← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 197

Sashe 69

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

hajiya ta ce uhmm ta dai faɗa ne kawai, duk yadda Balaraba ta yi da Salma taƙi ta amshi dubu ɗayan, sai da hajiya ta saka baki ta ce ta amsa to kuɗin ta Balaraba da kuma nata, Salma tana dariya ta ce, "To ai hajiya na ki alakoro ne kowa na kawo masa" hajiya ta ce, "Ai duk da haka na san tawan ta fi ta ɗari biyar kuma ga Deeni ma an basa, kin ga dai duk da haka kin bamu alakoron." Da ƙyar ta amsa dubu ɗayan ta yi ma aunty Balaraba godiya, wayar Deen ce ta fara yin ƙara alamar ana kira, tissue ya ciro a cikin tissue box ya goge hannunsa sosai kafin ya ɗauki wayan ya kai kunne, a taƙaice ya ba mai kiran nasa amsa da zai fito yanzu daga haka ya katse kiran, miƙewa ya yi hannunsa riƙe da robar sauran farar ya nufi shiga ciki, hajiya na tsokanarsa tana cewa ya kawo ta ajiye masa ya yi murmushi kawai, bayan ya koma bedroom ɗinsa toilet ya shiga ya wanke hannuwansa da bakinsa ya fito ya saka kaya, lokacin da ya fito idon hajiya a kansa ganin crazy jeans ɗin da ya saka ta ce, "Kai jama'a! Mutum ya ɗauki kuɗi da hannunsa ya siya kaya bana kirki ba da sunan gayu." Yana zuwa saitin ta ya kai hannu ya ɗan ja kumatunta ya ce mata kuɗin wandon zai siya gadonta, ƴar harara ta wurga masa ta ce ya san nawa gadonta yake da zai haɗa shi da yagaggen wando, ɗage mata gira ya yi ya ce tana zaune a ƙauye bata san gayu ba daga haka ya nufi hanyar fita yana murmushi, Salma dake ta bin sa da ido murmushi ne akan fuskarta a ranta tana ayyana ashe yana magana haka.....
Chapter 69 · 0% Book details