← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 197

Sashe 87

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ce, "Maganar gaskiya aunty Kubra Deen ba zai iya son ta ba, mutumin da mata masu kyau da aji ƙarewa ma farar fata ke rububin shi mi zai ci da wannan." Ƙwafa aunty Kubra ta yi ta ce, "Ka rubuta ka ajiye wannan maganar da ka yi don ubanka, in sha Allahu akwai ranar tado ta don ma kada ka ce ka manta, ba dai za su kasance tare ba za ta yi masa aiki, bi'iznillah sai Allah Ya nuna maka ikonSa kuma wallhi sai ka rinƙa kiranta da yaya." Gaba ɗayansu dariya suke har da sauran ƴan gidan don a speaker aka saka kiran, bayan ta gama yin magana da shi ta ce ya ba Salma, bayan ta taya ta murna itama ta yi mata nasiha kamar yadda iyayenta suka yi mata, daga baya ta tambayi Salmar tana a ina ne ta ce mata tana a tsakar gida ta ce ta je ɗaki su yi magana, bayan ta sanar mata ta shigo ɗakinta aunty Kubra da ke akan waya ta ce, "Kina ji na baby, so nike mu ba wancan shegen Sagir ɗin kunya, don haka ki dage da gyara kan ki, ki rinƙa yin kwalliya na san wataƙil har video call za ku rinƙa yi, sannan ki kasance mai gaskiya da riƙon amana, ki tsare mutuncin ki, ki zamo mai natsuwa ba kamar yayin da kike magana da shi, kuma ki zamo mai kauda kai kada ki rinƙa nuna kwaɗayi ko haɗama duk da na san dama wannan ba halin ki bane, to kada ki sake ki koyi hakan ba kamar ganin kin samu dama, sannan ki zamo mai kunya don tana tasiri sosai a kan maza ba kamar shi da yake rayuwa a cikin waɗanda ba sa da kunya sai ki ga hakan ya zamo yana burge shi a tattare da ke...." Shiru Salma ta yi tana ta sauraran auntyn tata tana ɗan sakin dariya, ita duk abun da ake yi ta ɗauke sa wasa amman ita aunty Kubra ta dage tana son hakan ya zamo gaske wanda bata tunanin hakan abu ne da zai yuwu tana dai saurarenta ne kawai tana amsa mata. Washe gari wuraren karfe bakwai na safe Deen ya isa gidansu Fahad bayan ya yi sallama da hajiya da tuni ta fara jin kewar jikan nata, su ma gidansu Fahad bankwana ya yi masu duk aka rako su waje har da daddynsu da yaran gidan da basu kai ga tafiya school ba, tare da Fahad za su tafi shi zai kai shi Kaduna a can zai bi charter flight sai ya dawo Zaria wurin aikinsa, addu'oi da fatan alkhairi duk suka yi ma Deen yana ta murmushi yake amsa masu, a sabuwar motar shi za su tafi Fahad ne ya zauna a driver seat Deen yana a ɗayan side ɗin, yana ta ɗaga masu hannu da suma suke ɗago masa a haka motar ta bar gidan. Suna tafiya suna hira tsakanin su har suka iso Kaduna wurin karfe goma da wasu mintuna, kai tsaye airport suka nufa har wurin da zai hau jirgi Fahad ya sauke shi, duk a tunanin Fahad a nan Kaduna Deen zai bar motar a bishi da ita Abuja, bayan sun fito Deen ya miƙa mashi hannu yana murmushi ya yi masa bankwana, Fahad da shima murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Saduwar alkhairi bru. Allah Ya tsare, sai mun yi magana." Deen yana murmushi ya ce, "Thank you for everything ya Fahad, amman dai zamu sake haɗuwa before I leave for London?" Shiru Fahad ya ɗan yi haka nan bai son abun da zai sake kai shi Abuja gidansu, amman shima zai so ya sake ganawa da ɗan'uwan nasa kafin ya tafi don za a a iya ɗaukar lokaci bai sake ganinsa ba, amsa ya bashi da zai yi ƙoƙarin zuwa idan zai tafi, Deen ya yi mashi godiya tare da sake miƙa masa hannu suka yi musabaha, lokacin ya saka ma Fahad makullin motan, bayan ya zame hannunsa yana murmushi ya ce masa, "Dama motan taka ce, na ɗan yi amfani da ita ne kafin na tafi." Daga haka ya kai hannu ya kama suitcase ɗinsa da jaka ya nufi jirgin da ke a ɗan can gaban su, tsananin mamaki ya sa Fahad kasa cewa komai sai ido kawai da ya bi Deen da ke tafiya da shi, sai da zai shige cikin jirgin ya juyo tare da ɗaga ma Fahad hannu, jiki a matuƙar sanyaye Fahad shima ya ɗaga masa hannu daga haka ya shige. Fahad na driving bayan ya ɗauki hanyar komawa zaria, a cikin ransa mamakin kyautar motar kawai yake, ba wannan ne karo na farko da ya ta6a yi mashi kyauta mai girma ba, amman wannan ne karo na farko da ya yi mashi kyauta mai darajan da ta kai haka, Bai san wane irin so Deen ke mashi ba haka, yana driving yana ɗan murmushi wani lokacin ya ɗan girgiza kan sa yayin da yake tunawa da wasu abubuwan. Bayan Deen ya sauka Abuja daddynsa tare da