← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 197

Sashe 158

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨A CIKIN RAYUWA✨

ZAINAB BATURE

51

A saman gado Maleek ya kwantar da Sapna ya nufi bathroom ɗin ɗakin da sauri, ruwa ya ɗebo ya dawo ya ɗan yayyafa mata a fuska, numfashi ta sauke kafin a hankali ta fara motsa idanunta, Maleek ya zauna gefen ta yana kallon ta tare da kama hannunta guda, a hankali ta fara buɗe idanunta, bin Maleek ta yi da kallo kamar mai son tuna abu, sannu da ya ce mata ta sa komai ya dawo mata akai hawaye suka fara zubo mata, "Why ka ƙi sanar mani tun farko honey? Wannan ba abu ne da ya kamata ka 6oye mani ba, da na sani zan fi ɗaukar matakin da ya dace..." Shiru ya ɗan yi shima ƙwalla sun cika idanunsa, cikin raunanniyar murya ya ce, "Ina gudun halin da zaki iya shiga idan kika ji ne." Ɗan girgiza kai ta yi ta ce, "Duk da haka da ka sanar mani, ai ni musulma ce na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau." Shiru ya yi kawai yana ta kallon ta, juyar da fuskarta ta yi tana sake ambaton innalillahi....a hankali ta furta, "Ya aka yi baby ta koya wannan mummunan ɗabian?" Maleek ya ce shima abun da ke ta damunsa ke nan don ya gane duk abubuwan da ta faɗa masa a baya ba gaskiya bane, shiru Sapna ta yi idanunta na kallon gefe, wani irin faɗuwa gaban ta ya shiga yi lokacin da wani tunani ya zo mata, can ta yunƙura Maleek ya kalle ta da sauri ya ce mata ina zata je cikin muryarta da har ta ɗan disashe ta ce bathroom zata shiga, taimaka mata ya yi ta sauka daga gadon cikin rashin ƙwarin jiki ta nufi banɗakin ya bita da kallo cike da tausayawa, Sapna na shiga ta kulle ƙofar, gaban mirror ɗin kewayen ta tsaya tana kallon kanta lokaci guda ta saki sabon kuka tare da kai hannu ta toshe bakinta, wllh ta matuƙar girgiza da jin wannan abu, ta ɗauki tsawon mintuna a haka dama ba wani abu zata yi ba kawai ta rasa mike mata daɗi ne, wanke fuskarta ta yi ta nufi ƙofa, lokacin da ta fito bata iske Maleek ba a daƙin kamar yadda ta bar shi, bakin gado ta nufa ta zauna ta tsura ma guri guda ido yayin da ƙwalla ke ci gaba da gangaro mata, duniyar tunani ta afka can ta ɗan waro ido a cikin ranta ta raya, "Kada dai a ce halin wasu daga familynta ne ya shafi baby!" Tashin hankali ne ya bayyana sosai akan fuskarta da ta yi wani irin jajir alamar motsuwar jini, duk da rashin ƙarfin jikin da take ji haka ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita. Lokacin da ta dawo main falon ba kowa a ciki, ɗakin mrs Helen ta nufa ta tambaye ta baby nan ta sanar mata ta koma ɗakinta, bayan ta fito bene ta nufa cikin mutuwar jiki ta fara hawa, ɗakin Basma ta nufa koda ta kai hannu ta tura ƙofar ta ji a rufe take, hannunta ta saka a na'urar jiki nan ma bata buɗe ba hakan ya sa ta gane ta kulle ta ciki, kiran sunanta ta fara yi tana cewa ta buɗe mata ƙofa, shiru har bayan wani lokaci ba alamar zata buɗe, hankalin Sapna ne ya ƙara tashi bayan tunanin kada a ce Basma ta aikata ma kanta wani mummunan abu ya zo mata a rai, da ƙarfi ta shiga bugun ƙofar tana kiran sunanta, "Baby...I know you can hear me...come and open the door I want to talk to you." Haka ta koma tana faɗi cikin ɗan ɗaga murya, sai can bayan wani lokaci ƙasa ƙasa ta jiyo muryar Basma tana magana, sai dai sam bata gane abun da take cewa, kanga kunne Sapna ta yi tana son ta ji abun da take faɗi, da ƙyar ta jiyo ta tana cewa, " I'm sorry mom...I promise....i won't do it again..." Cikin kwantar da murya Sapna ke ce mata to ta buɗe ƙofar tana son magana da ita ne ba wani abu ba, ta ji ta ce, "Kema na san zaki buge ni ne." Da sauri Sapna ta ce mata a'a ba bugun ta zata yi ba kawai magana take son za su yi...sai da Sapna ta yi fama da ita sannan ta ji ta buɗe ƙofar, lokacin da ta shiga cikin ɗakin, Basma har ta kai bakin bathroom tana ta zare ido alamar ƙiris take jira ta faɗa cikin banɗakin, bin ta da kallo Sapna ta yi, jikinta ta saka doguwar riga gashinta duk a hargitse kamar sabon kamu, har lokacin goshinta da gefen bakinta suna fitar da jini amman ba sosai ba, maimakon Sapna ta ji haushin