← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 197

Sashe 18

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shima Deen murmushin yake na jin daɗin yabon da ministan ke yi masa, yayin da mutane suka ƙara saka tafi, cikin natsuwa yake ɗaga ma mutane hannu alamar ya ji daɗin tafin da suke masa. Bayan ministan ya gama jawabin nashi mai girma mataimakin shugaban ƙasa shima ya yi wanda yabo ne da kalaman ƙarfafa guiwa ya yi ma Deen, haka wasu a cikin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa suma suka yi nasu jawabin wanda yabo ne akan irin ƙoƙari da jajircewar Deen a harkar ƙwallo da kuma yadda yake saka ƙasa alfahari. Bayan gama duk jawabe-jawaben aka fara ciye-ciyen abinci da abubuwan makulashe, daga can bangare guda na cikin ɗakin anan aka jere iyayen kayan abinci da masu aikin zubawa da rarraba ma mutane jikinsu sanye da uniform, sai abun da mutum ke so za a kawo mashi a cikin abubuwan cin abinci da kofuna na ƙawa sai walainiya suke, kowa saida aka zuba mashi duk abun da yake so duk da haka masu aikin raba abincin nata zagayawa suna tambayar mutane ko akwai abunda suke so akawo masu, iyayen Deen na daga can gaba daga bayan inda su Deen suke a zaune, Fahad da Leemarh da Omar suna a wuri guda gefe da su mom ɗinsu, an natsu ana ta ciye-ciye baka jin ƙarar komai sai ta cokulla dake haɗuwa da plate ɗin ƙarau, kowane tebur bayan kayan abinci an ajiye masu kwalin tissue mai kyau don goge hannu da baki, kowa ka gani fuskarsa cike da annashuwa wasu suna ci suna ɗan yin hira, kamar Fahad da Leemarh suma suna cin abincin suna ɗan ta6a hira, suna haka ta ɗan debo ta kai bakin shi yana murmushi ya buɗe baki ya amsa, itama ya ɗebo ya kai bakinta hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba dama saboda tana son ya bata a bakin yasa ta fara bashi, duk abun da suke mom ɗinsu na kallo baƙin ciki ya turnuke ta kamar ta je ta shaƙe Fahad take ji, gaba ɗaya fuskarta ba walwala ta haɗe rai, lura da yanayinta da ya canza da kuma saitin da take yawan kallo ya sa dad shima ya juya ya kalli wurin su Fahad ya ga yadda suke ba juna abinci duk da a lokacin shi har da Omar ya ga Leemarh ɗin ta ba abincin a baki hakan ne ya sa shi bai fahimci miye dalilin da ya sa mom ɗin daure fuska haka ba.
Bayan an yi nisa da fara cin abinci wasu ma har sun gama ci don abu ne na ƴan gayu da yawa ba wani sakin baki suke su yi ta cin abinci ba, wasu abu kaɗan suke tsakura shike nan sun ƙoshi tun da dama an saba cin mai dadi sa6anin talaka bawan Allah wani abincin sai dai ya gan shi a hoto sai kuma idan Allah Ya ci da shi ya tsinci kansa a hidima irin ta masu hannu da shuni ya samu ya ci. Kwatsam! mutane suka ga hasken cikin ɗakin ya ɗauke, har hayaniyar mutane ta ɗan fara karaɗe cikin ɗakin ana tambayar abun da ya faru suka ga an kunna wasu ƙananun fitulu ba masu haske ba sosai a can sama, basu gama mamakin dalilin ɗauke ainihin hasken wurin ba suka ga wani hasken mai yawa ya fara bayyana daga can sama yake saukowa ta gaban ɗakin taron inda mutum ke hawa in zai yi bayani ko za a nuna ma mutane wani abu ko bada kyauta, lokaci guda suka fahimci screen ne da alama wani abun za a haska mutane su kalla kamar dai a cinema, fahimtar abun da ke faruwa yasa hankalin mutane ya kwanta kowa ya natsu yana jira ya ga abun da za a haska, wani mutum ne da alama m.c ne ya fara magana ta cikin lasifika ya ba mutane hakuri kan rashin sanar masu abun da za a yi ya ce hakan cikin bazata ne, nan ya sanar dasu cewa za a haska wasu daga cikin performance ɗin Deen ne a fagen ƙwallo, gaba daya ɗakin aka saka tafi raf, raf, raf murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskokinsu. Wasu daga cikin manyan gasannin ƙwallo da ya buga kuma ya yi nasara aka shiga haskawa, nan fa ɗakin ya karaɗe da tafi da sowar mutane, tamkar a lokacin ake buga ƙwallon, idan ya ci haka zaka ji wasu sun saka ihu suna faɗin, 'Goallllll!' gaba ɗaya wurin sai ya koma kamar stadium kamar a nan take ake buga ƙwallon ba haskawa ake ba, kowa idonsa na akan screen, tuni masu cin abinci sun daina hankulansu sun koma can, shima Deen idonsa na akan screen yana kallo yana ta sakin faffadan murmushin jin dadin irin yadda mutane ke ta faɗin kalaman yabo kan yadda ya iya ƙwallo, wasu daga cikin matan dake wurin musamman ƴan mata ba wai yadda yake yin ƙwallon bane ke burge su don wasu ma ba masoya kwallon bane kawai shi Deen ɗin ne yake burge su, tun bayan fara taron wasu cikin yan matan dake a wurin idanunsu na akan duk wani motsin shi, hatta iyaye mata da wasu da yawa daga cikin mazan duk burge su Deen yake yi.

Bayan an gama kallon perfomance din sa sai kuma aka shiga haska mabambantan lokutta da aka bashi kyaututtuka a harkar kwallon, daga karshe aka yi replaying wuraren da ya ci ƙwallo daban-daban in slow-motion, gaba ɗaya ɗakin ya ƙara harmutsewa da hayaniyar murna, ba kamar ƙwallon ƙarshe da ya ci a extra time a gasar cin kofin zakarun nahiyar africa wato AFCON wadda ita ce ta saka Nigeria yin nasara.

Bayan an gama haskawa, hasken ɗakin ya dawo lokacin Deen din ya mike smiling humbly, sauran mahalarta taron ma duk suka miƙe suna mashi tafi fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki, manyan mutane dake a kusa da shi suka shiga shaking hand da shi wasu suna patting bayan shi suna taya shi murna da kuma fatan alkhairi a harkar shi ta ƙwallo. Daga baya minister da sauran football officials suka karrama shi ta hanyar bashi lambar yabo tare da yi mashi godiya kan irin gudunmawar da yake ba harkar wasanni a Nigeria.
Chapter 18 · 0% Book details