← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 197

Sashe 11

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Deen ya dauko wayarsa, babban falon ya dawo ya zauna a ɗaya daga cikin saitin kujerun ciki, bayan ya shiga shafukan shi na sada zumunta waɗanda yake da mabiya miliyan ɗaruruwa, tarin sharhin masoyansa ya taras, a nutse yake bi yana dubawa, yawanci fatan alkhairi ne suke mashi kan ziyarar da ya kai ƙasarsa, da masu gwarzanta shi da nuna yadda suke ƙaunar shi, akwai tarin saƙonni daga wasu ƙananu da manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Nigeria suna roƙon shi da ya kai masu ziyara su yi wasa tare da shi, wasu kuma roƙon shi suke kan ya basu dama don su haɗu da shi. Yayin da yake ci gaba da bin saƙonnin, ɗan murmushi ne akan fuskarsa, wasu yana basu amsa wasu kuma ya yi liking dama shi ba mutum bane mai shariya ga masoyan sa, da wuya ya share in an turo mashi saƙo mai muhimmanci, yana matuƙar ƙoƙari wurin ganin ya samu lokaci ya bada amsa ga saƙonnin da suka dace. Duk da wasu abubuwan da yawa da suka shafi social media accounts dinsa personal manager din sa ne ke kula da su.

KATSINA STATE

Funtua L.G.A

Madaidaicin gida ne irin wanda kana gani zaka fahimci mamallakan shi masu ƙaramin ƙarfi ne, akwai ɗakuna guda biyu masu baranda a gaban su daga 6angaren hagu, daga 6angaren dama akwai ɗaki ɗaya ware yana kallon barandar wanccan ɗakunan, idan ka shigo gidan daga ƙofar waje akwai rufaffan zaure daga ciki akwai ƙofa da taga irin ɗakin zaure, kana shigowa cikin gidan daga bangaren hagu gefen baranda anan wani ɗan ɗaki ne mara girma yana da buɗaɗɗun ƙofa da taga daga yanayin shi zaka fahimci kitchen ne, daga bangaren gefen ɗakin da ba a cikin baranda yake ba ɗan fili ne, akwai rijiya a wurin da wurin yin wanke-wanke sai wani zagayayyen ɗaki mara rufi akwai kofa a jiki da gani banɗaki ne. Gaba ɗaya tsakar gidan malale yake da siminta sannan ginin gidan bai ji jiki ba sosai.

Daga can gefen rijiya wata matashiyar budurwa ce zaune akan kujera ƴar tsugunno, daga gabanta roba ce mai ɗan faɗi tana yin wanki ta gicce, ta yadda robar ba a tsakiyar kafafunta take ba a gefenta take, a jikinta tana sanye da doguwar rigar atamfa yayin da kanta ke sanye da hula daga tsakiyar kanta ya yi tudu sosai alamun tana da gashi ko kuma ƙaton ribbom ne ta saka, saidai kana kallon gaban kanta da suma ta kwanta zaka fahimci tana da gashin, yanayin kalar fatarta warm caramel ce, irin kaman wankan tarwada amman wadda ta fita daban da ake kira fata mai tsada don ba kasafai aka fiye samun masu ita ba musamman mu a nan, yadda ta juyar da fuska ta ɗan sadda kanta ya bayyanar da hancinta wanda ke da tsawo sosai tamkar an tsaga kara.

