Sashe 49
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Captain Junaid.." Ta bashi amsa, ya ce Allah Ya nuna masu ta amsa da Amin, ɗaga fork ɗin hannunsa ya yi kaman zai jeho mata ya ce ita bata da kunya ne, ta duƙe tana dariya ta ce shi ne za ta ji ma wani kunya. Bayan ya kammala yin breakfast ɗin ya ce ma Sadeeya yana son zuwa gidan hajiya ko akwai motan da zai yi amfani da shi, ta bashi amsa da akwai ya ce ok, kafin ya sake tambayarta dad na nan ya je su gaisa ta ce mashi eh, tare da ita suka nufi bangaren dad, bayan sun gaisa ne Sadeeya ta yi mashi maganar Deen yana son motan da zai je gidan hajiya, dad ya ce mashi ba zai jira zuwa anjima ba idan suka yi sallan juma'a sai ya tafi, Deen ya amsa mashi da to sai kuma dad ɗin ya ƙara cewa ko da yake ya san ba lalle zaman gidan ya yi masa daɗi ba tun da abokin nashi baya nan, makullin mota ya bashi Deen ya yi masa godiya, lokacin da zai miƙe har dad ɗin na tambayar wai zai iya tuƙin saboda titunan nan ba kamar na can ƙasar su ba, da murmushi ya ce masa eh lafiya lau ko jiya ma shi ya kawo su nan daga Zaria, dad ya yaba masa kan hakan duba da yana daɗewa bai yi tuƙi a nan ba. Bayan sun dawo cikin falon ya je ya yi ma mom sallama suka fito tare da Sadeeya ta rako shi har bakin mota ta ce ya gaishe mata da hajiya tana nan zuwa within the weekend yanzu don za su yi online group discussion da ta bi shi, tana tsaye har ya ja motar cikin ɗaga murya take faɗin, "Ka kula sosai my lil bru." Ya sakar mata horn tana dariya ta juyo ciki.
Hajiya zaune a falo ta yi gayun juma'a tana sanye da doguwar rigar shadda ruwan toka da aka yi ma aiki mai kyau, falon ma ya sha gyara sai ƙamshi ke tashi, jin sallama ya sa ta kai idanunta kan ƙofa, ganin Deen ta saki murmushi ya nufo ciki a nutse, a gefen ta saman kujera mai mazaunin mutum biyu da take kai ya zauna yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa, ta ce, "Ai ban yi zaton ganin ka ba yanzu, na yi tunanin sai zuwa bayan sallan juma'a." Kwantar da kansa ya yi jikin kujera ya ce mata haka nan ya taho ya zo ya ganta." Murmushin jin daɗin maganar ta yi ta ce to ta gode ga ta ya gan ta, tambayar ta tashi lafiya ya yi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah, tare da tambayar suma sun tashi lafiya ko,
"Ya iyayen naka da Æ´an'uwanka duk suna lafiya?" Ya bata amsa da lafiya lau, hajiya ta ce, "Sai suka ga ka yi masu zuwan bazata." Ya É—aga mata kai yana murmushi ya ce sun ji daÉ—in ganinsa sosai, hajiya ta jinjina kai tana murmushi.
"Za ka ci abinci a shirya maka ne?" Kai ya girgiza ya ce mata bai daɗe da ya yi breakfast ba sai dai zuwa anjima ta amsa da to, ya faɗi mata saƙon gaisuwar Sadeeya.
"Ai jiya da daddare ta kira ni suna son awara, na ma isar da saƙon nasu wurin mai yi, na san zuwa yanzu ma ƙilan ta kusa gama masu." Labarin yadda aka ci awaran jiya ya bata tana dariya ta ce, "Ahaf, dama ni na san sai an yi rikici kan awaran in dai suka gani, dama ita haka take abun marmari ce, ai gata nan za a yi masu har ta tiya ɗaya sai su ci su ƙoshi. Fahad yana wurin aiki ne?" Amsa ya bata da eh ta ɗaga kai, kafin ta sake cewa, "Ko kana son awaran a sake yi maka?" Hannu ya kai ya shafo sumar kansa da murmushi ya ce idan akwai yana so ya ji daɗin shi da ya ci ta jinjina kai, bayan ɗan lokaci ya miƙe ya ce zai shiga ciki, har ya fara tafiya ta dakatar da shi ta hanyar sanar da shi cewa ta saka an gyara mashi part ɗin shi na can 6angaren su ko zai yi amfani da shi, ya yi mata godiya kafin ya wuce, wayarta ta ɗauka ta kira layin Innar su Salma, bayan sun gaisa cikin girmamawa innar ta ce mata ai ga aikin awaran nan ana gaf da gamawa, hajiya ta ce to in an gama za su aiko daga can gidan a amsar masu, kafin ta sake cewa dama tana son wata ta rabin tiya ne idan za a samu, baƙonta ya ji daɗin ta jiya shi ne za a ƙara yi mashi, cikin fara'a Innar ta ce mata eh lafiya lau za a samu dama da ta sauke wannan za ta ɗaura wata, hajiya ta ce to shike nan ba sauri take ba ko zuwa yamma ne idan an gama a ba Salma ta kawo, ta amsa mata da to suka yi sallama.
