Sashe 128
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"So, kin san abu ne mara kyau kike aikatawa, kuma kin san hakan zai jefa mu a cikin damuwa, amman baki yi tunanin guje ma aikata hakan ba gudun halin da zamu shiga...wannan ne sakayyar mu daga gare ki Basma! Miye kika nema kika rasa? Mi ye bamu yi maki? Wani riba ne zaki samu da kika za6i wannan hanyan da zai lalata rayuwarki?.....Is this what happens when love is given too much? wataƙila mune muka ja hakan, saboda soyayyan da muke nuna maki, muna yi maki duk wani abun da kike so sakamakon ke kaɗai ce Allah Ya bamu...sai dai na san mu bamu ɗora ki hanyan da rayuwarki zata gur6ace ba, muna bakin kokarin mu wurin ɗaura ki a hanyan daidai tare da nuna maki abu mai kyau da mara kyau...ban san daga ina matsalan yake ba..." Ya ƙarasa maganar cikin raunanniyar murya tare da ɗan jinjina kansa, yayin da hannunsa da ya dunƙule ya ɗaura a saman bakinsa ke ƴar kakkarwa, kuka wiwi Basma ke ta faman yi tana bashi haƙuri, bayan ɗan lokaci ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da kai idonsa kanta ya ce, "Allah Ubangiji Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya jarabe mu ta wannan hanyan. Allah Ya bamu ikon cinye jarabawan, Ya kuma shirya mana ke." Sadda kanta ta yi ƙasa tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta, ce mata ya yi ta tashi ta tafi, ta ɗago ta kalle shi cikin muryar kuka ta ce, "Pls dad ka yafe ni....ba zan sake ba...I promise you." Shiru ya yi idonsa a kanta yana mata kallo mai nuni da alamar mamakin mutum, ita kuma ta kasa tsayar da idanunta kansa, juyar da kansa ya yi daga barin kallonta ya ce mata ta je za su yi magana later, ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi hanyar barin falon, juyo fuskarsa ya yi ya bita da kallo, zuciyarsa ta shiga dawo masa da hoton halin da ya riske ta, da sauri ya runtse idanunsa tare da kai hannu ya dafe goshinsa da ke wani irin sara masa tun faruwar abun. Misalin ƙarfe ukku saura Sapna ta shigo cikin gidan, tana sanye da riga da wando na wani silky yadi mai kyau kalar ruwan ƙasa da ya hau da fatarta sosai, kanta ta yi rolling gyale kalar kayan, hannunta tana riƙe da doguwar baƙar jacket sai yar babbar bakar jaka, mrs Helen ce ta fito ta tarbe ta da fara'a, bayan sun gaisa ta amshi jacket da jakan nata suka nufi shiga ciki, "Ko honey da baby sun dawo? Na kira wayan shi bai ɗauka ba." Sapna ta tambayi Helen da turanci yayin da suke tafiya cikin falon, amsa ta bata da eh sun dawo tun ɗazun, ta gyaɗa mata kai, part ɗinta ta ce ta kai mata kayan ita kuma kai tsaye ta nufi part ɗin Maleek dake nan ƙasa, ganin baya a nan ta fito ta nufi saman bene, tana shiga cikin falonsa ta ci karo da wayarsa dake ajiye a saman kujera, ta ɗan yi mamakin ganin wayan a nan ba tare da shi ba, sai kuma ta yi tunanin ko ya zauna a wurin ne ya shiga ciki yin wani uzurin, bedroom ɗinsa ta nufa tana shiga ta ja ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallon haɗaɗɗan gadonsa fuskarta da ɗan alamun razana, da sauri ta shiga cikin ɗakin ta nufi gadon muryarta da yanayin tashin hankali ta furta, "Honey! Mi yake faruwa..." Hannu ta kai da sauri bayan ta ƙarasa bakin gadon ta yaye lallausan farin bargon da ya lullube har kansa da shi, a hankali ya buɗe idanunsa da suka yi ja ya kalle ta, a ruɗe Sapna ta kai hannu ta ta6a fuskarsa, jin zafi a jikin nasa da sauri ta ce, "Honey what's wrong with you? Baka lafiya?" Kai ya ɗan ɗaga tare da lumshe ido, "But...why didn't you call me ka sanar mani?" Shiru ya ɗan yi yana kallonta, cike da ƙarfin hali ya ɗan yi murmushi ya ce, "Bana son in tayar maki da hankali ne..." Ta katse sa fuska a yamutse ta ce, "Haba honey...to miye amfani na?" Hannu ya ɗago ya shafa fuskarta ta sigar rarrashi ya ce, "Sorry..ba wani rashin lafiya bane sosai..." cire hannunsa ya yi daga fuskarta ya dafe kan shi ya ce, "Kai na yake mini ciwo sosai." Ya yi maganar yana ɗan nishi, "And you are running a temperature too." ta faɗa tana ƙara taba jikinsa, shiru ya yi yana kallonta, "Where is baby?" Ta tambaye shi ganin bata ga Basma ba a kusa da shi, ɗan janye idonsa ya yi bayan ya lumshe idanun ya bata amsa da suna tare shi ya ce mata ta je ta kwanta ganin ta tada hankalinta saboda rashin lafiyan da yake, ta jinjina masa kai alamar gamsuwa kafin ta tambayi ya ci abinci ya ce mata bai jin yana son cin komai, sumbatar bayan hannunsa ta yi ta ce dole ya daure ya ci abinci sai ya sha