← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 197

Sashe 83

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

innarsu ya yi sai da ya ji dalilin da yasa Deen ke kiran Salma, gyale ta yafo saman doguwar rigan jikinta ta fito tana kallon Sagir da ke mata dariya irin ta ka raina ma mutum wayo, ya ce, "Ni wllh nama gode maki da kika bashi no ɗina, kin ga na rinƙa gaisawa da shi." Ƴar harara ta wurga mashi ta ce ai dai da ya koma ƙasar waje shike nan ba zai iya samun shi da layin ba, yana dariya ya ce mata matsalar shi da ita ƴar ƙauye ce waya ce mata ba ya iya amfani da layin a can, sai ta dawo ta yi ma innarsu ta ce mata to daga haka ta nufi kofar fita Sagir ya bi bayanta yana mata shegantaka kan alwashin da ya sha na kiranta yayar shi. Tun kafin ta ƙarasa gidan hajiya ta hango mutane dadda6e a bakin gate ɗin, bayan ta ƙarasa wani daga cikin jami'an dake tsaron gate ɗin ya dakatar da ita yana tambayar ta wurin wa zata je, tana niyyar bashi amsa wani jami'i da ya san ta tana zuwa gidan ya ce mashi ya bar ta ta wuce, tana shiga ta hango Deen daga can cikin parking space yana zaune a saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, daga gefensa wani jami'i ne a tsaye gefensa tarin kayan abinci ne masu yawa, wurin da yake ta nufa ganin yana cikin magana da wani dattijon mutumi dake zaune akan kujera ya ɗan rankwafa ya sa ta tsaya tana jira ya gama da shi, bata daɗe da zuwa ba mutumin ya miƙe hannunsa riƙe da kuɗi da Deen ya bashi muryar shi kamar zai yi kuka yake faɗin, "Allah Ubangiji Ya saka maka da gidan Aljanna Ya ƙara maka ɗaukaka, Allah Ya sa ka gama da iyayenka lafiya..." Haka ya yi ta jero addu'oi har muryarsa na karewa, kai Deen ke jinjina masa a hankali bakinsa ke motsawa alamar yana amsa addu'an, "Taho baba." Jami'in da ke tsaye ya faɗa, da sauri dattijon ya nufe shi kamar zai faɗi, kallon mutumin jami'in ya yi kafin ya ce, "Anya kuwa baba zaka iya ɗaukar kayan nan?" Da sauri dattijon ya ce to akwai yaron shi da suka zo tare ba a barsa ya shigo ba yana a bakin gate, sunan yaron jami'in ya tambaya ya bashi amsa, ɗaga murya jami'in ya yi yana faɗin, "Officer Kamal, allow one Sabi'u to come in..." Matashin yaron ne ya shigo ciki officer ya ɗaga murya ya ce mashi ya zo da sauri ya nufe su da sassarfa, madaidaicin buhun shinkafa da kwalin taliya da macaroni officer ɗin ya nuna masa ya ce su zai ɗauka, taimaka masa ya yi ya ɗaura masa shinkafar sai kwalin taliyar, dattijon ya ce a bashi ma macaronin, sai da yaron ya ɗan rankwafa ya yi ma Deen godiya kafin suka tafi farin ciki kwance akan fuskokinsu, kallon officer ɗin Deen ya yi ya ce a dakata da shigo da wani sai ya yi magana, ya amsa masa da ok tare da nufar bakin gate, kallon Salma dake tsaye ya yi suka haɗa idanu, ɗan murmushi ta shiga yi masa da hannu ya yi mata alamar ta ƙarasa, nuna mata kujera ya yi ta zauna, tana kallon shi a nutse ta ce, "Ina kwana." Ya ɗaga mata kai, shiru ta ɗan biyo baya, gently ta ji ya ce, "How can I help u?" Waro ido ta yi jin tambayar da ya yi mata, mamaki ya bayyana akan fuskarta a ranta ta fara kokonton ba shi ya kira ta ba? Ganin yana ta kallonta alamar ita yake jira ta yi magana ya sa ta fara kikkafta idanu ta ce, "Kai ka kira ni.." Shiru bai ce komai ba yana ta kallonta kawai ta shiga yan kame kame, ɗan murmushin da ta ga ya yi ya sa itama ta yi don ta gane wasa yake mata, "Baki je school ba?" Tana kallon shi ta ce, "Islamiyya?" Kai ya ɗaga mata, ta ce, "Ban yi haddar da aka bamu ba shi ya sa ban je ba." Ya ce, "Why baki yi ba?" Tana murmushi ta ce, "Saboda rasuwan da aka yi ban samu na zauna na yi ba, amman yanzu ma ina cikin yi ka kira ni." Nodding kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, hannu ya kai gefensa ya ɗauko wata ƙaramar bag ya ɗaura saman tabur ɗin da ke a tsakanin kujerun da suke zaune tare da tura ta gabanta ya ce, "It's ur phone, zamu rinƙa communicating da shi kada a takura ma brother ɗin ki, but ka da ki bari ya ɗauke maki hankali ki daina karatu." Murmushi ta yi ta maida idanunta kan ledan, kallon shi ta yi ta ce, "Na gode Allah Ya saka da alkhairi." Slowly ya amsa da Ameen, shiru ta ɗan ƙara biyo baya kafin ta ji ya ce, "Aikin da zaki yi ni ne zan rinƙa