← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 197

Sashe 51

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Su kawun ka ma Hamida ɗazun sun zo nan suka ce sun ji labarin zuwan ka, na sanar da su kana can gidan baban naka. Yakamata ka samu lokaci ka kai ma ƴan'uwa na nan ziyara ku gaisa za su ji daɗin hakan sosai." Amsa mata ya yi da in sha Allah zai yi hakan. "Ko a shirya maka abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta sake cewa, "Ga awaran ma da ka ce kana so can Salma ta kawo Balaraba na haɗa maku." Kai idonsa ya yi kan Salma suka haɗa ido, sam ta kasa janye nata sai ƴan kame-kame da ta shiga yi tana kikkafta idanu. "Su suke yin shi ne?" Ya tambaya bayan ya maida idanunsa kan hajiya ta bashi amsa da eh, bai ce komai ba ya mayar da kallonsa kan waya, can ya miƙe ya nufi ciki Salma nata kallonsa, ita a wurin ta ganin shi da take yi hakan ba ƙaramar alfarma bace a wurinta, don in ba haka ba to ina zata samu damar ganin mutum mai kyau da ɗaukaka irin wannan? Ci gaba da kallon ta ta yi don ta san ko ta koma gida a lokacin ba wani abun da zata yi, dama ɗazun ƙarya ta yi ma innarsu cewa assignment take, kawai don bata son zuwa ne kada ta haɗu da Fahad, to ƙarshe ma sun haɗun ya nuna da ita da bola duk ɗaya.

Motsin da suka ji ya sa duk suka kai idanunsu kan Deen da ya dawo cikin falon, ya canza kaya zuwa ƙananu na shan iska riga mara hannuwa da wandonta gajere dukkan su kalar ruwan ƙasa mai haske da ta hau da fatarsa, kayan na ɗauke da tambarin Louis Vuitton, "Jama'a ku taya ni kallo, mi nake gani ne a saman kan Deeni?" Hajiya ta tambaya tana kallon saman kan nasa da mamaki akan fuskarta, wadda za ta bata amsa bata wuce Salma ba tun da su biyu ne kawai, sai dai itama gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan Deen ɗin da yanayin al'ajabi take kallon saman kan nasa, nufar kujeran da ya tashi ya yi ya zauna fuskarsa da ɗan murmushi don ya san abun da hajiyan ke ma mamaki, "Wai miye a kan ka Deeni kamar kitso?" Hajiya ta tambaya har lokacin da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta, ba don bata ta6a ganin kitso a kan nasa ba, ta san yana yi musamman idan suna ƙwallo, to amman mamakinta waye ya yi masa kitson yanzu? hannu ya kai ya shafi kan nasa ya bata amsa da kitso ne, ta ce, "Ikon Allah! Waye ya yi maka kitso cikin ɗaki? ko kuwa shima kitson an yo injin da ke yin sa ne tun da Bature dai ba zai gaji da kashe mu da abubuwan al'ajabi ba?" Murmushinsa ne ya ɗan faɗaɗa jin zancen hajiya, ya ce, "Nah, ni ne na yi shi." Ya yi maganar yana jingina kansa da kujeran, "Kana nufin yanzu kai ne ka zauna ka kitse kan ka haka?" Kai ya jinjina mata ya ce eh, kafin ya ɗaura da cewa zafi ya yi yawa a nan gashi ya saka manyan kaya sun ƙara masa zafin, hajiya ta ce, "To ai dama ka san yadda weather ɗin tamu a nan take, a haka ma da sauƙi tun da damuna ta fara don ma dai ruwan bai zauna ba sosai. To mi zai hana ka aske gashin kawai ko kuma ka rage shi sai ka fi samun sauƙin jin zafin a kai, idan sumar kake so sai ka bari idan ka koma ka ƙara tara wata tun da gashin bai maka wuyar taruwa." Shiru bai ce komai ba sai ɗan murmushi da yake yi, Salma dai ta kasa ɗauke idonta akan nasa, al'ajabi ne bayyane a saman fuskar tata don ita tun da take bata ta6a ganin namiji da kitso a zahiri ba sai yau, gashi abun da ya fi ɗaure mata kai shine jin cewa da ya yi shi ya yi ma kan sa kitson, dama akwai mazan da suka iya kitso? hakan take ayyanawa a ranta, ko Sagir da take roƙa wani lokacin ya taya ta tsifan kanta bai ta6a jaraba cewa zai yi mata kitso ba, jin bai ce komai ba bayan hajiya ta yi masa maganar aske sumar ya sa ta ƙara cewa, "Ko ba a ko ina kake yin aski ba? Balle garin namu ƙauye ko?" Tana rufe baki caraf Salma ta ce, "Ai akwai wani wurin aski mai kyau a can bakin tasha, ƴan gayu masu kuɗi nan suke zuwa aski, ko wannan ɗan film ɗin na nan garin na taba ganin shi a can an masa ask..." Kasa ƙarasa maganar da ta ɗauko ta yi sakamakon ido da Deen ya ɗago ya yi mata wani kallo mai kama da kallon ni tsaran wasan ki ne? hajiya da ta lura da abun da ke faruwa a tsakanin su ta sa dariya, dama maganar Salmar ta bata dariya, cikin dariyan ta ce ma Deen, "To kai shike nan ma ka ji Salma ta san inda ake ma irin ku celebrity aski sai ta raka ka a yi maka." Maida idonsa ya yi kan Tv ba tare da ya ce komai, itama Salma tun da ta yi maganar ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarta ke tsawatar mata kan ita ina ruwanta da shiga maganar su! sosai ta ji rashin daɗin su6utar bakin da ta yi masu, kunya duk ta lullu6e ta tana jin kaman ta nutse a wurin, bayan ɗan lokaci da ƙyar ta miƙe hajiya ta kalle ta ta ce ina zata je, cikin ƴar rawar murya ta bata amsa da gida za ta tafi, hajiya na murmushi ta ce, "Kina yin kallon ki muna hira, ki zaman ki." Shiru ta yi tana ɗan wasa da yatsun ta,

