Sashe 154
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
sanɗa, lokacin da ta ƙarasa bakin kitchen ɗin ta leƙa bata ga kowa ba a ciki, juyowa ta yi tana kallon hanyar da ɗakin mrs Helen yake, nufar ɗakin ta yi tana ci gaba da yin ƴan waige-waige, daga bakin ƙofar ta tsaya ta yi ɗan jim tana saurarawa, kafin ta kai hannu a hankali ta kama handle ɗin cikin sa'a ƙofar a buɗe take, a hankali ta ɗan tura ƙofar ta kai idonta tana leƙa ciki, hango mrs Helen ɗin ta yi a saman madaidaicin gadon ɗakin wanda yake matsayin nata tana yin bacci, wani daɗi Basma ta ji, sakin ƙofar ta yi ta juya da sauri ta koma kitchen, wani ɗan dogon stool ta ɗauko tare da floor wiper ta fito ta nufi hanyar da zata kai ta bayan gidan, a ƙofar shigowa ta baya akwai Cctv Camera haka ta gaban gidan ma, dama iya wajen gidan ne ke da kamerorin tsaro banda ciki saboda nan akwai na'urorin dake sanar da shigowar mutum, da yake camera ɗin irin wadda ake juyawa ce, ana kuma control ɗinta ta computer ko waya, da stool ɗin ta yi amfani bayan ta hau ta saka sandar floor wiper ɗin ta juyar da camera ɗin ta koma kallon wani direction, dama tana yin hakan a lokuttan baya da asirinta bai tuno ba, ɗaukar stool da wiper ɗin ta yi ta ajiye su gefe wurin flowers, a nan ta tsaya tana dakon isowar ƙawar tata gaba ɗaya kana ganin ta duk a tsorace take....