← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 197

Sashe 179

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ƙaruwar mashi yake, slowly ya furta, "Salmerh.." Kanta na duƙe ta amsa, ya ce ta ɗago ta kalle shi, jimm ta ɗan yi kafin ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta maida idonta ƙasa, hanky ta ga ya miƙo mata ta amsa tana goge hawayen a hankali, ɗan ɗago fuskarta ta sake yi suka haɗa ido ya ce mata mi yasa take kuka ta girgiza masa kai kawai, bai matsa mata kan sai ta faɗa masa ba don ya san kukan na farin ciki ne ba wani abu ba, tambayarta ya yi akwai abun da take buƙata nan ma ta girgiza masa kai, flowers ɗin ya ɗauka ya miƙa mata ta riƙe tana ta kallo fuskarta da yanayin farin ciki, wayarsa ya ɗauka yana latsawa bayan ɗan lokaci bodygurd ɗinsa ɗaya ya shigo, ya nuna masa kwalin cake ɗin alamar ya ɗauka, daga haka ya miƙe ya ce ma Salma su tafi, tana rumgume da flowers ɗin a gefen hannunta guda suka nufi ƙofa, bodyguard ɗinne ya riga su ƙarasowa wurin motan ya buɗe boot ya saka kwalin cake ɗin kafin ya zo ya buɗe masu kofofin, sai bayan da suka shiga cikin motan ɗayan bodyguad ɗin ya fito daga cikin wurin tare da wasu ma'aikata maza guda biyu suna biye da shi suma suna sanye da uniform, kowanne hannunsa na riƙe da ƴan manyan ledoji masu ɗauke da tambarin restaurant ɗin guda biyu, bayan an nuna masu boot suka saka ciki, daga haka bodyguards ɗin kowa ya shiga wurin zaman shi suka tafi...tun da suka hau hanya idanun Salma na ƙasa tana ta kallon flowers ɗin da suka burge ta sosai, a cikin ranta wani irin daɗi take ji, abun da take gani saurayi ya yi ma budurwa a kallo yawanci kuma ƴan ƙasar waje yau shine itama aka yi mata, har ɗan lumshe ido take yi tana shaƙar daddaɗan kamshin da suke saki, shi dai Deen idanunsa na akan wayarsa yana danna ta, lokaci lokaci yake ɗaga ido ya ɗan kalli Salma...bayan sun ɗan yi tafiya suka iso wata babban plaza, ciki suka shiga aka faka motar a wurin da aka tanada don haka, bodyguard ɗin da ke a front seat ne ya buɗe ƙofa ya fita, Salma ta bi sa da kallo yayin da ya nufi cikin plaza ɗin yana tafiya a bubbuɗe, maido idanunta ta yi kan flowers ɗinta bayan ta daina hango mutumin, can ta ji muryar Deen yana ce mata bata gaji da riƙe flowers ɗin ba, ta ɗaga ido ta kalle shi ya ce ta ajiye saman seat ta huta, ta yi ɗan murmushi tana sauke idanunta kafin a hankali ta ajiye gefen ta, after few minutes sai ga bodygurd ɗin ya dawo yana riƙe da wata yar shopping bag, 6angaren da Deen ya ke ya zagaya ya buɗe ƙofar tare da bashi jakan, bayan ya rufe masa kofan ya koma seat ɗin gaba da yake suka tafi. Kai tsaye gidan aunty Kubra suka dawo, bayan an buɗe gate motan ta kutsa ciki, gaba ɗaya bodyguards ɗin suka fita daga cikin motan ya rage saura Deen da Salma kaɗai, a hankali ta juya hannunta looking at the diamond ring sparkling on her finger, ɗago kai ta yi ta kalli Deen da ya jingina da seat yana kallonta, tana ɗan murmushi ta ce masa, "Thank you." Ya ɗan ɗage gira ya ce, "For..." Ta ce, "Proposing to me" Ɗan lumshe ido ya yi ba tare da ya ce komai ba, tambayar shi ta yi ya aka yi ya san wanda zai mata daidai har da kayan ma komai ya yi mata daidai, ya ce kawai ya ƙiyasta ne kuma tana ɗan yawan saka hannu ta rufe fuska ta nan ya san girman yatsunta, ta yi shiru tana murmushi, bayan ɗan lokaci ta ji ya ce, "I'm leaving today." Salma ta ji gabanta ya ɗan faɗi, bin shi da ido ta yi kafin a sanyaye ta ce, "Abuja zaka koma?" Ya ɗan girgiza mata kai, "Zan je Funtua kafin in koma Abuja." Salma ta yi shiru tana ta kallon shi, can ta ce, "Daga Abujan zaka koma London?" Ya ɗaga mata kai alamar eh, shiru ta yi tare da sauke idonta, haka nan ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, sai take jin kamar idan ya tafi shike nan zata rasa shi ne, lokaci guda ƙwalla suka fara tarun mata a ido, kiran sunanta ta ji ya yi ta ɗaga kai ta kalle shi tana kokarin maida ƙwallan, "Why kika yi shiru, ko da wani abu?" Girgiza kai ta hau yi kawai ƙwallan suka yi decieving nata sai ji ta yi sun zubo mata sharr, da sauri ta maida kanta ƙasa tana gogewa, ta ji muryarsa softly ya ce, "Don't you want me to go?" Ta girgiza masa kai a hankali, can ta ɗago ta kalle cikin rawar murya ta ce, "I..will miss you..." Tana yin maganar wasu ƙwallan suka taho mata, ita kanta ta rasa yadda aka yi ƙwallan ke