Daga can gabanta saman tudunkar baranda wani matashin saurayi ne da a shekaru zai iya kai wa shekara ashirin da ukku zuwa da huɗu, duk da girman namiji in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun ma, jikin shi na sanye da riga mara hannu irin ta shan iska da wando tiri kwata, daga gaban shi tsakankanin ƙafafuwansa plate ɗin abinci ne dauƙe da shinkafa da wake da mai da ya ji har da salat, hannun shi na dama na ruƙe da cokali da yake cin abincin da shi yayin da hannun hagun shi ke ruƙe da waya android yana ɗan latsa ta, yana yi yana kai idonsa akan abincin in zai ɗebo ya kai baki,

Wani matashin saurayin ne ya shigo cikin gidan yana sanye da singileti da gajeran wando, da alama daga cikin ɗakin zaure yake, a shekaru zai kai shekara ashirin zuwa da ɗaya, wurin inda matashiyar budurwar take ya nufa hannunshi ruƙe da wasu kaya, daga gabanta ya tsaya tare da sakin kayan ƙasa ya ce,

"Salma ɗan wanke mani su yanzu ki shanya mani su bushe, muna da match anjima su zan sanya." A hankali ta ɗago da fuskarta ta jefa mashi wani kallo mai kama da harara, ma sha Allah! ganin irin kyawun fuskarta, baya ga dogon hancinta tana da madaidaitan idanuwa farare tass da su, idan ka ƙura mata idanu zaka fahimci ƙwayar idanun nata baƙin su bai ciza ba sosai ta yi ɗan kalan ruwan ƙasa, haka ma labbanta kalar su brown ne da ya ɗan ciza, da kallo ɗaya zaka fahimci kyawunta, kana ci gaba da kallonta za kai ta ƙara ganin ƙaruwar kyawun nata.

"Ni fa gaskiya Sageer na gaji, duka yaushe na dawo daga makaranta, ba don uniform ɗin nawa sun yi datti ba da bama zan yi wankin ba hutawa zan yi, gashi ka kawo mani kayan ƙwallo masu dauɗar tsiya, safar ma sai wari take yi wllh." Ta ƙarasa tana kallon kayan tare da tura baki, harara ya jefa mata ya ce, "Dole ki wanke su!" Yana faɗin haka ya juya zai bar wurin, bin shi ta yi da harara, tunanin abun da zata yi ta fanshe fushinta ne ya zo mata a rai, wata ƴar dariyar gefe ta yi ta buɗe baki ta fara yin waƙa, "Delu ƙanwar maza, ta fi mazan wayau...." Idanunta akan saurayin dake zaune yana cin abinci wanda sam bai kalle ta ba kamar ma bai ji mi take cewa ba, kallon Sageer dake nufar zaure ta yi shima bai bi ta kanta ba, ganin haƙarta bata cimma ruwa ba ya sa ta ƙara ɗaga muryarta mai daɗin sauraro ta ƙara yin waƙar,

"_....Ni Delu ƙanwar maza, duk na fi mazan wayou...._" Tana rufe baki matashin dake zaune yana cin abinci ya kai hannunshi ɗaya ya ciro ƙaton takalmin robar dake ƙafarsa, ɗagowa ya yi tare da saita ta ya jefo mata shi, da sauri ta goce tana dariya, shi kuwa Sageer maimakon ya fice sai ya nufi ƙofar kicin dake gefe, fitowa ya yi hannunsa ruƙe da muciya ya nufo ta yana faɗin, "Yau zaki gaya mani ubanwa kika fi wayou..." Tana ganin abun da ya ɗauko ta yi zumbur ta miƙe, miƙewar da ta yi ainihin suffar jikinta ta bayyana, sam ba gajera bace za a iya kiranta da doguwa, jikinta dum-dum bata da sirantaka sosai, daga wurin ƙugunta ya ɗan buɗe alamar tana da hips ba laifi, hakan ya sa straight gown ɗin jikinta ta fitar da shape ɗin ta gwanin burgewa, nufar wurin ƙofar banɗaki dake wurin ta yi cikin ɗaga murya ta shiga faɗin,

