Sashe 153
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne ba wani abu ba. Wama ya sani ko already kin riga kin ba wani daman hakan shiyasa ni kika ƙi amince mani don kada in sani in canza ra'ayina akan ki." Ɗan juya kai ta yi tare da yin murmushin takaici ta ce, "Allah shine shaida na ya Bash, wllh ni ban ta6a ba wani namiji damar koda riƙe mani hannu ne da son raina. Ni a gani na idan ka so ko nan da wata ɗaya ne zamu iya yin aure." Ɗan girgiza kai ya yi ya ce, "Ban shirya yin aure nan da wata ɗaya ba, a tsarina akwai abubuwan da sai na kammala su sannan ko zan yi aure, ciki har da ginina da zan fara." Fadeela ta ce, "Ni ya Bash na amince ko gidan haya ne ka kama mani, sannan koma lefe ba sai ka yi mani ba." Wani kallon kina da hankali ya jefa mata ya ce, "Allah Ya kyauta na zauna wai a gidan haya, ai hakan ma ƙasƙanci zai ja mani yadda mutane ke ɗauka na, ni a tsarina sabuwar amarya ƙerarran sabon gida nawa na kaina." Fadeela ta ce, "Ka ce sabuwar amarya, taya zan zama sabuwar amarya idan ka samu abun da kake buƙata daga gare ni." Wani ɗan iskan murmushi ya yi ya ce, "Ai wannan tsakani na da ke ne kawai, a wurin kowa ke sabuwar amarya ce, ko kina tunanin wai idan na samu abun da nike buƙata a wurin ki zan yi dumping naki ne?" A hankali ta ɗaga masa kai, ya ce "To kima daina wannan tunanin, don hakan sai ma ƙara mani son ki da zai yi saboda na san ke ɗin tawa ce ni kaɗai, kuma idan ma na guje ki ai kaina na yi mawa tunda ke matsayin ƙanwata ce, ko wani ya yi maki hakan to sai in da ƙarfi na ya ƙare wurin kwatar maki hakkin ki." Shiru ta yi tana kallon shi, kafe ta ya yi da wani mayen kallo, burinsa kawai ta amince masa don ba ƙaramar shawarta ya ke ba, kuma ita ce mace ta farko da ya sha wahalan samun hakan daga gare ta, ɗage mata gira ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce, "Kin amince?" Shiru ta yi tana ta kallon shi yayin da gaban ta ke bugu sosai, gaba ɗaya fargabar amsar da zata bashi take tsakanin amincewa ko akasin hakan, nasihar da ummanta ke yawan yi mata kan riƙe maraicinta da kula da mutuncinta ta shiga yi mata yawo a kai...hannu Bash ya kai ya kama hannunta yana bin ta da wani mayaudarin kallo, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Idan kin amince ko sau ɗaya ne na yarda." Shiru ta yi tana ta kallon farin hannunsa da ke riƙe da nata yayin da ƙirjinta yake ƙara tsananta bugu, "Zamu iya tafiya hotel yanzu?" Da sauri ta ɗago da manyan idanunta ta kalle shi, ganin duk tsoro ya bayyana a tare da ita ya ce, "Ki kwantar da hankalin ki, ba wanda zai san da hakan, akwai nose mask a mota sai ki saka yadda ba wanda zai ga fuskar ki." Nan ma shiru bata ce komai ba sai ido da take ta bin sa da shi, wani murmushi ya saki tare da miƙewa ya ce mata yana zuwa bari ya sallami Zee, har ya juya ya ji muryar ta ta ce, "Ya Bash...." Juyowa ya yi ya kalle ta, cikin rawar murya ta furta, "Ka...yi haƙuri...ba zan iya amincewa mu aikata hakan ba tare da mun yi aure ba." Wani ɗaure fuska ya yi yana jefa mata wani kallo da alamun 6acin rai, can ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce duk yadda ta so, fita ta yi daga cikin kujerar zata tafi, har ta juya ta ji ya ce, "Fadeela..." Dakatawa ta yi ta juyo ta kalle shi, a kausashe ya ce, "Daga yau na yanke alaƙar soyayyar da ke tsakanin mu, don na fahimci ƙaryar so na kike, kada ki sake bibiyana, idan ba haka ba komai na yi maki ke kika siya da kuɗin ki." Yana kai wa nan ya juya ya nufi komawa in da ya taso, tsaye ta yi a wurin tana ta kallon shi har ya haye cikin veranda ɗin, jiki a matuƙar sanyaye ta juya ta nufi hanyar fita daga wurin, yayin da maganganun da ya yi suke ta mata yawo a cikin kai, sosai take ta ƙoƙarin hana hawayen da suka taho mata zubowa saboda mutanen da ke a wurin, lokacin da ta kai bakin gate ɗin wurin ta ɗan dakata tare da juyowa tana kallo saitin da Bash ɗin yake duk da bata hango shi, tsaye ta yi tana sauraran 6angarori biyu na zuciyarta dake tafka muhawara, ɗaya na goyon bayan ta amince masa tun da ya ce ko sau ɗaya ne, yayin da ɗayan 6angaren ke hana ta aikata hakan ta hanyar nuna mata haramcin hakan da kuma tuna mata da nasihar mahaifiyarta a gare ta, ɗan lumshe ido ta yi hawayen da suka tarun