← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 197

Sashe 167

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Washe gari suna yin breakfast, aunty na lura da yadda duk Salma ta yi sukuku, ta ƙi sakin jiki ta ci abinci sosai, "Baby..." A hankali Salma ta ɗago idanunta ta kalli aunty jin ta kira sunanta, "Ya aka yi ne na gan ki duk wani iri, wani abu na damun ki ne?" Da sauri Salma ta ɗan girgiza mata kai a hankali ta ce a'a ba komai, shiru aunty ta ɗan yi tana kallonta kafin ta ce, "Baby yaushe kika fara 6oye mani damuwar ki? idan baki fada mani damuwar ki ba wa zaki faɗa mawa ehm?" Salma ta sauke idanunta tare da yin shiru, hakan ya sa aunty gane akwai abun da yake damunta, cikin kwantar da kurya ta ce, "Tell me baby minene?" Ɗago ido ta yi ta kalli aunty a sanyaye ta ce, "Ba wani abu bane aunty...dama yaya Deen ne na ga har ya tafi..." Shiru ta yi a ranta tana ganin miye amfanin faɗin hakan ma,
"Can ƙasar da yake ya koma?" aunty ta tambaya, Salma ta ce, "Ban sani ba, na dai ga ya je France." shiru aunty ta yi tana kallon Salma da ta sauke idanunta, ta fahimci ta kamu da son Deen sosai, sai dai bata ga laifinta ba don bata tunanin akwai macen da zata ce bata son Deen balle kuma a ce shine ya furta mata so, ko rannan sai da ta tambayi Salma ko sun yi magana da shi ganin ya zo ƙasar Salma ta ce mata basu yi ba,
"Har yanzu baku ƙara magana da shi ba?" aunty ta tambaya, ɗaga mata kai ta yi ba tare da ta ɗago ba, "Ke baki yi mashi magana bane?" Salma ta ɗan ɗago ta ce mata ta tura masa saƙo har sau biyu amman bai reply ba har yanzu, ɗan shiru aunty ta yi kamar mai nazarin abu, can ta ce, "Ina tunanin uzururrukan gasar da suka yi ne suka yi mashi yawa, na san ƙilan ya bari ne sai ya natsu sosai zai waiwaye ki, ki daina damuwa kin ji." Salma ta ɗan yi murmushi mai kaman na yaƙe ta yi saurin cewa, "Aunty nifa ba damuwa na yi ba..." aunty ta yi ɗan murmushi kawai ta ce mata ta ci abinci.....

09013804524, 08169856268 for more info.

*✨A CIKIN RAYUWA

ZAINAB BATURE

54
Chapter 167 · 0% Book details