← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 197

Sashe 59

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Wararen ƙarfe sha biyu saura Salma ta nufi kasuwa bayan ta taso daga islamiyya, a nutse take tafiya a gefen hanya tana sanye da dogon hijab ɗin islamiyyarta, daidai lokacin da ta zo ƙarshen hanyar zata hau babban titi ta hango mota na tahowa ta hanyar da take, hakan ya sa ta dakata don motan ta wuce, lokacin da motar ta ƙaraso saitin ta sam Salma ta kasa ɗauke idanunta akan motar, bama ita kaɗai ba duk idanun mutane na akan motan, hatta waɗanda ke a saman ababen hawa kallon motar suke, a cikin rai Salma ke faɗin, "Wannan wata irin mota ce! Amman dai ta haɗu sosai...." Ita tun da take ma bata ta6a ganin mota irinta ba, ɗan gaba da ita motan ta tsaya da alama mai motan na jiran ababen hawa su gama wucewa ne ya hau kan babban titin, sam ba a ganin wanda ke a ciki hakan ya ɗarsa ma mutane mamakin waye mamallakin haɗaɗɗar motar wadda mafiya yawan mutanen garin basu ta6a ganin irinta ba, a maimakon motar ta tsallaka sai gani Salma ta yi ta ɗan yo baya hakan ya sa ta yi saurin ƙara matsawa gefe don ta ba motan wuri, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan glass ɗin ta ya fara sauka ƙasa a hankali, bugawa ƙirjin Salma ya yi damm! lokacin da idanunta suka yi tozali da wanda ke a mazaunin driver, nan take ta dabarbarce ta shiga motsa baki don bata yi zaton shi zata gani ba, kallonta ya yi suka haɗa ido ta shiga kikkafta nata, da kai ya yi mata alamar ta zo, tamkar wadda babu laka a jikinta haka ta ɗan matsa sai dai bata yadda ta yi saiti da shi ba, "Ina..kwa...wuni." Ta faɗa cikin dabarbarcewa, kai ya ɗaga kawai ta sunnar da kanta ƙasa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ta ji ya ce, "Where are you going to?" Da sauri ta ɗago ta kalle shi sai ka ce bashi ya yi maganar ba, da ƴar rawar murya ta ce, "Kasuwa aka aike ni..." Shiru ya ɗan yi tare da ɗauke idanunsa, ƙasa-ƙasa ta ji ya ce, "Get in to the car.." Ta wani zaro ido sai ka ce wadda aka faɗa ma wani mugun abu, kokonto ta shiga yi na abun da ta ji ya faɗa haka ne ko kuwa dai kunnuwanta ne suka jiye mata ba daidai ba, after some seconds ya yi mata wani kallo ya ce, "Baki ji maganan da na yi ba?" Da sauri ta ce, "Cewa ka yi in shigo motan?" Kai ya ɗan ɗaga mata alamar yes, sumi-sumi ta zagayo ɗaya bangaren, sai da ta ɗan yi tunanin ina zata shiga tsakanin gaba da baya, ƙofar baya ta buɗe kafin ta shiga ta ɗan ɗago ta kalli mutanan dake a area ɗin, sai da gabanta ya ƙara bugu ganin gaba ɗaya idanun mutanen wurin na a kan ta, ruɗewa ta yi da ganin yadda ake kallonta da sauri ta kama handle ɗin ta ja ya buɗe ta shiga bugun ƙirjinta na ƙara tsananta tamkar wadda ta aikata wani laifi, wani irin ni'imtaccen sanyi ne tare da ƙamshi mai kwantar da zuciya suka tarbe ta, bin cikin motan ta yi da kallo at the same time al'ajabi ya bayyana akan fuskarta, ita dai ko a film bata ta6a ganin mota haka ba balle a zahiri, ɗaga kanta ta yi sama ta ɗan waro idanu ganin yadda take ganin kanta tamkar tana kallon madubi, tana cikin kalle-kallen ta sauke idanunta a kan madubin gaban motan karaf suka haɗa ido, da sauri ta sunne kanta ƙasa cike da jin kunya, duk yadda Salma ta