nutse ya fara cin abincin yayin da take ɗan satar kallon sa, ita dai bata san ya akai ba komai nashi burgeta yake ba tun yanzu ba, ba kamar kwantaccen sajen shi da irin gyaran da ake mashi burgeta yake sosai, tana cikin kallon nashi maganganun da suka yi da mom ɗinta suka shiga dawo mata, jikinta ne ya yi sanyi tasan halin mom ɗinsu, idan har ta nuna bata son abu to fa ba a isa ba a yi, tasan tun da ta nuna bata son alaƙar soyayya a tsakanin su to kuwa mawuyacin abu ne in ma sun fara yi ta bari su auri juna. Ta yi nisa a duniyar tunani ya ɗago ya kalle ta, daga yanayin fuskarta ya fahimci kamar wani abu na damunta, ɗan gyaran murya ya yi shiru bata dawo hayyacinta ba,
"Leemahh..." Ya kira ta da wani irin sauti, É—an firgit ta yi ta kalle shi,
"What's wrong with you?" Ya tambaya bayan ya ajiye cokalin hannunsa, É—an kikkafta idanu ta shiga yi bata san mi zata ce mashi
ba,
"Tell me, mi ya faru?" Cike da nuna kulawa ya tambaya, sauke idonta ta yi tana ci gaba da kikkafta idanu, ɗagowa ta yi ta kalle shi ya kafe ta da nasa idanun alamar amsarta yake jira, motsa baki ta fara, slowly ta furta, "Mom ce..." Ta faɗa kaman zata yi kuka, shiru ya yi yana ci gaba da kallon ta, bai ji yana son ya tambaye ta abun da ya faru ba saboda ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, da wuya abun da ya haɗa ta da ita in ba akan shi bane.
"Ki yi hakuri, they're our parents komai suka yi mana sai dai mu yi haƙuri, and sometimes suna yi mana abu ne for our own good." Shiru ta yi fuskarta a ɗan ɗaure, ɗage mata gira ya yi alamar ta ji, a hankali ta jinjina masa kai, murmushi ya yi tare da ɗaukar cokalin ya ci gaba da cin abincin, after a while ya ƙara dakatawa tare da kallon ta ya ce mata ta zuba abincin itama,
"Na ƙoshi, bamu daɗe da muka ci ba ka zo." Ta faɗa da murmushi,
"Shine ni kika tsare ni don ki ga yadda nike yin loma ki yi mani sharri?" Dariya ta yi har fararen haƙoranta suka bayyana,
"Ai nasan baka yin loma Ya Fahad." Ɗan murmushin gefe ya yi kafin ya ci gaba da cin abincin, ganin ya tsaya yana ƙoƙarin zuba lemu ta miƙe da sauri ta zuba mashi, miƙa masa ta yi ya kar6a tare da yi mata godiya, bayan ya sha ya ajiye glass cup ɗin, kallon ta ya yi suka haɗa ido ya ce, "Ya school, an kusa gamawa ko?" Kai ta jinjina tare da faɗi mashi lokacin da ya rage,
"Da an gama sai a ci gaba ko, mi kike son karanta ne?" Tsintar kanta ta yi da kasa bashi amsa ta bishi da ido tana kikkafta su, shiru ya yi yana nazarin ta, can ya É—an yi murmushi slowly ya furta, "Ko aure zaki yi?" Har saida gabanta ya faÉ—i jin abun da ya faÉ—a, nan ma kasa bashi amsa ta yi, ganin kallon da yake mata ya sa ta sunnar da kanta tana É—an motsa baki,
"Leemah..." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, "Speak your mind, ai ba laifi bane in shi kike son yi abu ne mai kyau." Motsa baki ta yi da ƙyar ta ce, "Duk abun da Allah Ya za6a mani."
"Amman kin fi son ki yi aure?" Abu ta haÉ—iya kafin ta ce, "Ni da ko saurayi bani da Ya Fahad." Ya yi É—an murmushi,
"In kin yi saurayin za ki yi auren ke nan?" Shiru ta É—an yi tana kallon sa tana É—an murmushi yayin da zuciyarta ke ta tunzura ta kan ta fallasa mashi sirrinta, kai ta jinjina, ta ce, "In muna son juna." Dariya ya yi duk dimples É—in sa suka lotsa,
"Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya baki saurayi na gari wanda zai so ki saboda Allah ya kula mana da ke sosai." A hankali ta amsa da Amin tare da sauke idanunta, ji take kamar ta faɗa mashi cewa tana son shi saidai tana jin fargabar hakan ba kamar da yake matsayin yayanta kada ya ƙi amincewa ya kuma tsawatar mata kan hakan, a nutse ya ci gaba da cin abincinsa tana ta ɗagowa tana satar kallon shi,
"Amman na yi mamakin jin baki da saurayi, yadda sister nawa take tubarkalla, ko dai ke ce baki amincewa in an ce ana son ki....? Ko da yake kamata ya yi dama yanzu ki focus kan karatun ki ba wannan ba, gashi kuma kin ce aure kike so to kuma ba boyfriend, ya za a yi ke nan?" Ya ƙare yana sakin murmushi, tura mashi baki ta yi a shagwa6e ta ce, "Ni fa Ya Fahad ba cewa na yi banson karatu ba ko, ba kai ne ka matsa in faɗi maka ba har ka ce abu mai kyau ne, ni shiyasa na ce ina so kuma na ga ko an yi aure ana iya yin karatu."
"To yanzu ya zamu samo boyfriend en?" Ya faɗa yana ɗan shafa gemun shi da hannunsa na hagu, wani kallo ta yi masa ta ce, "Ai ina da wanda suke cewa suna so na, wasu yaran friends ɗin mom ne wasu kuma na dad, amman ni duk bani son su, akwai wanda nike so amman shi bai sani ba..." Ta ƙare maganar ƙirjinta na ɗan bugawa,
"You should tell him.." Ya faɗa tare da ɗan ƙanƙance ido ya shigar da lip ɗin sa na ƙasa,
"I'm scared he might reject me...ban so na zubar da ƙima ta." Da ƙyar ta faɗa tana ta ƴan kame-kame, ƙayataccen murmushi ya saki ya bita da wani irin kallo da yasa duk ta sha jinin jikinta, lokaci guda ta ji kallon na neman haifar mata da kasala, ta kasa tsaida idanunta akan shi sai ƴan kifce-kifce take tare da kallon ƙasa,
"Bana tunanin akwai namijin da zaki furta ma hakan ya ƙi amincewa, with your beauty inside and out, I'm sure he will adore you. Kawai yanzu kamata ya yi ki maida hankali kan karatu, forget about any relationship for now, lokacin hakan zai zo, and you will meet the right person to marry " Ɗan jinjina mashi kai ta yi kafin ta sunnar da kanta ƙasa, hannu ya kai ya ɗauki glass ɗin lemu ya kai baki, a hankali yake kur6ar ruwan lemun idanun shi akan Leemah kamar mai nazarin wani abu.