Sashe 160
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Maleek na fitowa daga gida a mota kai tsaye gidan su Huda ya nufa, bayan ya yi parking yau ma a waya ya kira mummy ɗinta bayan sun gaisa ya ce idan tana nan ta turo ta, bada jimawa ba Huda ɗin ta fito jikinta sanye da jeans da riga da ta kawo mata zuwa rabin cinyoyinta, kanta ta yafo gyale, a nutse take tafiya har ta ƙaraso parking space ɗin Maleek ya kai hannu ya buɗe mata front seat, shiga ta yi ciki ta zauna lokacin da suka haɗa ido da shi har saida gabanta ya ɗan faɗi don ta ga alamun damuwa a tattare da shi, a sanyaye ta ce, "Good afternoon dad." Kai kawai ya jinjina mata, Huda ta yi shiru tare da sauke kanta ƙasa a ranta tana tunanin ko wani abu ya faru, "Huda..." Da sauri ta ɗago jin muryarsa ya kira ta, da ƙyar ta ce, "Yes dad..." Juyawa yay looking at her in the eyes, a ɗan kausashe ya ce,"...I trusted you, but you lied to me!" Miyau Huda ta haɗiya ta zaro idanunta masu ɗauke da brown ƙwayar ido, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Dad....yaushe na yi maka ƙarya?" Maleek ya ce, "Abubuwan da kika faɗa mani lokacin da na kama ku ke da Basma na gane duk ba gaskiya bane, kuma sannan kin yi mani alƙawarin kun daina amman kuka ci gaba da yi....kin ga yanzu dole nima zan sanar da iyayen ki, kuma zan ɗauki mummunan mataki akan ku kaman yadda na faɗa maku a lokacin." Gaba ɗaya Huda ta zaro idanunta, nan da nan jikinta ya hau yin kerma sosai, cikin rawar murya ta ce, "Dad na rantse da Allah ban ƙara yi ba tun daga lokacin...Wllh ban yi ba...ban yi ba dad." Kuka sosai ta sakar masa, Maleek ya yi shiru yana ta kallonta kamar yana nazarin wani abu tattare da ita, dama kawai ya faɗa ne don gano wani abu, amman tabbas a video ɗin ya ga ba ita ba ce, sigh ya yi ya ce mata ta yi shiru to su yi magana, idan ya gano gaskiya take faɗa masa shike nan ba zai sanar ma iyayen nata ba, da sauri ta gyaɗa masa kai tasa gyalenta tana goge hawayen, "Yanzu ina son ki sanar da ni gaskiyar abubuwan da na tambaye ki a baya, waye ya koya maku hakan da kuma tun lokacin da kuke yi." Miyau Huda ta haɗiya muryarta na rawa ta ce, "Ba cousin ena ce ta koya mana ba, Basma ne ta kira ni lokacin ta ce in faɗa hakan idan ka tambaye mu....ita Basma ita ne ta fara koya mani haka, farko ma na nuna mata ba zan yi ba saboda abu ne ba mai kyau ba amman sai da ta ja ra'ayina, kuma kamar yadda na faɗa maka gaskiya ne ni lokacin mun yi one year muna yi..." Fuska a hautsine Maleek ke kallon ta yana sauraron ta, cikin ƙarfin hali ya ce, "Bayan nan kuma na zo na gane kun ci gaba da aikatawa duk da alƙawarin da kuka ɗaukar mani." Da sauri Huda ta girgiza masa kai ta ce, "Wallahi Allah dad tun daga lokacin ban sake yi ba ka ji na rantse." Maleek ya ce, "Idan na ɗauko alqur'an na baki zaki rantse da shi?" Da sauri ta ɗaga masa kai ta ce eh, cike da barazana ya buɗe glove box, hannu ya kai ya fiddo wani madaidaicin alqurani, kallonta ya yi ya ce mata ta san hukuncin mutum ya yi rantsuwa da shi akan ƙarya, da sauri ta ce masa eh ta sani har da ƙoƙarin miƙo hannu ta amsa, Maleek ya yi shiru yana kallonta sai ya ji a ransa ya yadda da ita, janye alquranin ya yi don ya san koda mutum yana da gaskiya ba a son ya rantse da shi, tambayarta ya yi ko Basma ta ƙara buƙatar su yi hakan, ta bashi amsa da eh amman ita ta ce mata bazata ƙara yi ba, hakan ne ma ya sa yanzu ta rage shiri da ita, Maleek ya yi shiru, tabbas ya san shirin da suke ya ragu, to amma shi ya yi tunanin saboda kama sun da ya yi ne wanccan lokacin, tambayar ta ya sake yi ko ta san yadda aka yi Basma ta koya yin hakan ta ce masa bata sani ba, ya ƙara tambayar ta da su wa suke yi lokacin da ake yi da ita, ta ce ita da Basma ne kawai suke yi lokacin, Maleek ya maida kan sa ya jingina da kujera tare da rufe idanunsa, gaba ɗaya ya ji duniyar ta masa zafi, ba abun da yake maimaitawa a cikin ransa face innalillahi...wannan wace irin ƙaddara ce mai muni ta same sa, Huda nata kallon shi cikin ɗaurewar kai, tunaninta komi ya faru da ya sa ya zo yake mata tambayoyin, gashi ta fahimci yana cikin tashin hankali sosai, tausayi ta ji ya bata a hankali ta ce, "I'm sorry dad..." Sai lokacin ya buɗe idanunsa da har sun rine da ja, kallonta ya yi ya jinjina mata kai, hannu ya kai cikin glove box ya ciro wasu kuɗi masu yawa da shi kan sa bai san nawa bane ya miƙa mata ya ce ta amsa ta je gida, ta bi kuɗin da kallo sai kuma ta ce mashi a'a ya bar su, ya ɗan lumshe ido ya ce ta amsa kyauta ce ya bata, ta miƙo hannu ta amsa tare da yi mashi godiya, cikin raunin murya ya ce mata pls ta ƙara kiyaye aikata duk wani abu da yake sa6on Allah ne, Huda ta ce masa in sha Allah ba zata ƙara aikata abu mara kyau ba, ya jinjina kai tare da saka mata albarka, ya ce ta tafi ta gaishe masa da mom ɗinta, kuma idan ta tambaye ta dalilin zuwan shi ta ce mata tare suke da Basma sun tsaya su gaisa da ita, ta ce masa to ta ƙara yi masa godiya daga haka ta fita daga motar.....
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
52
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
52