Sashe 38
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka taso jiki a mace suka baro part ɗin, bayan dawowar su 6angaren hajiya, ɗaya cikin su ta kasa haƙuri ta gaya ma hajiya irin wulaƙancin da aka yi masu, ran hajiya ya 6aci sosai nan Asabe ta ƙara faɗa mata cewa ba wannan ne karo na farko ba don ko ranar da wasu danginsu suka zo ta saka ta raka su suma haka ta yi masu, bayan sun baro part ɗin su baƙin ne suka roƙe ta kan kada ta sanar ma hajiyan, Asabe na rufe baki hajiya ta miƙe, wata a cikin baƙin ta fara mata magiya kan ta rabu da ita kawai yayin da wadda ta faɗi ma hajiyar abun da aka yi masu cikin 6acin rai ta ce ta ƙyale ta, gara ta je ta ja mata kunne in ma zata rinka wulaƙanta mutane to ban da su da suke dangin su.
Jameela na ganin yanayin fuskar hajiya bayan ta isa falon ta sha jinin jikinta, tsaye ta yi a tsakiyar falon ba tare da ta zauna ba, Asabe da suka taho tare na daga gefen ta a baya, cikin yanayi na bacin rai tana kallon Jameela ta ce mata don me take hana mutane su ga Deeni kuma ma har da waÉ—anda suke dangin shi! Nan ta shiga Æ´an kame-kame tana kifce-kifcen idanu ta ce tun kwanaki da wasu suka zo aka basu shi bayan sun tafi ya yi ta kuka har jijiyoyin kan shi suka fito, da ta rasa mike damun sa sai ta kira Ammin su ta sanar mata, shine Ammin ta tambayi wani malami dake a layin su ya ce a daina ba ko wane mutane shi don mayya ce ta so kama shi, baki a kwa6e hajiya ke kallon ta har ta gama, sam bata ma yarda da zancen nata ba, daga yanayin fuskarta da yadda take yin maganar zaka fahimci karya take faÉ—i, bayan ta gama bayanin cikin É—aure fuska hajiya ta ce mata to su kaf dangin su babu mai maita, kuma ba wannan bace haihuwar da kaÉ—ai aka ta6a yi a familyn su da za a ce maitar bata ta6a shafar wani ba sai shi, don haka daga yanzu kada ta sake jin wai ta hana wani yaro koda bacci yake indai aka zo ganin shi to a É—auko shi a ba mutane, in ba haka ba ranta zai 6aci,
"Asabe je ki kar6o shi!" Cike da bada umarni ta ce ma Asabe, nufar Naila ta yi ta je ta amso babyn, juyawa hajiya ta yi tana faɗin Ibarahim ɗin zai dawo zata ji in har da shi ya bada goyon baya ake ma dangin shi hakan, Jameela da Naila suka bi su da kallon harara har suka fuce. Bayan wata ɗaya da yin haihuwar Maleek ya zo daga ƙasar India da a lokacin a can yake aiki da wani kamfani da ya danganci fasaha, kuma sannan yana ci gaba da yin karatun degree ɗin shi na biyu wato master's degree. A gidan su na Kano ya sauka, a ranar da daddare ya shirya zuwa wurin Sapna wanda shine karo na farko da zai fara zuwa gidan su tun bayan da suka shaƙu da juna, har abun ya juye ya koma soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, sai dai ba wanda ya sani sun bar abun a tsakanin su, Sapna ta yi farin cikin jin zuwan shi lokacin da ya kira ta ya sanar mata, duk da ta wani 6angaren tana ɗan jin fargaba saboda bata san yadda zata tarbe shi ba, a wata haɗaɗɗan ash din mota ya isa gidan su bayan la'asar, jikin shi sanye da jeans da t-shirt, kiranta ya yi ya sanar da ita ya iso, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana sanye da brown ɗin doguwar riga ta ɗaura ƴar ƙaramar baƙar hijab mai tattara a ƙasa, ta yi kyau sosai cikin shigar haskenta ya fito fayau, yana ganin ta ya sauke glass ɗin motar ya zuba mata ido yayin da take nufo motar tana tafiya a nutse, tun da suka haɗa ido ta sadda kanta ƙasa tana murmushi, yana daga abun da yake ƙara mashi son ta yadda take da kunya ga kamun kai, daga gefen ƙofar da yake ta tsaya tana kallon shi, haka shima idanunsa na a cikin nata suka shiga sakar ma juna murmushi, sam ta kasa yi mashi magana don tun da abun su ya juye zuwa soyayya basu ga juna ba,
"Ko dai ba a murnar gani na?" Ya faɗa da muryarsa mai cike da natsuwa, ɗan girgiza mashi kai ta yi still tana ta murmushi, ɗage gira ya yi ya ce gashi nan ta ƙi yi mashi magana idan ta ji daɗin ganinsa ai baza ta ƙi yin magana ba,