Misalin ƙarfe ɗaya Fahad ya zo nan gidan hajiya dawowarsa ke nan daga aiki ya ɗauki Deen suka koma gidan su don su je sallar juma'a, bayan sun je Fahad ya ba Deen kayan da zai shirya wanda sabbabi ne a cikin leda ta brand din kayan, bayan ya saka kayan wanda shadda ce sky blue riga da wando da aka yi masu aiki kalan na ƴan gayu, tubarkallah sosai kayan suka amshe shi, shi ma Deen ɗin murmushi ya shiga saki yayin da yake kallon kan sa a madubi bayan ya gama saka kayan, shi ma Fahad shiryawa ya yi cikin shadda ruwan toka irin ɗinkin ɗaya da na Deen suma kayan sababbi ne tare ya siyo masu.
"Kayan ya yi kyau sosai." Deen ya faɗa yana gyara zaman hular da ya saka wadda take mahaɗin kayan ce itama sabuwa ce sai salƙi take, "When last ka saka kaya irin wannan?" Fahad ya tambaya yana ɗaura agogo a hannunsa, amsa Deen ya bashi da ba zai iya tunawa ba don an daɗe rabon da ya saka manyan kaya. Bayan sun gama shiryawa suka nufi ƙasa sai baza uban ƙamshi suke, idan ka gan su sun fito a zaratan samari tamkar ka sace su.
"Wow, ma sha Allah, ƙanina wannan wanka haka!" Sadeeya dake zaune cikin falo ta yi gayun juma'a da jan lace ta faɗa tana nufo su, "Yaya Deen ka yi kyau sosai!" Binafa ta faɗa tana washe baki, tambayarta ya yi da gaske ya yi kyau ta ce eh wllh, hannun Ayden ya kamo yana masa murmushi don jiya da ya zo basu haɗu ba ya yi bacci, yana ta kallon Deen ɗin don bai saba da shi ba sosai.
"Tubarkallah ma sha Allah, son ka ƙara matuƙar kyau cikin kayan nan." Mom ɗinsu Fahad ce ta yi maganar yayin da take nufo inda suke tana sanye da doguwar rigar shadda ta yi ɗauri mai kyau, godiya ya yi mata yana murmushi, haka sauran mazan da duk suma sun yi gayun juma'a duk suka yaba gayun Deen, dad ne ya shigo cikin falon ya sha manyan kayan farar shadda, nufo su ya yi yana tambayar su Sadeeq duk sun shirya ko don sun kusa makara, yana ganin Deen ya yi faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Ma sha Allah yarona, kayan nan sun matuƙar amsar ka. A can ma kana saka kaya irin wannan?" Amsa ya ba dad ɗin da yana da su amman yana daɗewa bai saka ba wannan ma Fahad ne ya kawo masa,
"Amma gaskiya sun yi maka kyau sosai, yakamata kana saka irin su ko a can don za ka burge mutane sosai." Godiya ya yi ma dad ya ce zai rinƙa sakawa in sha Allah, hoto Sadeeya ta ɗauke shi tana faɗin dole ta watsa wankan nan daga haka suka tafi masallaci.
Zaune take a saman tabarma cikin baranda tana cin abinci, bata daÉ—e da dawowa daga makaranta ba ta yi wanka tana sanye da riga da skirt na atamfa, daga gefen ta su Imrana ne suma suna cin abincin su basu daÉ—e da dawowa daga sallar juma'a ba duk suna sanye da yadi mai kyau kala É—aya, daga can saman tudun baranda yayansu Auwalu ne zaune shima yana cin abincin yana latsa waya,
"Ina zaka je?" Innar su ta ɗaga kai tana tambayar Sagir da ya shigo gidan ya nufi hanyar kicin yana sanye da wandon yadi ya cire rigar sai farar singlet. "Zan ɗan ƙaro abincin ne ban ƙoshi ba ni da su Aliyu muka ci."
"To ina ruwan wani da tare kuka ci, kowa kason shi aka zuba masa, saboda ma an san kafi kowa ci wanda aka zuba maka ya fi na kowa yawa kuma shine zaka zo ka kwashe sauran..." Salma bata ƙarasa ba ya nufo ta zai ƙwala mata cokali yana faɗin, "Ke wai uban mi yasa kika raina ni ne..." Da sauri ta 6oye a jikin innarsu, "Sagir kada ka sake ka buge ta, ai gaskiya ta faɗa, abincin da aka zuba maka ya fi na kowa, ba a hana ka ci da wasu ba, amman kuma ba zancen ka zo kai ta kwashe ma mutane abinci, idan kuma ya ƙare aka yi tuwo da daddare ka fi kowa yin tsegumin za a kashe ku da tuwo." Innar su ta faɗa da ɗan ɗaure fuska, ya ce, "Innarmu kaɗan zan ɗan ƙaro." Ya faɗa ya na nufar kicin,
"Kai dai ka sani, abinci dai har dare aka yi shi, idan ka kwashe ka nemi abun da zaka ci da dare, don ba wani abincin da za a ƙara dafawa." Bayan ya zubo abincin innarsu ta ce ya kawo ta gani, ya tsaya ɗan nesa da ita ya ɗan karkato mata da kulan yadda ba za ta gani ba sosai,
"Kam! wllh innarmu cuko ta ya yi." Imran ya faÉ—a, da sauri Sagir É—in ya fice yana dariya innar ta ce za su haÉ—e da dare ne. "Allah wanda ya rage mu za a zuba mawa da daddare ban da shi." Imrana ya faÉ—a yana tura abinci baki,
"Su Imrana mala'ikun tauna..." Salma ta faÉ—a tana dariya.