magani, bayan ta yi maganar ta miƙe tana faɗin bari ta je ta samo mashi abun da zai ɗan mashi daɗin ci, bin ta da kallo Maleek ya yi yayin da ta nufi ƙofa da sauri, wani irin tausayinta ne ya ratsa masa zuciya, ya runtse idanunsa yana mai jin inama abun da ya faru mafarki ne ba gaske ba. Tana fitowa 6angaren Basma ta nufa, har sai da gabanta ya ɗan faɗi bayan ta shiga ciki ganin itama Basmar a kwance ta lullu6e har kanta da duvet, da sauri ta nufe ta ta zauna a bakin gadon tare da kai hannu ta buɗe mata fuska, ta furta, "Baby...." Ɗan firgit Basma ta yi ta buɗe idanunta, tun bayan data baro 6angaren dad ɗinta itama zazza6i ya rufe ta, bayan ta sha uban kuka ne bacci ba mai nauyi ba ya ɗauke ta, "Baby are you okey?" Sapna ta tambaya da alamun tashin hankali, shiru Basma bata yi mata magana ba sai idanu da ta bita da su gabanta na bugu da ƙarfi, tsoronta kada a ce dad ya faɗa mata, duk da bata ga alamun ta san abun da ya faru ba a tattare da mom ɗin tata, hannu Sapna ta kai tana shafa fuskarta, ta san dama in dai dad ɗinta baya lafiya haka zata shiga damuwa, itama wani lokacin har ciwo take yi, hakan ya sa Sapna yin tunanin saboda ciwon Maleek ɗin ne itama ta shiga wannan yanayin, matsawa ta yi kusa da kanta ta ɗaura kan nata a saman jikinta ta shiga rarrashinta tana faɗin, "It's okey, zai samu lafiya dad ɗin naki, ki daina damuwa pls, kin ga kema har ciwo ya kama ki." Bin ta da kallo Basma ta yi da alamun razana jin maganar ta, ke nan dad ɗinta baya lafiya saboda abun da ya faru? ta faɗa a cikin ranta, "Ko nima kina son damuwa ya yi mani yawa saboda halin da kuke ciki har ciwo ya kama ni?" Sapna ta faɗa fuska a yamutse ganin Basma ɗin taƙi cewa komai, da sauri ta girgiza mata kai ta yi saurin kife fuskarta a jikin mom ɗin nata jin kuka ya taho mata, shafa sumarta da ke a tarwatse Sapna ta shiga yi tana ƙara rarrashinta, bayan ɗan lokaci ta ce mata bari ta je zata haɗa ma dad ɗinta abun da zai ci ya sha magani, tambayarta ta yi mi take son ci itama ta haɗa mata, ta girgiza mata kai alamar bata son komai, Sapna ta ce mata dole ta daure ta ci abinci sai itama ta sha magani, daga haka ta sauka daga saman gadon tana faɗin zata turo mrs Helen ta kawo mata abincin kafin ta gama haɗa ma dad ɗinta ta daure ta ci, tana fita Basma ta kife fuskarta a jikin pillow ta saki kuka, yau ita ce silarta dad ɗinta ya kwanta ciwo, abun sam bai mata daɗi ba, ta ji gaba ɗaya ta tsani kanta, a haka ma don mom dinta bata sani ba ita bata san wani irin hali zata shiga ba, amman tabbas ta san sai ta fi dad ɗinta shiga mawuyacin hali. Wunin ranar haka ta kasance ma Maleek da Basma ba daɗi, sa6anin yadda suke yin hutun ranakun ƙarshen sati cike da nishaɗi da annashuwa, ita kanta Sapna duk ta shiga damuwan halin da suke ciki, don ma Maleek nata ƙarfin halin nuna ya samu sauƙi saboda halin damuwan da Sapna ta shiga. Washe gari lahadi duk suna a gida, har sannan Maleek baya jin daɗin jikinsa daurewa kawai yake yana nuna ya samu lafiya, gaba ɗaya duk a ɗaki suka yi breakfast, tun jiya da abun ya faru tsakanin shi da Basma ba wanda ya sake fitowa daga part ɗinsa, sai Sapna ce ke ta faman kai kawo tsakanin parts ɗin su. Bayan sallar azahar lokacin Sapna tana a bedroom ɗin Maleek ta yi bacci, fitowa ya yi daga part ɗin sa jikinsa sanye da farar jallabiya, a wajen part ɗin ya tsaya idanunsa na kallon hanyar zuwa 6angaren Basma, a karon farko da ya ta6a jin shakkar zuwa 6angarenta, after a while ya sauke ƴar ajiyar zuciya ya fara tafiya a sanyaye ya nufi 6angaren nata, lokacin da ya kama hannun ƙofar har saida ya ɗan runtse idanunsa jin yadda fargaba ta kama sa ƙirjinsa nata bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarsa ta shiga dawo masa da abun da ya gani a ɗakin, da sauri ya saki handle ɗin kansa a ƙasa, bayan ɗan lokaci ya dake ya sake kai hannu ya tura ƙofar, tsaye ya yi a bakin kofar bayan ya shiga idanunsa a kan Basma dake kwance ta lullube jikinta, dama ba bacci take ba tana dai kwance kawai, jin kamar an shigo cikin ɗakin ya sa ta buɗe fuskarta, tana yin arba da wanda ke a tsaye, a razane ta yi saurin tashi zaune tana zazzare idanunta, kallon shi ta shiga yi da alamun tsoro akan fuskarta, ganin kallon da yake jifar ta da shi ya sa ta sauke idanunta ƙasa, gabaɗaya ta takure jikinta gabanta sai duka yake, cikin rashin ƙarfin jiki ya nufo cikin ɗakin, duk da bata kalle shi ba ta gane shigowa ya yi ta shiga ƙara zazzare idanunta, daga ɗan nesa