← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 197

Sashe 114

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

bata nuna ba sosai ta ce, "Sannu da zuwa ajiya." Tana ta latsa waya sai da ta gadama sannan ta ɗago kanta suka haɗa ido, "Ina matar gidan?" Ta tambaya a taƙaice, cikin girmamawa matashiyar ta ce mata tana part ɗinta lokacin baccin ta ne yanzu, wani kallo ta watsa mata jin abun da ta ce, cike da bada umarni ta ce, "Je ki taso man ita!" Tana niyyar juyawa ta nufi kujera ta ji matashiyar ta ce, "Sorry ajiya, ba a tada ta idan tana bacci." Cak baƙuwar ta dakata tare da juyowa ta ɗan ƙanƙance ido tana kallon matashiyar, ba tare da ta ankara ba ta ji ta ɗauke ta da wani wawan mari ta ce, "Ni kike faɗa ma haka don ubanki!" A gigice matashiyar ta saki ƙara tare da dafe kuncinta lokaci ɗaya jikinta ya fara yin rawa ta shiga ɗan ja da baya da gani marin ya shige ta sosai, ƙarar da chef Alima ta jiyo ya sa ta leƙowa cikin falon, tana hango su ta nufo ciki da sauri don ta ga alamun akwai matsala, tana ganin baƙuwar cike da girmamawa ta ce, "You are welcome hajiya." Maimakon ta amsa sai ta nuna matashiyar yarinyar ta ce wannan bata san ita wacece ba? Da sauri ta ce mata eh baƙuwa ce bata jima da fara aiki ba, kallon Alimar ta yi da ta ɗan russunar da kai gabanta duk da koda bata haife ta ba ta girme mata nesa ba kusa ba ta ce ta je ta tado mata matar gidan, ba musu ta ce mata to ta nufi hanyar part ɗin mom Jameela, duk da ta san ƙa'idarta ba a tada ta idan tana yin bacci amman ta za6i ta karya dokar tata akan ta karya ta baƙuwar don itama ta ta6a shan marinta, nufar kujera baƙuwar ta yi zata zauna hakan ya sa matashiyar juyawa zata wuce ciki har lokacin tana dafe da kuncinta ƙwalla na zubo mata, "Did I tell you to leave?!" Cikin yar tsawa baƙuwar ta yi magana, da sauri ta juyo murya na rawa ta ce, "Sorry hajia." Zama ta yi akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya fararen ƙafafunta suka bayyana saboda tsagar rigar da ke da tsawo. Saida Alima ta yi knocking kusan sau biyar a ƙofar ɗakin mom Jameela sannan ta jiyo muryarta daga ciki a ɗan fusace tana tambayar waye ne? Cikin ɗaga murya ta ce, "Hajiya it's me Alima, kin yi baƙuwa ne." wani uban tsoki ta buga daga ciki ta ce ma Alima ta shigo, tura ƙofar ta yi ta tsaya daga bakin kofa tana yan kame kame kamar munafuka, mom da ta ɗago da fuskarta ta ɗaure ta tamau ta ce, "Ban hana idan ina yin bacci ba a tashe ni ko waye ya zo?" Cikin yar rawar murya Alima ta ce, "Pls sorry ma, ki gafarce ni, dama sis naki ne ta zo and she insists sai an tado ki, har ta mari Rashidat da ta ce mata ba a tada ki idan kina bacci." Alamun mamaki ne ya bayyana akan fuskar mom ta maimaita sis ɗinta, da sauri Alima ta ɗaga mata kai, shiru ta ɗan yi kafin ta ce mata ta je gata nan zuwa, da sauri ta ce, "Thank you ma.." Ta juyo ta futo daga ɗakin a ranta tana gode ma Allah da na hajiya bai yi zafi ba, bayan ta dawo cikin falon daga gefen kujeran da baƙuwar ke zaune ta tsaya cikin girmamawa ta ce mata ta ce tana zuwa, baƙuwar ta ɗan ɗaga mata kai kawai ba tare da ta kalle ta ba, tsaye Alima ta yi tana gudun tafiya ta yi laifi, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan ta ɗan ɗaga mata hannu alamar ta je, godiya ta yi mata har za ta juya sai kuma ta dakata cikin ɗan rusunawa ta tambaye ta kalar lemun da za ta kawo mata don shima bata manta ba ta ta6a yi mata laifi akan lemun, kamar baza ta tanka ta ba tana ta pressing phone ɗinta, ƙasa ƙasa ta ji ta ce mata ta je idan tana buƙata za ta yi magana, Alima ta yi mata godiya kafin ta wuce tana ɗan yi ma Rashidat kallon tausayawa......
Chapter 114 · 0% Book details