"Wayyo Innarmu! Ga yaya Auwalu da Sageer nan zasu kashe maki ni...." Bada jimawa ba ƙofar ta fara yin ƙara alamar za a buɗe, wata mata ce ta fito daga ciki, a yanayin shekaru zata iya kai shekaru arba'in zuwa da ɗaya, sam jikinta bai nuna manyantaka ba, ta fuska ne zaka ɗan iya fahimtar hakan, tana da tsawo sannan bata da jiki, yanayin fatar ta za a iya kiranta da wankan tarwaɗa, jelar kitson dake a kanta ta sauka a tsakankanin kafaɗunta alamar tana da gashi ba laifi, akwai ɗan yanayinta a tattare da yaran dake wurin duk da tafi mazan haske don su baƙaƙe ne ba kamar Auwalun, shi Sageer ɗin ya ɗan daukko haskenta amman ita kuma Salmar tafi ma uwar haske koma in ce sam kalar fatar su ba ɗaya bane.

Bayan mahaifiyar tasu ta je ta 6oye tana leƙen Sagir da ya tsaya hannunsa ruƙe da muciya ya ɗaure fuska,

"Mi ya haÉ—a ku da ita?" Innar ta tambaya da É—an murmushi akan fuskarta,

"Innarmu ba kina jin ta ba, mu sa'aninta ne da zata rinƙa yi ma wannan waƙar!" Ya faɗa cikin fushi,

"To ai da wasa take yin waƙar..." Katse Innar ya yi, "Wllh ba wani wasa, kuma mu ai ba tsaran wasanta bane, kawai don kina goya mata baya ne ya sa duk ta bi ta raina mu, ko Auwalu bata ƙyale ba balle ni, in kuma za a ɗauki mataki a kanta ki hana shiyasa ai take ci gaba da yi ma mutane iskanci." Ya ƙare yana ta hura hanci, daga bayan innar tasu ta leƙo da kyakkyawar fuskarta tana ƴar dariya ta ce, "In haka ne kaima ai ka raina yaya Auwalu ba gashi nan ko yaya baka iya ce mashi..." Bata ƙare maganar ba ganin ya yo kukan kura yana ƙoƙarin kwaɗa mata muciyar, ihu ta saka tare da ƙara ƙanƙame innar tasu kamar zata kayar da ita ƙasa ta shiga fadin, "Wallahi idan ka doke ni sai na faɗa ma aunty Kubra, ka san kuma ba ƙyale ka zata yi ba (Aunty Kubra ita ce wadda ta riƙe ta ta yi karatun primary a wurinta, kuma cousin ɗin innarsu ce, wato mahaifin innarsu yayan mahaifin aunty Kubra ne. Aunty Kubra ita da iyayenta suna zaune a garin Kaduna, saidai mahaifiyarta ta rasu, yayin da ita kuma innarsu iyayenta na zaune a nan garin Funtua, sannan mahaifin aunty Kubra dan boko ne kuma ma'aikacin gwamnati sa6anin mahaifin innarsu Salma da ba ɗan boko bane manomi ne) Dariya innarsu ta shiga yi ta tare Sageer ɗin tana cewa, "Sageer kana da hankali kuwa! Kashe min ita kake son ka yi dama kana ganin ita kaɗai Allah Ya bani yar mace...."

Cikin huci muryarshi da 6acin rai ya ce, "Wallahi innarmu duk ke kika sa ta raina mu, ko muna tare da abokanmu rashin kunya take mana don ta san ba ki bari mu hukunta ta."

Girgiza kai Innar ta yi tana ci gaba da yin dariya ta ce, "Duk fa yadda Salma ta kasance kai ne sila Sageer, nan yarinyar nan ta taso ba ruwanta shiru-shiru da ita magana ma sai ta kama take yi, amman ka dage sai ka canza ta kana ce mata sakarya, ba dama daga waje a yi mata abu ta yi kuka sai ka hau yi mata faɗa kana cewa in bata ramawa sai ka duke ta. Har fa yadda zata rinƙa yin dambe kake koya mata a cikin gidan nan, sai yanzu kuma da ta ɗauki horon ka ta kasance yadda kake so ka ce kuma zaka hukuntata kan hakan?"
Chapter 11 · 0% Book details