Sashe 129
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da gadon ya tsaya yana kallonta, "Have you prayed?" Ta ji saukar muryarshi yana tambayarta ta yi salla, ɗago ido ta yi suka shiga cikin nasa ta ɗaga masa kai alamar eh, kauda nasa idanun ya yi, ya yarda da ta yi sallan don ga abun salla da hijab nan a wurin da ta saba yin salla, kallon shi ta ci gaba da yi fuskarta a marairaice, ta lura da ko kallonta baya son yi abun da bata ta6a tunanin hakan zata kasance a tsakanin su ba, kneel down ta yi a saman gadon cikin rawar murya ta ce, "Dad pls ka yafe ni, na yi alƙawarin ba zan ƙara ba....na tuba don Allah kada ka yi fushi da ni..." Ɗan lumshe ido Maleek ya yi, idan ya ce yana jin daɗin hakan dake kasancewa a tsakanin sa da gudan jininsa mafi soyuwa a garesa ya yi ƙarya, to amman ba yadda ya iya dole ne yasa ta gane ta aikata laifi mai girma da muni, "Pls dad...." Ya ji ta sake faɗa, slowly ya maido idanunsa kanta, da sauri ta haɗe hannuwanta ƙwalla na zubo mata tana kikkafta idanu, "Kin san cikin irin halin da kika jefa ni Basma..." Cikin raunanniyar murya ya faɗi hakan, shesshekar kuka ta shiga yi tana kallonsa, "Har yanzu ina tantamar idan da gaske ke ce kika aikata hakan..." Ya jinjina kansa, still tana akan gwiwowinta cikin kuka ta ce, "Aikin shaiɗan ne dad, don Allah ka yafe min. Na san na yi kuskure, kuma ba zan sake ba....wallahi ba zan sake ba." Yana kallonta ya ce, "Ke kika ba shaiɗan ɗin goyon baya, kin za6i aikata hakan da iliminki, kin san abu mai kyau da mara kyau." Sauke idanunta ta yi ƙasa ƙwalla na ci gaba da saukar mata tana yamutsa yatsun hannunta, "I will ask you some questions, bana son ki yi mani ƙarya." Da sauri ta kalle sa tare da jinjina masa kai, shiru ya yi idanunsa na kallon direction daban, bai da yadda zai yi da zai mata tambayoyin amman ba don yana son hakan ba, "Who is the other girl?" Bayan ɗan lokaci kamar ba zai yi magana ba ta ji ya tambaya muryarsa ƙasa, da sauri ta maida idanunta ƙasa bugun ƙirjinta na ƙara tsananta, ita kanta tambayar ta saka ta jin ba daɗi a cikin zuciya, da ƙyar ta furta, "It's Huda." Ɗan runtse ido Maleek ya yi don ya san Huda ɗin best friend ɗin ta ce, bai ta6a zaton a tarayyar su suna aikata abu mara kyau ba, itama Huda mahaifiyarta likita ce ƴar nijeriya kuma ƙawar Sapna, amman mahaifinta Bature ne ɗan nan ƙasar kuma a kamfanin Maleek yake aiki, sau da yawa Basma tana tambayar iyayen nata kuɗi ta ce zata siya ma Huda abu, ko kuma idan aka siya mata kaya ta fidda wasu ta ce Huda ɗin zata ba, har ta kai wani lokacin idan suka yi mata siyayya har da Huda ɗin suke siya ma wasu abubuwan, dalilin shaƙuwar yaran nasu ya sa suma iyayen suke mutunci sosai da juna, har ma ta kai sun zama tamkar ƴan'uwa, kuma Maleek na yi ma dad ɗin Huda alkhairi mai yawa duk dalilin abotar yaran nasu, sai da Maleek ya ji kamar ba zai iya ci gaba da yi mata tambayoyin ba saboda zullumin da ya kama sa na kada ya ƙara jin abun da zai ƙara girgiza masa zuciya, amman ba yadda zai yi dole ya binciki yadda aka yi ta fara aikata hakan, "Ban da ita sai wa kuke yin hakan tare?" Ba tare da ta kalle sa ba ta ce masa ita kaɗai ce, ya ce mata ya ce bai son ta yi masa ƙarya, still ba ta kalle sa ba ta ce wallahi ita kaɗai ce, "Waye ya koya maku?" Bugun ƙirjin Basma ya ƙaru, cikin raunin murya ta ce, "Wata cousin sis ɗin Huda ce da ta zo hutu daga U.S." Maleek ya yi shiru tun da ya fara mata tambayoyin bai kalle ta ba, "Tun yaushe ne kuke yi?" Saida ta haɗiyi miyau kafin ta basa amsa da an yi shekara guda, Maleek ya girgiza da jin cewa shekara guda suna aikata hakan ba tare da asirin su ya tonu ba, tambayarta ya sake yi a ina suke aikatawa, ta ce masa a nan gidan ko a can gidan su Huda, ya ce kenan duk dawowar da take yi daga makaranta ba tare da lokacin tashin ta ya yi ba ta faɗi wani uzurin abun da take dawowa yi ke nan, murya na rawa ta ce wasu lokuttan amman ba duka ba, wani lokacin da gaske idan ta ji bata jin daɗi sai ta dawo, shiru ya yi ya ɗan cije lebensa na ƙasa tare da rufe idanunsa, jin bai ƙara cewa komai ba ya sa ta ɗago idanunta da suke jiƙe tai ta kallon sa tana jin wani iri a cikin ranta, after a while ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da juyawa ta ji ya ce ta sako veil ta biyo sa daga haka ya nufi ƙofar fita, hannu ta kai ta ɗauki gyalen ta dake a gefe saman gadon kafin ta sauka daga saman gadon, bayan ta ɗaura gyalen a saman dogowar rigar jikinta cikin sanyin jiki ta bi bayansa, sauka ta gansa ya yi ƙasa itama ta fara taka mattakalar benen ta sauka, babbar kofar fita daga gidan ya nufa tana biye da shi, bayan sun fito motar da Sapna ta dawo da ita daga aiki da ke ajiye a nan gaban gidan ya nufa ya buɗe driver seat, sai lokacin ya kalli Basma suka haɗa ido, da hannu ya yi mata alamar ta shiga cikin motan, ta kai hannu ta buɗe back door ta shiga, abun da bai ta6a faruwa ba a tsakanin su zama wuri daban daban a cikin mota, koda gaba ɗayan su ne za su fita har da mom dinta, ita ke zama a gaba don yawanci idan fitar da ta dangance su ce shine ke driving nasu, wani lokacin hannunsa guda a cikin nata, amman yau the reverse was the case.....