mata suka zubo sharr, a sanyaye ta juya ta fita daga cikin wurin. Tun bayan da Fadeela ta hau keke napep lokaci lokaci take kai gefen gyalenta tana goge ƙwallan dake zubo mata, ta rasa ya zata yi da son Bash da ke ta azalzalar ta a zuciya, yanzu da abun nan ya faru a tsakanin su maimakon ta cire shi a ranta sai ma ta ji son nasa ƙaruwa yake a ranta, mai keke napep ɗin sai ɗan kallon ta yake ta cikin madubi, a ransa yake ayyana gata dai mace har mace amman Allah kaɗai ya san mike damunta, daga baya kuma ya raya yanzun hakan namiji ne silar damuwar tata tun da ya ga daga bakin in da ya ɗauko ta, a ransa ya ce shi da Allah zai bashi wannan a matsayin mata ai an gama masa komai, can dai ya kasa haƙuri ya ce, "Malama ban san ko zaki ga na yi maki katsalandan ba, amman don Allah ki yi haƙuri, ki fawwalawa Allah al'amuranki, dama A CIKIN RAYUWA mumini dole ne ya fuskanci jarabawa saboda Allah yana son sa, kuma idan kika ji damuwar wani zaki ga ke taki ba komai bace, babban arziƙin shine da Allah Ya barki da lafiya da hankali, sai ki yi amfani da hakan ki dage wurin roƙonsa ya yaye maki damuwar ki, ya baki ikon cin jarabawar da ya yi maki." Gefen gyalenta ta kai ta share hawayen ta, a sanyaye ta ce, "Na gode da shawara, in sha Allahu zan yi amfani da ita." Mai keke napep ɗin ya yi saurin cewa, "Ah ba komai, nine da godiya da kika fahimce ni har kika ɗauki shawara ta." Koda suka iso gida ta bashi kuɗin napep ɗin cewa ya yi ta bar su duk da nisan daga in da ya ɗauko ta, ƙarshe da ya ƙi amsa ta yi masa godiya ta nufi gida. Bayan kwanaki da tafiyar Maleek U.S, Basma na zaune a cikin ɗakinta, gaba ɗaya ji take duk ta takura, dama idan ta je makaranta ne take samu tana yin abun da ranta ke so, gashi yanzu sun samu hutu tun kafin dad ɗinta ya yi tafiya, kuma yanzu itama mom ɗinta tana saka mata ido sosai, can baya har tunani ta yi ko dai dad ɗinta ya faɗa mata abun da ya ta6a kama ta tana aikatawa, to amma da ya gaya mata zata gane ta sani, ta yi tunanin wataƙila wani abun daban ya faɗa mata shiyasa take saka mata ido, yanzu duk in da zata je mom ɗin ke sakawa a kaita a kuma maido ta, wani lokacin ma ita da kanta take kai ta, dama makaranta kai ta ake a ɗauko ta, mafi yawancin lokutta ma iyayen nata ne ke kai ta su ɗauko ta, gaba ɗaya duk shawaran da Maleek ya ba Sapna akan Basma can baya ta ɗauka, yanzu basu bata kuɗi sai da dalili, komai take buƙata siya mata ake yi kuma su tabbatar da ita ɗin ce ta yi amfani da abun. Gaba ɗaya tun lokacin da abubuwa suka canza mata take jin ta a matuƙar takure, har ta kai tana ɗaukar abubuwanta masu daraja tana zuwa da su school ta bada a saido mata. Yanzu da take zaune kokonton ko ta aikata abun da zuciyarta ke raya mata take, duk da tana jin tsananin son aiwatar da hakan amman bata san ta yaya ba don ba zuwa school zata yi ba, gashi ko da mom ɗinta bata nan baza ta iya fita ba, don ta saka dokar hana ta fita ba tare da izininta ba kuma da ta fita sai ta sani, a gefe guda kuma tana tuna jan kunnen da dad ɗinta ya yi mata kafin tafiyarsa, ta ɗauki lokaci tana ta saƙe-saƙe a rai, can ta ɗauko wayarta dake ajiye gefe ta ɗan yi jim tana kallon screen ɗin, ta6a wayar ta fara yi kafin a ɗarare ta kai ta kunne, magana ta fara yi da wata da ta kira da suna Lily, tambayar ta ta yi ta koma gida ko tana a gari, bayan ta bata amsa, Basma ta ce mata pls ko zata taimaka mata ta zo gidan su, ɗan saurarawa ta yi sai kuma da sauri ta ce mata ok zata bata kuɗin amman sai idan ta zo don bata da isassun kuɗi a account ɗinta sai dai cash, amman idan ta zo kada ta shigo ta gate ta tsaya ta baya sai ta kira ta, daga haka ta yanke kiran, ɗan jimm ta yi sai kuma ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita daga cikin ɗakin, kana ganinta ka san a tsorace ta ke ta nufi bakin bene ta tsaya tana kallo cikin falon ƙasa, ta san mom ɗinta ba yanzu zata dawo daga wurin aiki ba don bata ma daɗe sosai da tafiya ba lokacin duka ƙarfe goma da wasu mintuna na safiya, tunani ta shiga yi ko mrs Helen na a kitchen duk da tana ganin kamar lokacin da take yin girkin abincin rana bai yi ba, a hankali ta fara taka matakalar benen tana yi tana ƴan waige waige, ƙasa ta sauko ta nufi hanyar kitchen tana tafiya mai kaman