← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 197

Sashe 125

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

don ita dai bata taba sanin cewa ana bada saƙo ta jirgi ba kamar yadda ake yi ta mota, ba wannan ne ya fi ɗaure mata kai ba yadda zata bada saƙon fara ta jirgi, ita da ko airport ma bata ta6a zuwa ba, ko lokacin da tana wurin aunty Kubra da zata je makka gida aka maido ta, kasa daurewa ta yi ta ce, "Kuma har faran za a iya bada saƙon ta ta jirgi a kawo maka?" Shiru ya yi yana ɗan murmushi kaman ba zai ce komai ba ita kuma tana ta kallon shi alamar tana jiran amsa, ɗan gyara kishingidar sa ya yi calmly ya ce, "I don't know ko har shi za a iya bada saƙon shi, amman ina wasa ne, wani lokacin idan na zo sai ki yi mani." Ta ɗaga kai, shiru suka ɗan ƙara yi kafin ta ji ya ce, "Is there any problem?" Da sauri ta ɗan girgiza masa kai alamar a'a, ya ɗan yi shiru yana ta kallon ta ita kuma sai ɗan murmushi take yi tana sauke idonta, "Let me know if you need anything." Ta ji ya faɗa, ta sake girgiza masa kai, softly ya ce, "Mi yasa baki son faɗi mani?" Da sauri ta ce, "Allah da gaske nike yi bani buƙatan komai." Ya yi shiru yana kallonta, ita ce mutum ta farko da duk lokacin da zai tambayi idan tana da matsala ko tana buƙatan wani abu ta ke ce masa babu, ganin yadda yake kallonta ya sa ta yi tunanin ko bai yarda da abun da ta faɗa ba, tana kallonsa ta ce, "Ai kana bani albashi duk abun da nike so da su nike yin amfani." Kamar ba zai ce komai, sai kuma calmly ya ce, "But 50k a wata ba komai zai iya yi ba, and you also have your family to support" Ta ɗan langa6ar da kai tana ɗan faffaɗan murmushi ta ce duk 50k ɗin na isarta, wani kallo ta ga ya yi mata da sauri ta sa hannunta guda ta rufe rabin fuskarta, ya bita da kallo, sigh ya yi ya ce ya saka an tada ita tana bacci kuma ya san baccin relief ne a wurinta bari ya barta ta ƙara hutawa, tana kallon shi ta ce, "Yanzu na san sai bayan wani lokacin zamu ƙara magana." Ya ce, "Why do you say that?" ta ce, "Ba komai, kawai na ga kana zama busy sosai, ko saƙo na tura maka wani sai ya daɗe kafin ka duba." Kai ya ɗan ɗaga alamar haka ne kafin ya ce bai cika samun lokacin kan sa bane a irin wannan lokacin da suke yin gasanni sosai, ta ɗaga masa kai alamar ta fahimta, ta ji ya sake cewa, "I will send you another number, duk lokacin da kike son magana da ni ki yi amfani da shi, personal manager na ke kula da shi, I will tell him about you and he will help us get in touch when i'm available ." Ta jinjina masa kai sai kuma ta tambaye shi kira zata yi, ya ce duk yadda ta yi amman zai fi mata sauƙi ta kira whatsApp call ko ta sending masa message, idonta cikin nasa ta ce masa to, tambayarta ya yi shike nan ta yi saurin ɗaga masa kai ta ce, "Nagode, Allah Ya sa ku yi nasara." Ya ɗan lumshe ido tare da yin ɗan murmushi ya ce, "Amin thank you, Allah Ya baki lafiya." Ta amsa da Amin, ya ƙara cewa, "Take care." Ta ɗaga masa kai daga haka ya yanke kiran, Salma ta bi wayar da kallo bayan sun gama fuskarta da ɗan murmushi, bata yi tunanin zai iya kiranta vedio call ba kuma har su yi magana haka sosai, don tun da ya tafi ma basu yi magana ta kira ba sai dai ta chat, shima ba kowane sako in ta yi masa yake bata amsa ba wani lokacin sai daga baya, kuɗin albashinta dai da yake bata wannan da lokaci ya yi take ganin an turo mata ta account ɗinta, har tana tunanin kaman wani yasa yake tura mata, amman Sageer ya ce zai iya yuwuwa shine ya sa direct daga banki ake turo mata duk idan lokaci ya yi, ajiye wayar ta yi a gefe, har zata kwanta sai kuma ta sauko daga gadon tana tafiya a hankali ta nufi wurin dressing mirror, drawer ɗin farko ta buɗe ta saka hannu ta ciro wayarta, dawowa ta yi wurin gadon ta hau ta ta6a wayan ta kawo haske, bin saƙon da ta ga an turo mata a notification daga bankinta ta yi da kallo, hannu ta kai ta buɗe wayar ta shiga saƙon, lokaci guda ta zaro ido ganin kuɗi masu yawa da aka tura mata har miliyan ɗaya, kuma ta gane daga Deen ne don ta account ɗin da ake turo mata albashi ne, ɗan jimm ta yi tana ta kallon saƙon ƙirjinta har ɗan bugawa yake, tunanin mi yakamata ta yi ta shiga yi zuciyarta ta bata kawai ta kira shi ta yi masa godiya, sai dai ko da ta kira layin nashi baya shiga, whatsApp ta shiga ta kira sa voice call, har kiran ya ƙare ringing ba a ɗaga ba, kuma tana ganin kamar yana online don har ya turo mata lambar da ya ce ta nan, sake kiran sa voice call ta yi ta ga an katse kiran, kawai sai gani ta yi ya turo mata saƙo ya ce, "Just use it." Iya abun da ya rubuto mata ke nan, ta yi shiru tana ta kallon saƙon, ƙarshe ta tura masa saƙon godiya kafin ta miƙe ta nufi hanyar fita don ta je ta nuna ma innarsu. Har su Leemarh sun fara yin terminal exams din su, dad dinta ya sanar da ita da shi za su je Funtua bayan sun gama sai ya baro ta can ta yi hutu, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, har ta kira Fahad ta sanar da shi, shima ya nuna jin daɗin hakan, ya kuma ce ta maida hankali sosai kan jarabawarta ta yi masa alƙawarin yin hakan.
Chapter 125 · 0% Book details