Sashe 177
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
....Gaba ɗaya sauran yinin ranar Salma a cikin tsananin farin ciki ta kasance, ba kamar idan ta kalli kayan da Deen ya kawo mata da aunty ta sa suka kawo su nan ɗakinta, bata gajiya da tunanin Deen da abun da ya wakana a tsakanin su, kana kallonta zaka fahimci tana a cikin farin ciki. A daren ranar, bayan Salma ta gama shirin kwanciya sai ga kiran Deen ya shigo wayarta, dama ɗazun ta kira shi bayan ya tafi ta yi masa ya ya koma da godiyar kaya...soyayya suka sha sosai, har saida Salma ta yi mamakin yadda ya saki jiki, daga baya ya ce ta kwanta sai ya zo gobe, suka yi bankwana cike da nuna ƙaunar juna. Washe gari bayan sun tashi Salma ta yi duk ayyukan da ta saba yi duk da lokacin ma sai da aunty ta hana ta yin wasu abubuwan ba kamar wanda zata ta6a ruwa sosai, a cewar ta kada lallenta ya disashe tun da Deen ɗin ba tafiya ya yi ba gashi kuma za su fita tare...wuraren ƙarfe sha biyu ya kira ta ya sanar da ita bayan an gama sallan azahar zai zo ya ɗauke ta, suna gama yin wayar ta je ta sanar ma aunty ta ce ta je ta yi wanka, after some minutes ta fito tana tsaye a gaban mirror tana goge jikinta aunty ta shigo, cikin ɗakin ta nufa tana tambayarta ta fito wankan ta ce mata eh, ganin zata fara shafa mayukanta da ke a wurin aunty ta yi saurin cewa, "Ina waɗanda ya kawo maki?" Salma ta ce mata suna cikin akwatin, "To ai ba kawo maki yayi don ki ajiye ba ko, su yakamata ki yi amfani da su" Daga haka ta nufi inda akwatunan suke ta fara buɗewa, mayukan ta fiddo mata ta ce ta zo ta ɗauka, dama jiya duk sai da ta dudduba bayanan yadda ake amfani da komai, bayan ta zo ta kwashi mayukan ta koma gaban mirror ta fara shafawa, kana jin yanayin su ma a jiki ka san za su yi aikin su, har da na su tafin ƙafa da tafin hannu, wanda ake shafa ma gashi suma duk ta shafa, aunty ta nufo ta da wata Abaya da ta fiddo daga cikin kayan tana faɗin, "Wannan Abayan ta yi kyau over, ina ganin ki saka ta, shima idan ya ga kin saka cikin kayan zai ji daɗi." Salma ta jiyo tana kallon rigan, a gefen gado aunty ta ajiye ta ta nufo Salma, taimaka mata ta shiga yi ta gyara mata gashinta sannan ta yi mata light make up kaman jiya, bayan ta gama ta ce ma Salma ta saka underwear ta ce to tare da nufar wardrobe ɗin bango inda kayanta suke, aunty ta koma wurin akwatunan tana ce ma Salma ta zo su za6i jewellery da takalman da zata saka...aunty ta bi Salma da kallo tana ta sakin nurmushin jin daɗi bayan ta gama shirya ta, cike da sha'awa ta ce, "Ma sha Allah jiki ya ji naira, kin ga wani kalan kyau na musamman da kika yi baby, duk wanda ya gan ki sai ya yi tunanin ɗiyar wani babba ce a ƙasa, don da an ga kayan nan ansan ba ƙananun kaya bane." Ita dai Salma dariya kawai take tana ta kallon kanta a madubi, sosai ta yi wani irin kyau a cikin abayar wadda take ruwan madara, a jikinta wani irin design ɗin ado aka yi, sam kwalliyan rigar ba mai hayaniya bace amman tsarin kwalliyan da aka yi ya ƙawata rigan sosai, ga yadin ta shima na musamman, a jikin kwalliyan rigar akwai ratsin golden brown da wasu irin fararen stones masu sheƙi, takalman da ta saka kalan kwalliyan rigan ne da clutch bag mahaɗin takalman, aunty ta kai idonta kan takalman ta ce, "Baby anya kuwa zaki iya yin tafiya da takalman nan, na ga sun fi kalan wanda kika saba sakawa tsini." Salma dake ta faffaɗan murmushi ta ce zata iya ai suna da maɗauri, cike da shakku aunty ta ce, "Kada fa a je a yi abun kunya, kin san mutane irin shi public figure koda yaushe cikin ɗaura masu camera ake, bamu sani ba ko wani wurin mutane zaku je." Gaban Salma ya ɗan faɗi jin maganar aunty, ita sam tunanin ko wurin mutane za su je bai zo mata a rai ba, aunty tana ƴar dariya ta ce bari dai su ɗan yi little practice ɗin tafiyan saboda tsaro, daga farkon shigowa ɗakin zuwa ƙarshe ta saka Salma yin tafiya, tana yi tana gyara mata inda ke buƙatar gyara, sai da aunty ta ga tana yin tafiyan lafiya lau yadda ta nuna mata, sannan suka koma gaban mirror tana ƙara gyara ta kuma tana koya mata yadda zatai behave har da magana idan buƙatan hakan ta taso, suna haka suka jiyo ƙarar buɗe gate, aunty ta ce tana jin shine ya zo, tana rufe baki wayar Salma ta fara yin ringing ta nufi gado zata duba aunty ta bita da kallo cike da sha'awa tana sakin murmushin