ƙaninsa Omar suka je tarbo sa, sun nuna farin cikin dawowar shi daga baya suka nufo gida, yana shiga cikin falo suka yi ido huɗu da mom ɗin shi da ke saukowa daga bene jikinta sanye da doguwar riga ta ɗaura mayafin a saman kanta, daga bakin benen ta tsaya suka ƙarasa wurinta, fuskarta babu yabo babu fallasa take kallon Deen da ke mata murmushi, daddy ya ce, "Ga yaron ki ya dawo sai hankali ya kwanta ko." Ya yi maganar yana ƴar dariya, ta ɗan ta6e baki ta juyar da fuskarta gefe, Deen ya fahimci fushi take yi da shi daga yanayin fuskarta, dama ya yi zaton ganinta ta je tarbarsa a airport sai ya ga akasin haka, a hankali ya ce, "Mom, I'm back." Ya yi maganar da murmushi, ba tare da ta kalle shi ba ta ƙara ta6e baki a daƙile ta ce ai da ya koma tun da can ya za6a, shiru ya ɗan yi yana kallonta can ya juya tare da yi ma Omar dake riƙe da jakar shi alamar su je, "Deen ina za ka?" Dad din su ya tambaya da sauri ganin ya juya, dakatawa ya yi ya kalli dad ɗin a sanyaye ya ce, "Zan koma ne dad, since I'm not welcome here." Yana juyawa kafin ya ƙara step a fusace mom ɗin shi ta ce, "Don't you dare walk out of this house Deen! Idan ba haka ba wllh ranka sai ya 6aci." Juyowa ya yi ya kalle ta ta ɗaure fuska, da ɗan murmushi ya ce, "But, ke kika ce in koma ai." A faɗace ta ce, "To ka tafin who cares! Ai dama bamu da muhimmanci a wurin ka shi ya sa ka ɗauki ƙafa ka tafi just kwana ɗaya da dawowar ka, shekara nawa baka zo ba? Ka san yadda muke mararin ganin ka? Do you know how eager we are to sit and talk with you?" As your parents, we're ready mu baka dukkan lokacin mu, mu ji idan kana da problems mu yi ƙoƙarin ganin mun magance maka, idan kana buƙatan shawarwari mu baka, siblings ɗin ka suma a koda yaushe burin su ɗan'uwansu wanda ake ɗaukar lokaci basu gan shi ba ya dawo, ka basu lokaci ku yi hira, ku yi raha, ka ji matsalolin su, But unfortunately wasu ne daban suka samu dukkan wannan muhimmancin...you're free ka tafi, ka koma ka ci gaba da faranta ma wasu can bare Deen!" Tun da ta fara maganar idon shi na akanta yanayin fuskarsa ya nuna rashin jin daɗin maganganun da take furtawa, tana gama maganganun ta juya zata haye saman benen, da sauri Deen ya kamo hannunta, ta juyo a fusace ta ce, "Leave my han..." Bata ƙarasa ba ya jawo ta jikinsa ya tungume ta sosai, uwa daban ce ko da tana yin abun da rai bai so, sosai ransa bai ji daɗin 6acin ran da ya gani a tattare da ita ba, slowly ya ce, "I'm sorry mom, don Allah ki yi haƙuri, fushin ki akai na zai iya affecting nawa. It's not as you think mom, my family is always first, you are my number one priority....do forgive me pls." Ba ita da yake gaya ma maganganun ba hatta su dad da Omar sai da jikinsu ya yi sanyi da ganin abun da ke faruwa, sun ɗan ɗauki lokaci haka dukkan su kowa ya rufe ido, sai da ya tabbatar ta sauko sannan ya sake ta idanunsu cikin na juna, slowly ya ce, "Pls ki yi haƙuri, I realize my mistake and it won’t happen again In sha Allah." Ɗauke idonta ta yi ta koma tana kallon gefe tana ɗan far far da idanunta, juyowa ta yi ta kalle shi a tausashe ta ce, "It's Okay, ya wuce." Murmushi ya saki tare da furta, "Thank you my world." Ƴar harara ta sakar masa ta ɗan yi murmushi, su dad da Omar ma duk murmushin ne akan fuskokin su, Jameela ke nan, tana da matuƙar wuyar sha'ani, amman idan ta so wani lokacin tana da sauƙin sha'ani, haka dad ɗin su ke rayawa a cikin ransa, cikin falon suka koma duk suka zauna Omar ya wuce upstairs part din Deen don ya kai mashi kayan shi, hira suka shiga yi tun mom ɗin bata saki jiki ba har ta dawo ta saki jiki sosai, bayan ɗan lokaci dad ɗin su ya yi masu sallama zai koma wurin aiki dama daga can ya tafi tarbo Deen, abinci mom ta ce mashi gashi can an shirya a table su je ya ci, duk da ba wata yunwa yake ji ba haka ya miƙe gudun ya ce ba zai ci ba hakan ya zama wata matsala kuma, da kanta ta yi serving na shi bayan ta gama ta zauna shi kuma ya fara cin abincin a nutse, haka ta shiga jero masa ƙorafe-ƙorafe ciki har da maganar rashin zuwa Kano wurin su Amminta, bayan ya gama cin abincin ta so su zauna a falo su yi magana, ya nuna mata ya gaji yanzu yana son ya je ya huta ta yi haƙuri zuwa anjima zai bata isasshen lokaci su yi duk maganar da za su yi, jin haka ta amince ya
Chapter 87 · 0% Book details