← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 197

Sashe 74

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da su Salma suka iso, wasu a cikin mutanen gidan su Habu na a waje suna dakon isowar su, keke napep ɗin na tsayawa shima baban su Habu ya ƙaraso hakan ya sa iyalan nashi nufo su, fitowa innarsu Habu ta yi idanunta cike da ƙwalla, bayan baban su Habu ya sauko daga saman mashin ɗinsa ya nufi 6angaren da Salma take, cikin kwantar da murya yake rarrashinta ya ruƙo ta ta fito, su Sagir da abokansa dake zaune daga can gaban wani gida dake kallon nasu suka taso zuwa wurin su, Salma na ganin Sagir sautin kukanta ya ƙaru, fuskarsa da alhini ya kamo ta ya rungume ta ta gefe yana rarrashinta ya nufi gida da ita, suna shiga cikin zaure daidai da fitowar innarsu tana gyara hijab, dakatawa ta yi tun kafin ta ce wani abu Salma ta nufe ta da sauri ta faɗa jikinta tare da fashewa da matsanancin kuka tana faɗin Habu ya rasu dama bata kai shi asibitin ba, kama ta innar tasu ta yi suka shiga cikin gida ta nufi ɗakinta da ita, bayan ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna tare da rungumo ta jikinta ta shiga rarrashin ta tana kwantar mata da hankali. Ba'a ɗauki lokaci ba aka gama shirya Habu, a nan kofar gida aka yi masa salla har da su Sagir da baban su da ya dawo don halartar jana'izar, lokacin da aka gama sallar Hamza ya ruga cikin gida ya nufi ɗakin innarsu, Salma na kwance ta duƙunƙune a saman gado har lokacin kuka take ta yi, Hamza ya ce mata gashi can za a tafi a rufo Habu, tana jin hakan ta miƙe idanuwanta duk sun kumbura ta nufi hanyar waje, a cikin zaure ta tsaya tana leƙe yayin da take ci gaba da kuka ƙasa-ƙasa, tana ganin lokacin da aka wuce da shi ta duƙe nan wurin ta saka kanta a cikin gwiwuwinta ta shiga raira wani sabon kukan. Bayan sallar magrib duk suna zaune a cikin baranda, Salma na kwance a saman tabarma ta tada kanta a saman cinyar innarsu, babansu na daga gefe saman darduma sai Sagir da Auwalu na zaune a saman tudunkar baranda, basu jima da dawowa daga rufo Habu ba aka yi sallar magrib, bayan gama sallar ne duk suka shigo gida, gaba ɗaya jimamin rasuwar yaron suke, sauke ajiyar zuciya babansu ya yi ya ce, "Haka rayuwar take, dukkan mai rai mamaci ne, kowa da lokacin sa ya yi to ba makawa sai ya tafi ba tare da an ƙara ma mutum ko da sakan ba, shi yasa ake son mutum ya zauna a cikin shiri kuma ya kasance mai aikata aikin alkhairi sannan ka zauna da kowa lafiya. Yaron nan ina tunanin bai fi shekaranjiya ba da na je wurin mahaifinsa na gansa, yau gashi babu shi." Girgiza kai innarsu ta yi cike da jimami ta ce ko ranar juma'a ya shigo nan har aka bashi abinci ya je su ci da ƴan'uwansa ashe ƙarshen shigowar shi gidan ke nan, jin maganar innar tasu ya sa Salma fara yin kuka ƙasa-ƙasa, haƙuri iyayensu suka shiga bata, "Imrana yanzu hankalinka sai ya kwanta ko? Habu ba zai ƙara shigo maku gida ba har ya ci maku abinci." Sagir ya faɗa yana jifar Imrana da harara da yake akwai hasken kwai mai caji wurin ya yi fayau, duru duru Imrana ya yi ya kasa cewa komai, dama tun da ya ji Habu ya rasu duk jikinsa ya yi sanyi laƙwas, jin maganar Sagir babansu ya tambaye shi mi ya sa ya faɗi haka, nan ya kwashe yadda Imrana ke kyarar yaron saboda abinci ya faɗa masa, sam baban nasu bai ji daɗin maganar ba nan ya shiga yi ma Imrana nasiha kan ya rinƙa ɗaukar komai ba komai ba ya nuna masa duk abun da mutum ya bada shike da riba musamman ciyar da wanda ke jin yunwa ba ƙaramar falala hakan yake da, da alamu nasihar ta shiga Imrana sosai har da kuka ya yi tare da yi ma babansu alƙawarin ba zai sake ba, kiran sallar isha'i da aka fara ya sa duk suka miƙe, wurin Salma baban nasu ya nufa ya ɗan duƙa yana kallon ta ya ce, "Ki yi haƙuri mamana, ki daina saka damuwa a ranki, komai kika ga ya faru to dama can rubutacce ne, ko baki kai shi asibiti ba dama Allah Ya rubuta a yau zai bar duniya, abun da kika yi mai kyau ne kuma kina da lada, kada hakan ya sa ki sare ki ci gaba da taimakon duk wanda yake a hali kuma kika ga kina da ikon taimaka mashi." Kai Salma ta ɗaga ma mahaifinta tana kallon shi idanuwanta cike da ƙwalla, ya ce, "Yauwa mamana, pls ki cire komai a ranki kada damuwa ta sa ki kamu da ciwo, mu yi masa addu'a ita ce yake buƙata a yanzu, duk da muna kyautata masa zaton ya huta tun da yaro ne." Nan