jin dadin ganin yadda babynta ta fito, bayan ta duba ta ga shine, cikin kwantar da murya suka yi magana ya ce mata ya zo, bayan ta gama ta ɗago tana murmushi ta ce ma aunty, "Shine ya zo." aunty ta nufo ta ta ce ta saka wayan a jakar da zata tafi da ita, tare suka nufi ƙofa da aunty ta kama mata hannu suka fita, har bakin falo aunty ta kai ta sannan ta saki hannunta tana kallon ta da murmushi ta ce, "Sai kun dawo babynah, ki kula pls." Salma ta ɗaga mata kai, sai kuma ta ce, "Ki raka ni ko bakin haraban." Aunty ta yi mata wani kallon hararan wasa, kafin ta ɗan yi murmushi ta ce, "Go on, don't keep him waiting..." Salma ta ɗaga hannunta da ya sha abun hannu mai matuƙar kyaun gaske ta yi mata bye bye itama aunty ta mayar mata daga haka ta tafi...a nutse ta nufo harabar tana tafiya, Salma ta bi danƙareriyar baƙar mercedes benz G- Class (G-Wagon) dake ta sheƙi da aka faka a gaban gate da kallo, sauke idonta ta yi tunowa da huɗubar da aunty ta yi mata na kada ta nuna ƙauyanci koda ta ga abun da ya ɗauki hankalinta, ta basar ko kuma ta yi al'ajabin a zuciya, a cikin rai take tunanin yadda aka yi yau ya canzo mota ganin ba da wannan ya zo jiya ba ko kuwa duka ya zo da su daga Abuja...tun da ta nufo motar idanun Deen na akan ta, da yake parker motan aka yi tana kallon ginin gidan ba tare da an rufe gate ɗin ba, tana kusa zuwa wurin motan mutumin da ke a gaban motan wanda da gani bodyguard ɗin jiya ne don irin shigar jiyan ce a jikinsa ya fito ya buɗe mata ƙofar baya tun kafin ta ƙaraso, kai ya ɗan sunkuya mata alamar gaisuwa itama ta yi masa haka, bayan ta shiga ya maida ƙofar ya rufe, har Salma bata san lokacin da ta ɗan lumshe ido ba lokacin da ta shiga cikin motan, haɗa ido suka da Deen da ke ɗaya 6angaren back seat ɗin, ya yi shigar fararen ƙananun kaya designers, farin jeans da riga fara mai ɗan ratsin baƙi sai farar hula face cap, a ƙafafunsa ya saka baƙaƙen takalma, haka hannunsa na ɗaure da wata rantsattsar baƙar agogo ta miliyoyin kuɗi, sai faman sakin ƙamshi mai narkar da zuciya yake, idan ka gan shi sam bazaka ta6a tunanin ya haɗa iri da hausawa ba ba kamar yadda sumar shi ta zuba a wuyansa, haɗa ido suka yi Salma ta sakar masa lallausan murmushi, softly ta ce, "Welcome...ina yini." Ya ɗan nod kan sa fuskarsa da murmushi, kasa jure kallon shi ta yi saboda kunyar hirar da suka yi da shi a daren jiya, don a hiran har da irin rayuwan da za su yi idan suka yi aure ya faɗi mata, itama ta tambaye shi abubuwan da yake son matarsa ta rinƙa yi mashi kamar shigar kaya da sauran su, ƙasa da murya ta ji ya ce, "Kin yi kyau sosai princess." A hankali ta ɗaga kai ta kalle shi ta ga ita yake kallo, a hankali itama ta ce, "Ai kai ne ka sa na yi kyau ɗin." Ya ɗan lumshe ido bai ce komai ba, mutumin na mazaunin driver ne ya tambayi za su iya tafiya Deen ya amsa mashi, bayan motan ta fita daga cikin gidan, ɗayan bodyguard ɗin da bai shigo cikin motan ba ya rufe gate din sannan ya koma ciki daga haka suka tafi....tun da suka hau hanya ba wanda ya ƙara cewa komai, idon Salma na akan hanya shi kuma Deen yana ta6a waya, bayan wani ɗan lokaci ta juya ta kalle shi, slowly ya dago kai shima ya kalle ta tare da yi mata murmushi, a hankali ta ce, "Kai ma ka yi kyau sosai.." Ya ɗan ɗage gira ya ce shima ita ce ta sa shi ya yi kyaun, Salma ta yi ɗan faffaɗan murmushi, tambayarta aunty ya yi ta ce mashi tana lafiya ta ce ma ta gaishe shi ya ɗaga kai, jefi jefi suka ci gaba da yin magana....bayan tafiyan mintuna masu ɗan tsayi suka iso wani wuri, duk yadda Salma ta so ta kasa ɗauke idanunta daga kallon ginin, duk da bata yi yadda zai yi ƙauyanci ba, tun daga tsarin ginin wurin da gate ɗin shiga masu matuƙar ɗaukar hankali ne, bayan sun shiga nan Salma ta ga ashe bata ga komai ba a wajen ginin, yadda ka san ginin ba a Nigeria ba yadda ya tsaru ga tafka tafkan gilasai ta ko ina a ginin benen, daga rubutun da ta gani a gaban ginin ta gane Restaurant ne, kuma kusan shine babban restaurant na garin, babban wurin parking ɗin motoci da ke can gefe na ɗauke da motoci masu numfashi, kai daga ganin wurin ka san ba wurin zuwan ƙananun mutane bane, ba su nufi parking space din ba ta gefen ginin suka bi, a daidai gaban wata babbar kofar glass da itama ta haɗu suka tsaya, bodyguard ɗin da ke a gaba ne ya ɗaga waya tare da yin