so ta kama kanta ta kasa a hankali take ci gaba da bin cikin motan da kallo, tafiya suke suwet kamar ba a mota ba don ba wata ƙara ko irin gumin cikin mota da zaka ji wani lokacin haɗe da warin fetir, sauke idanunta ta yi akan screen ɗin da ke a kusa da sitiyarin motan, wani sabon mamakin ne ya kamata ganin duk abun da ke faruwa a bayansu ana gani ta cikinsa kamar vedio, "I don't know the place, zaki nuna mani..." Da sauri ta kai idanunta kansa jin ya yi magana sai dai bata ji abun da ya faɗa ba, daga yanayin kallon da ya ga tana mashi ta cikin madubi ya gane bata fahimci mi ya ce ba, haɗa ido suka yi ta madubin calmly ya sake faɗar abun da ya faɗa ta ɗaga mashi kai alamar toh, tafiya kaɗan suka ƙara suka zo roundabout, da sauri ta ce mashi da an ɗan wuce round ɗin ne wurin, bayan ya yi parking ya bi wurin da kallo, hannu ta kai za ta buɗe kofar saidai in da ta yi tunanin nan ne ake buɗewar ta ta6a amman kofan ta ki ta buɗe, juyowa ta yi da niyyar yi masa magana daidai lokacin shima ya juyo idanunsa suka shiga cikin nata ya ce mata, "But nan kasuwa ne?" Kikkafta idanu ta shiga yi ta ce, "A'a, amman da na ɗan ƙara gaba kasuwan take, a zagaye take mota bata shiga sai dai a aje a bakin hanya." nodding kai ya yi tare da juyawa, ganin bai gane ta kasa buɗe kofar ba ya sa innocently ta ce, "Ban san ya zan buɗe kofar ba..." Haɗa ido suka yi ta mirror ta yi saurin sunnar da kai, bata san ina ya ta6a ba kawai ta ji kofar ta yi wani ɗan sauti har sai da ta ɗan tsorata ta yi saurin kallon ƙofar ta ganta a buɗe, har zata fita ta juyo a hankali ta ce, "Na gode.." Kai ya ɗaga ba tare da ya kalle ta ba, tsaye ta yi bayan ta fito tana kallon motar ya ja ya tafi, sai da motar ta 6ace ma ganinta sannan ta ankare da irin kallon da mutane suke yi mata, da sauri ta juya ta fara tafiya ta gefen hanya, yayin da a cikin ranta take ta jinjina haɗuwar motar, ta raya a zuciyarta ba tantama ita ce motar da Sagir ya zo yana masu santi, ita cikin motar ya fi yi mata kama da irin cikin private jirgi da take ganin hoto , "Anya ba jirgi bane aka yi da suffar mota?" ta yi tambayar a ranta, ƙarshe zuciyarta ta yanke hukunci da alama ma hakan ne, maida akalar tunaninta ta yi kan yadda akai har ya ganta ya gane ta ya tsaya ya ɗauke ta, tunowa ta yi da screen ɗin nan dake nuna mashi komai dake faruwa a bayan shi ta raya ta san ta hakan ne ya ganta, tana ta tunane tunane har ta iso kasuwar. Bayan Deen ya isa gidansu Fahad ya yi parking motan, kai tsaye cikin gidan ya nufa, Sadeeya na zaune tana latsa waya ta hango shi ya shigo, miƙewa ta yi tana murmushi ta nufe shi tana masa welcome, hannunta ya kama bayan ya amsa suka dawo wurin kujerun, Khaleel dake kwance shima yana latsa waya ya miƙe zaune da murmushi ya ce, "Ya Deen sannu da zuwa." Da murmushi ya amsa mashi yana kokarin zama a saman 2 sitter Sadeeya ma ta zauna gefensa, tambayar su Binafa ya yi Sadeeya ta bashi amsa da suna islamiyya sai yamma, momy ce ta ƙaraso wurin su da fara'a ta ce, "Son, an shigo." Amsa mata ya yi kafin ya gaishe ta ta amsa tare da zama, "Ya hajiya da gajiyan ɗanin mota." Yana murmushi ya bata amsa da tana gida tana gaishe su, "Da jigunannar motar ka zo?" Sadeeya ta tambaya, ƴar dariya ya yi jin yadda