baki salary, tell me how much you want, and whether you want it to be weekly or monthly" Zaro ido ta yi jin tambayar da ya yi mata, a ranta take raya dama idan mutum zai yi aiki shi ake tambaya kuɗin da yake so a rinƙa biyan sa da kuma lokacin da yake so? Jin ta ƙi cewa komai ya ce ita yake sauraro yana son ya ci gaba da attending mutanen da ke waje, a daburce ta ɗan watsa hannu ta ce ai aikin ba wani aiki bane ya basshi ba sai ya rinƙa biyanta ba, ɗage mata gira ya yi ya ce dama ana yin aiki haka? Shiru ta yi kawai tana ɗan murmushi, gyara zaman shi ya yi ya ce mata idan ba zata rinƙa amsar salary ba a bar aikin, waro ido ta yi sai kuma ta ɗan marairaice fuska ta ce, "A'a yaya Deen zan yi tun da kana so." Ya ce ok yana jinta ta faɗi kuɗin da take so, ji ta yi duk ya ɗaure ta ta rasa ya zata ce, can ta ce bari ta je to ta tambayo innarsu, ya ce mata ai ita zata yi aikin kuma bashi da isasshen lokaci don gobe da safe zai tafi ga mutane na jiran shi, slowly ta ce, "Can ƙasar da kake?" Ya ce mata a'a zai koma Abuja after a week zai koma London, ta yi shiru tana kallon shi, ya ɗage mata gira alamar ita yake sauraro, sauke idonta ta yi ƙasa a cikin zuciyarta tana tunanin ita ya zata ce masa, can dai ta ɗago cike da jin nauyi ta ce, "Ka rinƙa bani dubu biyar." Shiru ya ɗan yi sai kuma ya tambaye ta weekly ko monthly, a sanyaye ta ce monthly wato duk ƙarshen wata, wani guntun murmushi ta ga ya yi ya ɗan juyar da fuskarsa, ta yi shiru tana kallon shi kamar mai son karantar yanayin fuskarsa, "Zan rinƙa baki 100k..." Tun kafin ya rufe baki ta wani zaro ido tare da kai hannunta guda ta rufe baki, idon shi akan ta ya ce ya yi mata ko a ƙara, da sauri ta janye hannunta ta hau girgiza masa kai cikin rawar murya ta ce, "S..sun yi yawa sosai gaskiya." Ya ce to haka yake son bata, marairaice mashi ta yi kan ita dai sun yi yawa, ganin ya ƙi amincewa ya rage kamar yadda take so sai kawai ta saka mashi kuka, mamaki sosai ya kama Deen ganin ta rufe idanunta da hannunta, shi bai ta6a ganin in da ake gudun kuɗi ba sai a kanta, ya ɗage gira ya ce, "Mi ye na kuka?" Janye hannunta ta yi ta kalle shi da idanunta da suka jiƙe cikin muryar kuka ta ce, "Kuɗin sun yi yawa wallahi, ko gida ma haka za a ce." Yana murmushi ya ce yanzu ya take son a yi, da sauri ta ce ya rinƙa bata kamar yadda ta ce, ɗan jimm ya yi kafin ya ce mata hakan ai ya yi kaɗan kuma monthly, ta ce to shike nan ya rinƙa bata dubu goma, ɗan murmushi kawai ya yi yana ci gaba da kallonta ta sauke idanunta ƙasa, tunanin ko ya rinƙa bata yadda hajiya ta ce da ya tambaye ta shawara wato dubu talatin, sai dai shi yana ganin sun yi kaɗan, sigh ya yi ya ce "Ok I will be giving you 50k, idan baki yarda da hakan ba a bar aikin kawai." Ɗago idanunta ta yi ta kalle shi, ganin yanayin fuskarsa ta nuna da gaske yake abun da ya faɗa ya sa bata ce komai ba, shiru na ɗan lokaci can ya ce mata idan tana da wani matsala ta faɗa mashi, ɗan girgiza masa kai ta yi ta ce bata da wata matsala, daga haka ya ce mata zata iya tafiya sai sun yi magana, godiya ta yi masa ya ɗaga mata kai ta ɗauki ledan wayan, har zata miƙe sai kuma ta dakata a sanyaye ta ce mashi goben da safe zai tafi, ya ɗaga mata kai sai kuma ya ce ko akwai wani abu, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a, ganin yana ta kallonta ya sa ta ce, "Dama na yi zaton ko bada sassafe zaka ta fi ba in soya maka fara, yanzu ba lalle har in yi ba zuwa dare." Murmushi ya yi ya ce, "Don't worry, na gode, wani lokacin idan na sake zuwa." Ta yi shiru tana kallonsa sai kuma ta ce, "Za ka sake zuwa?" Still da murmushi ya ce mata eh ai nan garin shi ne, ta ce, "Amman tun da na dawo nan ban ta6a ji ka zo ba." Tambayar ta ya yi daga ina ta dawo nan, ta ce, "A wurin auntyna Kaduna na yi primary school, bayan na gama na dawo nan yanzu shekara biyar." Kai ya jinjina mata ya ce shekaru ukku da ya zo kuma lokacin bai zo nan Funtua ba iyakar sa Abuja, ta ce, "Yanzu ma idan ka tafi sai an daɗe zaka ƙara zuwa?" Ya ɗan yi shiru idonsa akanta itama kallon nashi take duk da bata iya jure ma kallonsa cikin ido amman sai ta kasa janye idanun nata, slowly ya ce bai tunanin zai daɗe sosai kafin ya ƙara zuwa, kai ta
Chapter 83 · 0% Book details