"Deeni ka ga zaka korar mini baƙuwa." Kamar ba zai ce wani abu ba, slowly ya juyo idanunsa ya kalli Salma, janye idonsa ya yi ya mayar kan Tv tare da faɗin, "Ban kore ta ba. If I want to cut my hair, I have a clipper (Idan ina son aske gashina ina da abun yin askin)" Hajiya dake murmushi ta ce mata, "To kin ji, shi ba ruwan shi da ke ki zaman ki." A hankali ta ɗago kai ta kalle sa, daidai lokacin ya maido nasa kanta idanunsu suka haɗu, kawai sai gani ta yi ya ɗage mata gira tare da ɗan jinjina kansa alamar ta ji abun da ya ce? ɗan kikkafta idanu ta shiga yi tare da tsuke baki ta jinjina masa kanta alamar eh, ya kauda idanunsa daga barin kallonta, komawa ta yi ta zauna amman duk da haka ta kasa sakin jiki, after some few minutes ta sake miƙewa hajiya ta kalle ta, tun kafin ta ce wani abun Salma ta riga ta cewa, "Zan je in shirya ne, anjima zan fara tuyan awara." Da alamun rashin fahimta hajiya ta ce, "Dama ke kike tuyar awaran?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, ta sake tambayar ta anan cikin gidan su? ta bata amsa da a ƙofar gida.

"Amman ba kina da ƙannai ba?" ta ce mata eh amman duk maza ne, tambayarta ta yi maza basu tuyar awaran ne, tana ɗan murmushi tare da wasa da yatsunta ta ce suna yi kawai dai ita ce ke son tana yi, hajiya ta ce, "Amman Salma baki gudun samarinki su gan ki kina tuyar awara?" Still da murmushi ta ce ai ita bata da saurayi, kallon ban yarda da abun da kika faɗa ba hajiya ta yi mata, "Ya za ai budurwa kamar ke, ga ki kuma tubarkallah ki ce mani baki da saurayi Salma?" Ƴar dariya ta yi kanta a ƙasa ta ce ai ita ce bata saurarar su,

"To saboda me?" hajiya ta tambaya tana kallonta da ɗan murmushi, cikin yar en-ina Salma ta ce, "I...idan na gama makaranta so nike in ci gaba da karatu shi ya sa." Kai hajiya ta jinjina alamar gamsuwa kafin ta ce, "Duk da haka dai idan akwai wanda ya zo da magana ta kirki mai nagarta, kuma kin ga ya yi maki yakamata ki saurare shi, saboda karatu baya hana ai a saurari saurayi, kuma ko da mace tana cikin karatunta zata iya yin aurenta ta ƙarasa a ɗakin mijinta. Ita mace akwai lokacin da zaki ga tauraruwarta ta haska samari sun yi mata caa har da masu son aurenta, to ya kamata ta yi amfani da damarta don wani lokacin in ta ce sai lokacin da ta shirya sannan sai ki ga samarin ɗibb babu su, duk da dai dama komai ya faru da bawa rubutacce ne. A dage a rinƙa yin addu'ar neman za6in Allah." Cikin muryarta mai tattare da natsuwa ta amsa da in sha Allahu.
Chapter 51 · 0% Book details