ta kira motan ya ce mata eh, miƙewa ta yi tana faɗin bari ta je ta yi hotuna dama jiya don dare ne ya sa bata yi ba, miƙa mata makullan motan ya yi ta amsa da sauri tare da faɗin yauwa ta gode, kallon Khaleel ta yi ta ce ya zo su je ya yi mata hotunan ya amsa da toh tare da miƙewa, "Kafin ki tafi yin packaging ɗin ki fara samo mashi abun da zai ci." Momy ta faɗa tana murmushi, Sadeeya ta yi dariya tare da faɗin, "Kai momy, ai ba packaging bane tun da dai motan mallakinmu ce." Kallon Deen dake murmushi ta yi ta ce breakfast zata haɗo mashi kafin a gama abinci, ya ce mata no baya jin yunwa ya yi breakfast, ta ce to bari ta kawo mashi ko lemu shima ya ce ta basshi ta je, momy ta ce, "Son ka bari ta kawo maka wani abu mana kafin a ƙarasa abincin." Calmly ya ce mata yanzu baya jin yunwa a bari sai an gama abincin ta amsa da ok, bayan tafiyar su Sadeeya ya tambayi momy ko daddy na nan ya je ya gaishe shi, ta ce, "Eh yana nan, suna tare ma da Fahad a can part ɗin sa ina tunanin wani aikin suke yi." Miƙewa ya yi ya ce bari ya je part ɗin ya gaishe da shi ta amsa masa da ok, bin shi da kallo momy ta yi bayan ya nufi bangaren daddyn fuskarta da murmushi, tana son yaron saboda yana da hankali da natsuwa, duk da irin ɗaukakar da ya samu sam bai yada nasa ba ko ya canza masu, sam bai ɗauko ɗaya daga cikin halayen mahaifiyarsa ba, ta6e baki momy ta yi tunowa da irin munanan halayen mom Jameela, ba don ita ɗin tana da kyakkyawar zuciya ba ai ko kallon Deen ba zata yi ba balle ma ya ga murmushinta duba da yadda mahaifiyarsa ta yi maltreating mata yaro lokacin da yana wurin su. Da sallama Deen ya shiga falon daddy, a tare suka kai idanunsu kan ƙofa, da murmushi suka amsa masa ya ƙarasa ciki, daddy na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum biyu, Fahad na zaune daga gefensa a saman carpet, system ce a gaban Fahad da wasu takardu a gefe, "Barka da zuwa son." Daddy ya faɗa idonsa akan Deen da ya zauna a ƙasa gefen Fahad, da murmushi ya ce, "Yauwa daddy, ina wuni." Amsa mashi ya yi ya tambayi hajiyarsa, kallonsa Fahad ya yi yana murmushi ya ce, "Sannu da zuwa..." Ya ɗaga masa kai, bayan shiru na ɗan lokaci dad ya kalli Fahad ya ce, "Ka ce gaba ɗaya lissafin ya kama nawa?" amsa ya bashi ya ce, "Abun da ya bada 135m." Kai daddy ya jinjina sai kuma ya ce, "Ka saka har da na waɗanccan kayan da na fada maka?" Kai Fahad ya jinjina ya ce yes, daddy ya jinjina kai tare da komawa ya jingina bayansa da jikin kujera yana murmushin sa na dattako ya ce, "Alhamdulillah, saura mu ga abun da kuma wannan damunar zata kawo mana. Allah Ya saka mata albarka." A tare Deen da Fahad suka amsa da Ameen. "Son, ka zo muna ta lissafi, haka hanyar samun namu ya koma tun da yanzu ba aikin gwamnati, wannan ne ya koma aikin office ɗin nawa." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, shima Deen faffaɗan murmushi ne akan fuskarsa ya ce, "Allah Ya ƙara sama nema albarka daddy." ya ce, "Amin my son, Ya saka ma nemanmu baki ɗaya. Dama haka abun yake kowa da kalar hanyar samun sa, ga ɗan'uwanka nan shi rashin lafiyar mutane ne tasa hanyar samun, sa6anin kai kuma nishaɗin mutane ne naka hanyar samun." Gaba ɗaya faffaɗan murmushi ne akan fuskokinsu,
Chapter 59 · 0% Book details