zuwa, still Deen ya yi yana ta kallonta, shi kan shi mamakin yarinyar yake, yadda gaba ɗaya abubuwanta tafiya suke da shi tana ƙara dulmiya shi a son ta, ta ɗago ta kalle shi ganin ya matso a little closer to her, hanky ɗin da ta bashi da za su fito daga restaurant ya ɗago ya kai shi fuskarta yana goge mata ƙwallan da suka jiƙe idanunta dogayen lashes ɗinta sun makale ma juna, calmly ya ce, "Ki daina damuwa princess, ba zan daɗe ba zan dawo." Ta ɗago ido a sanyaye da ƴar sigar shagwa6a ta ce, "Yaushe zaka dawo to?" yana kallon cikin idanunta ya ce, "In two months time in sha Allah." Ta yi shiru tana sauke idanunta, in a whisper ya ce, "Zan je Funtua yanzu saboda ke....next time I come back we will be husband and wife, in sha Allah." Shiru ta yi tana kallon shi sai kuma ta yi murmushi tare da sauke idonta ƙasa, matsawa ya yi ya jingina da kujera yana kallonta, Basma ce ta zo mata a rai wanda ita mantawa ma take da su biyu zai aure, ta ji kaman ta tambaye shi lokaci guda zai aure su, wata zuciyar ce ta kwabe ta kan kada ta tambaye shi, ɗago kai Deen ya yi ya ɗaga hannu yana duba tsadaddan agogon hannunsa, kallon Salma ya yi suka haɗa ido ya ce, "I think I will take my leave now, kada yamma ya yi ." Salma ta ce, "Daga nan zaka wuce Funtua?" Ya ɗan girgiza kai ya ce zai koma hotel kafin ya wuce ta ɗaga masa kai, shiru ta ɗan yi sai kuma a sanyaye ta ce, "Allah Ubangiji Ya kiyaye hanya...Ya kai man kai lafiya ." Ya ɗan lumshe ido ya furta, "Ameen my love." Ta yi ɗan murmushi sai kuma ta langabe kai ta ce, "I love you so much..." Ya wani lumshe mata ido in a low voice ya furta, "I know..." Ta yi ƴar dariya, ɗan shiru suka yi kafin ya kai hannu ya ɗan ƙwanƙwasa glass ɗin ƙofa, bodyguard ɗaya ya zo ya buɗe ƙofan, Deen ya miƙa masa jakan da ya kawo masa ɗazun ya ce mashi a haɗa da kayan boot a kai ciki ya amsa tare da rufe kofar, ya juyo ya kalli Salma dake ta kallon shi yana ɗan murmushi ya ce ko ya tafi da ita, ta ce "Funtua?" Ya ɗaga mata kai alamar eh, ta gane wasa yake yi, ta ce auntynta ta ce za su je tare bada daɗewa ba ya ɗaga kai, lokacin da bodyguards din suka dawo ya ce mata ta je sai sun yi magana ta ɗaga mashi kai, suna ta kallon juna tana jin kamar kar su rabu, hannu ta kai zata buɗe ƙofar aka buɗe mata daga waje, har zata fita ta juyo ta kai hannu ta dauƙi flowers ɗinta, Deen da ke kallonta ya ce bata manta da su ba, ta ɗan girgiza kai kafin a hankali ta ce sune za su rinƙa rage mata kewan shi, ya sakar mata wani kallo tare da ɗan lumshe ido, Salma ta yi tsaye yayin da motan ke ƙoƙarin fita tana jin har ta fara kewar masoyin nata, lokacin da za a rufe gate ɗin ta ga glass ɗin back seat ya sauka, haɗa ido suka yi da shi jiki a mace ta ɗaga hannu tana yi masa bye bye shima ya ɗan yi mata, daga haka aka rufe gate ɗin tana jin tafiyar su...cikin gida ta nufa idonta akan flowers ɗin da ta rungume a hannu, tana shiga cikin falon ta iske aunty Kubra zaune tana latsa wayarta, juyowa ta yi tana kallon Salma da ta nufe ta da ɗan murmushi, aunty ta miƙa hannu ta kama nata tare da zaunar da ita kusa da ita, tana murmushi ta ce, "Baby kun dawo." Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta bi bouquet ɗin da ta rungume da kallo tana ta murmushi ta ce, "Yau ma sai ga mutane ne masu kama da saƙago sun shigo mani." Salma ta ɗan yi dariya tana bin kayan da suka shigo da su da kallo har da basket ɗin awaran jiya aka maido, "Ya aka yi baby na ga kaman jikin ki duk a sanyaye?" Aunty ta tambaya tana kallon ta, Salma ta ɗan yi murmushi tare da girgiza mata kai alamar ba komai, yatsanta mai sanye da zoben ta ɗago ta nuna mata, lokaci guda aunty ta ɗan zaro ido don tana ganin zoben ta gane na diamond ne, kama hannun Salma ta yi da al'ajabi ta ce, "Baby wannan ai diamond ne!" Salma na murmushi ta ɗaga mata kai a hankali ta ce, "He proposed to me." Aunty ta ƙara zaro ido tana sakin faffaɗan murmushi, Salma ta ɗauko kwalin cake ɗin ta buɗe tana nuna mata, a bayyane aunty ta karanta rubutun, ta kai hannu ta dafe ƙirji cikin nuna shauƙi ta ce, "Of course yes..." Salma ta saki dariya ganin yadda aunty ta yi maganar, sauran ledojin aunty ta shiga dubawa ta ga duk kayan ciye ciye ne iri-iri, Salma ta ɗauko ƴar jakar da bodyguard ya kawo ma Deen da suka je plaza tana son ganin miye a ciki, ƙamewa Salma ta yi bayan
Chapter 179 · 0% Book details