ta sai ma wani irin tausayin ta da ta ji ya kama ta, Basma da take ƴar gayu yau ita ce a haka, jiki a sanyaye Sapna ta ƙarasa shiga cikin ɗakin ta zauna a bakin gado, da hannu ta yi mata alamar ta zo, cikin marairaicewa ƙwalla na zubo mata ta ce, "Za ki buge ni..." Sapna ta girgiza mata kai ta ce ba bugun ta zata yi ba, "To ki rantse ba zaki buge ni ba." Basma ta faɗa da muryarta da har ta shaƙe, da alama dai ta gigita da bugun da Maleek ya yi mata, koda yake abu ne da bai ta6a faruwa da ita ba, tun da take ko hannunta ba a ta6a ta6awa ba da sunan bugu, Sapna da ke ta kallon ta sai da ta rantse mata ɗin sannan ta matso, amman ɗan nesa da ita ta durƙusa kan gwiwunta a ƙasa, sauka Sapna ta yi itama ƙasa da sauri Basma ta ƙara ja baya, Sapna na fuskantar ta cikin raunanniyar murya ta ce,"Baby why....miyasa kika ɗauki wannan mummunan ɗabi'an...mi kika nema kika rasa baby...kin san girman laifin abun da kike aikatawa a addini...why baby...why kike son lalata rayuwan ki?" Shiru Basma ta yi ta sauke idanunta da suka kumbura ƙasa tana shesshekar kuka, "Now i want u to tell me the truth, kuma bana son ki yi mani ƙarya kaman yadda kika yi ma dad ɗin ki, a ina kika koyi hakan?" Ɗago ido Basma ta yi ta ji ba zata iya yi ma mom ɗin nata ƙarya ba, cikin rawar murya ta ce, "Ba wani ya koya mani ba...kawai na ji ina son yi ne." Da sauri Sapna ta juyar da fuskarta tare da ɗage kanta irin alamar mutum ya bani ɗin nan, a cikin ranta take nanata "Wllh jini ne..." Sake kallon ta ta yi ƙwalla sun ciko idanunta ta ce, "Tun yaushe ne kika fara aikata haka?" Miyau Basma ta haɗiya kafin ta ce, "...since I was in secondary school..." Wannan karon kuka mai sauti Sapna ta saki jin ta daɗe tana aikata hakan don yanzu tana a jami'a ne zata shiga shekara ta ukku da hutun su ya ƙare, cikin kuka Sapna ke tunanin ta ina ma za su tari al'amarin, itama Basma kukan take sosai ta sadda kanta ƙasa, "Yanzu baby ki faɗi mani ya kike so mu yi maki...komi kike so in dai zaki daina aikata hakan ki faɗi mani wllh zan yi maki, koda duka abun da na mallaka zai ƙare in dai hakan zai saka ki daina aikata hakan zan yi maki....tell me baby what do you want?" Ɗago kai Basma ta yi hawaye sun wanke mata fuska cikin muryar kuka ta ce, "Ina son Aure mom...ina son a yi mani aure da ya Deen." Shiru Sapna ta yi tana kallon ta da jiƙaƙƙun idanu, sam bata ji Basma ɗin wai ko ta yi rashin kunya ba da ta faɗi haka, a cikin ranta take tunanin ko dai Basmar na daga irin mutanen da ake halitta da ƙarfin desire, a ganinta wannan ba wata babbar buƙata bace tun da dama akwai maganar auren a tsakanin su, ke nan idan hakan ne komai zai zo da sauƙi, ajiyar zuciya Sapna ta sauke ta ce, "Kin tabbata zaki daina a yi maki auren?" Da sauri ta jinjina mata kai, hannu Sapna ta kai ta goge ƙwallan fuskarta, da hannu ta yi mata alamar ta zo wurinta, ganin yanayin Sapna ɗin ba a fusace take ba ya sa a ɗarare ta matsa wurinta, hannu ta kai ta ta6a jikin Basma ta ji da zafi sosai, dama daga yanayin ta ta fahimci kamar tana running a temperature, miƙewa ta yi ta ce mata yanzu zata dawo, kamar ta san abun da Basma ɗin ke niyyar yi bayan ta kai bakin ƙofa ta juyo ta ce mata kada ta rufe ƙofar, zaune ta yi a wurin tana ta faman zare ido, gaba ɗaya a tsorace take da kada dad ɗinta ya shigo, after some few minutes Sapna ta dawo hannunta riƙe da ɗan first aid box, a bayanta mrs Helen ce riƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci, a nan ƙasa Sapna ta sa ta ajiye tray ɗin kan carpet kafin ta ɗago ta yi ma Basma sannu Sapna ta ce zata iya tafiya, mrs Helen ta nufi ƙofa har lokacin kanta a ƙulle yake dangane da wani irin laifi Basma ta aikata har dad ɗinta ya yi mata wannan jan bugun, da ƙyar Sapna ta tursasa Basma ta ɗan ci abinci ba sosai ba don da farko ta ce ba zata ci ba, bayan ta gama ta yi mata dressing ciwukanta tare da bata maganin zazzabi, sata ta yi ta hau gado ta kwanta, daga haka ita kuma ta nufi ƙofa ta tafi da niyyar zuwa ta iske Maleek kan maganar da suka yi da Basma ta son a yi mata aure da Deen.
Chapter 158 · 0% Book details