"To ai saboda murnan ne na kasa magana." Ta faɗa da ƴar zazzaƙar muryar ta, har saida ya ɗan lumshe ido yana murmushi, ce mata ya yi ta shigo cikin motan, ta yi ɗan jim tare da ɗan wawwaigawa ganin ba mutanen dake kallon ta ya sa ta zagaya ta shiga, wani ni'imtaccen sanyi haɗi da kamshi mai daɗi suka ratsa ta, gaishe da shi ta yi tare da yi mashi an zo lafiya ya amsa yana kallonta cike da so da kauna, shima ya tambayi yadda take tare da ƴan'gidansu ta amsa da duk suna lafiya, hira suka shiga yi irin ta masoya duk da ita bata cika yin magana sosai ba sai dai murmushi kawai, har yake tambayarta ya babyn su na wurin sister ɗinta ta amsa da duk suna lafiya, ya ce bai samu zuwa ya ganshi ba lokacin da aka yi haihuwar yana yin exams ne, kai ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba, ce mashi ta yi bari ta kawo mashi ruwa ya yi saurin dakatar da ita ya ce akwai ruwa a motan, ta ce to bari ta kawo mashi lemu, shima ya ce mata ta barshi, da ɗan yanayin shagwa6a ta ce ke nan yana nufin ba zai sha komai ba, murmushi ya yi ya fahimci ta iya shagwa6a duk da kunya na hanata yi sosai, tambayar ta ya yi ita ta haɗa lemun,
"A'a na shago ne, ban san da yau zaka zo ba dana haÉ—a maka, kuma lokacin da ka kira ni ka ce zaka zo nan ba time sosai." Ta faÉ—a tana yi tana sauke idanunta,
"Siyo mani kikai ke nan?" Kai ta É—aga mashi,
"Ok, tun da saboda ni aka siyo idan zan tafi sai a É—auko mani." Kai ta jinjina mashi suka É—an yi shiru,
"Ya maganar karatun ki, yaushe ne zaki fara tun da kin samu points mai kyau?"
Ta ce,"Yanzu ina jiran lokacin da zamu yi post utme ne." Kai ya jinjina suka ɗan ƙara yin shiru,
"Ai ina tunanin ci gaba da karatun ma anan babu shi..." Da sauri ta kalle shi, ya ci gaba, "I think ya kamata mu yi aure, da yadda na tsara sai na gama karatuna sannan, amman i have changed my mind." Da sauri ta sadda kanta ƙasa jin maganar aure da ya yi, ƴar dariya ya yi, "Ko baki shirya mu yi aure ba yanzu?" Tana a yadda take ta girgiza mashi kai, ce mata ya yi ta ɗago sosai su yi magana wannan serious abu ne, ɗagowa ta yi tana kallon shi ya tambayi miye ra'ayin ta kan hakan,
"Duk yadda ya yi maka nima ya yi mani, amman tun da ka ce kafi son sai ka gama karatunka ko ka bari idan Allah Ya kaimu ka gama É—in."
Iska ya ɗan furzar tare da shafa lallausar sumar kan shi ya ce, "Ai My Sapnah na ga nema kike ki hana ni maida hankali akan karatun, tunanin ki yana yi mani yawa gashi karatun mu baya son wasa, that's why I just decided in mallake ki ki kasance a tare da ni ko na tsayar da hankalina wuri ɗaya, idan muka yi auren a can sai ki ci gaba da karatun kawai." Wani irin daɗi ne ya lullube ta ta shiga yin murmushi dake bayyana hakan, tambayar ta ya yi ta amince su yi auren ta ce mashi eh, a nan suka gama magana ya ce zai sanar da mahaifin shi a zo nema mashi aurenta tun da yana a gari ko mi ake ciki zai mata magana, da zai tafi ya bata tsarabar da ya yo mata. Cike da farin ciki Sapna ta ƙarasa yinin ranar duk da a cikin zuciyar ta tana zullumin kada a ƙi amincewa da maganar auren nasu.
Bayan ya samu dad ɗinsa da maganar ya ce mashi ya jira zai neme shi, mahaifin su Ibraheem dad ɗin Maleek ya kira ya shaida mashi game da auren da Maleek ɗin ke son a nema mashi na yar'uwar matar Ibrahim, ya tambaye shi shawara game da hakan, a nan ambasada ya ce mashi ya bari za su yi magana da hajiya don ita tafi shi sanin abun da ya dangance su, hajiya ta yi mamakin jin Maleek yana son auren ƙanwar Jameela, saidai ita kanta ta fahimci Sapna ta sha bambam da sauran ƴan gidansu tun daga bikin Ibrahim ta gane hakan, ko lokacin da suka zo bayan ta haihu ita kaɗai ce ke zuwa ta gaishe ta safe da yamma har aiki take yi mata, koda ta ce ta bari sai ta yi kamar gyara mata falo da taya Asabe aiki, har Ibraheem ta kira ta tambaye shi game da halayen Sapna ya tabbatar mata da ta fi kowa kyawun hali a gidansu Jameela, anan yake ji a bakin hajiya cewa Maleek ne ke son auren ta, aikuwa ya yi mamaki sosai don shi kawai ya san dai suna mutunci da juna amman bai san abun ya juye zuwa soyayya ba.