ma kai ta ɗaga masa, innarsu ta ce ai yanzu haka ma akwai zazza6i a jikinta kuma ta san bata rasa ciwon kai saboda kuka, miƙewa baban ya yi yana tambayar ta bata magani ta ce masa eh bayan ta dawo daga gidan gaisuwar ta bata, nufar hanyar fita ya yi yana faɗin In sha Allahu zata warware damuwa ce, daga haka suka tafi masallaci shi da duka yaran maza. Bayan Salma ta yi sallar isha ita da innarsu, a nan cikin barandar ta sake kwanciya innarsu kuma ta wuce kicin don ta ɗumama mata ruwa ta yi wanka, ita ta haɗa mata ruwa ta zo ta kama ta ta kai ta har banɗakin, bayan ta yo wankan ta saka wata doguwar riga tare da hula, sosai ta ji daɗin jikinta don dama tun wankan safe da zata tafi makaranta bayan ta dawo bata samu yin wani ba ta tafi kai Habu asibiti. Bayan mazan sun dawo daga salla anan cikin barandar suka zauna cin abinci, babansu bai shigo ba yana can wurin zaman gaisuwan, shi kuma Sagir ɗaukan nashi ya yi ya fita ƙofar gida, Auwalu nan ya zaune inda ya saba zama yana cin abincin yana latsa waya as usual, saida innarsu ta lalla6a Salma sannan ta ɗan ci abincin don da ta ce baza ta ci ba, "Yaya Salma na manta ɗazun da na kai ma hajiya awara ta tambaye ki, shi ne na faɗa mata kin tafi kai Habu asibiti ta ce idan kin dawo in ce maki ki je." Imrana da duk ya yi sukuku ko abincin ya kasa sakin jiki ya ci ya faɗa yana kallon Salma dake zaune ta jingina da bango, shiru ta yi bata ce komai ba innarsu dake kallonta ta ce, "To wannan anya ma kya iya zuwa, bari Imranan idan ya gama cin abincin ya je ya sanar mata baki jin daɗi don kada ta ji shiru." Ɗan girgiza kai Salma ta yi a sanyaye ta ce mata bari ta je, innar tasu ta ce zata iya ta amsa mata da eh, miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta walking slowly, ƴar madaidaiciyar hijab ta ɗauro a saman rigar jikinta, bayan ta fito ta ce ma innarsu sai ta dawo, ta amsa mata da to sai kuma ta ce ko ta jira Imrana ya ƙarasa sai ya rakata, ta ce a'a bari ta je kawai dare na yi daga haka ta nufi ƙofa ta fita. Da sallama ta shiga cikin falon hajiya, yau ma Deen ne kadai zaune yana playing PS ya saka headphones jikinsa yana sanye da kayan shan iska riga armless da wandonta, yau ta ci sa'a tana shiga ya juyo ya kalle ta, kanta a ƙasa ta ƙarasa cikin falon ta tsaya ɗan nesa da shi daga gefe, gaishe shi ta yi da alama ya ji ba tare da ya cire headphones ɗin ba ya ɗaga mata kai, daga haka ta maida kanta ƙasa, motsin da ta ji ya sa ta ɗagowa ta ga ya kai hannu ya ɗauki wayarsa, kira ya yi ya kai kunne ta ji ya ce an zo wurinta hakan ya sa ta gane hajiya ya kira, after few seconds ya juyo yana niyyar ce mata ta zauna sai ga hajiya ta fito hakan ya sa shi fasa yin magana ya juya ya ci gaba da abun da yake yi, nufo cikin falon hajiya ta yi fuskarta a sake bayan ta ƙaraso ta ce, "Salma.." A hankali ta amsa mata tare da gaishe da ita idanunta a ƙasa, zama hajiya ta yi tana kallonta ta ce, "Ki zauna, kun dawo daga asibitin ke nan, ɗazun ɗan'uwanki da ya kawo awara ke faɗa mani kin tafi kai yaron makwabtan ku da bai lafiya asibiti, shine na ce idan kin dawo ya ce ki zo don ina son sanin halin da yaron yake ciki. To ya jikin yaron?" Kamar jira take ta tambaye ta game da jikin shi kawai sai gani hajiya ta yi ta fashe da kuka mai sauti, salati hajiya ta saka ta shiga tambayar ta lafiya miya faru ne, kukan da Salma take yi da maganganun hajiya su suka janyo attention ɗin Deen ya dawo kan su, kallon Salma dake a tsaye tana kuka ta rufe fuskarta da gefen hijab ya shiga yi ba tare da ya ce komai ba, miƙewa hajiya ta yi ta kamo hannun Salma guda tana tambayarta mi ya faru ne, cikin kuka Salma ta faɗa mata yaron ya rasu, dogon salati hajiya ta saka ta juya ta kalli Deen da idonsa ke akan su ta ce masa ya ji yaron da aka ce ta tafi kaiwa asibiti ɗazun ya rasu, ɗan buɗa ido ya yi hajiya ta jawo Salma jikinta tana rarrashinta tana cewa, "Ki yi haƙuri Salma, dukkan mai rai dama mamaci ne, lokacinsa ne ya yi. Allah Ya jiƙansa." Cikin kuka Salma ta ce dama bata kai shi asibitin ba...ɗan murmushi hajiya ta yi jin maganar da Salmar ta yi wadda ke bayyana yarintarta, kallon Deen hajiya ta yi still da murmushi akan fuskarta ta ce masa wai ita gani take har da kai shi asibitin da ta yi ne ya sa yaron ya mutu, shi ma ɗan murmushi ya yi kawai, zama hajiya ta yi da Salmar
Chapter 74 · 0% Book details