← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 197

Sashe 144

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Kubra ta shigo ward din da take sanye da uniform ta ɗaura after dress, shigowarta ke nan aiki bayan ta juya aikin rana hakan ne ya sa bata taho tare da Salma ba tun da da dare zata koma gida, wata staff ce ta zo wucewa ganin aunty Kubra ta tsaya suna gaisawa, "Aikuwa aunty Kubra ɗazun Dr Hisham ke tambayar ki na ce baki kai ga shigowa ba." Staff din ta faɗa, aunty ta tambaye ta ina Dr Hisham din ta ce mata yana office, kai tsaye office ɗin aunty ta nufa, bayan ta kwankwasa daga ciki aka bata izinin shiga, office ne ɗan babba irin na likitoci that's well equipped daidai da matsayinsa na specialist gynaecologist wato likita ƙwararre a 6angaren lalurorin da suka shafi mata, daddaɗan ƙamshi haɗe da sanyin Ac sun karaɗe ilahirin ofishin, Dr Hisham na zaune yana rubutu a saman desk ɗin gabansa, ɗago kai ya yi yana ganin aunty ya ajiye pen ɗin hannunsa yana amsa sallamarta da murmushi, a saman ɗaya daga cikin kujerun gaban desk ɗin da yake ta zauna ta ce, "Dr barka da rana." Ya ce, "Yauwa aunty Kubra an shigo." Ta amsa masa da eh, "Ya baƙuwar mu, ko tare kika zo da ita?" Ya tambaya da ɗan murmushi, aunty ta bashi amsa da tana gida dama saboda idan tana night ba kowa gidan shiyasa take tahowa da ita, Dr ya ɗan jinijina kai, "Yanzu ake ce mani kana nema na." ɗan murmushi ya yi ya kai hannu yana ɗan shafa kansa ya ce ai da ta bari ya iske ta, aunty da itama murmushin ne akan fuskarta ta ce ai ba wani abu don ta iske shi tun da anan shine babba, Dr ya ce, "To ai aunty baki san ko neman da nike maki bai shafi nan ɗin ba." Aunty ta yi ƴar dariya ta ce ta sani ko wani alkhairi ne ai gara kar ta tsaya jinkiri, shiru Dr ya yi yana ɗan murmushi aunty da ke kallon shi ta so ta fahimci kamar yana ɗan jin nauyin maganar da zai mata, sigh ya ɗan yi ya ce, "Nama rasa ta ina zan fara aunty." Tana faffaɗan murmushi ta ce ko ta ina ya fara lafiya lau, gyara zama ya ɗan yi a nutse ya fara magana, "Aunty dama dai ƙaninki ne ya ga abu a wurin ki to kuma ya ji zuciyarsa ta kamu da son abun, shine na ce bari in kawo ƙoƙon barana ko Allah zai sa in dace a bani." Aunty Kubra ta ɗan buɗa ido da ɗan murmushi ta ce, "To Dr miye abun, in dai nawa ne in sha Allah zan baka." Shiru ya ɗan yi still murmushi ne akan fuskarsa haka ma aunty dake jiran ya faɗi abun, "Aunty ƙanwata Salma nike so idan an amince za a bani..." Aunty Kubra ta ɗan jinjina kai tare da kauda fuskarta, dama dai ta so ta zargi hakan a game da shi tun ba yanzu ba ganin yadda yake nuna kulawa akan Salma, "Aunty ko na makara? don na san yadda take tubarkalla ba za a rasa wanɗanda suka kawo irin buƙata ta ba, kuma ƙilan ma an riga an ba wani." Juyowa aunty ta yi ta kalle shi tana murmushi ta ce, "Ba zan ce baby bata da masu son ta ba, amman dai ban tunanin akwai wanda aka ba ita, saboda na san ita sam soyayya ma bata gabanta, karatu take da burin yi sosai hakan ne ma ya sa ko kula samari bata yi." Dr ya ɗan yi faffaɗan murmushi alamar ya ji daɗin maganar, tana kallon sa ta ce, "Amman Dr kai wane irin so kake mata?" Dr ya ce, "Son ta nike da aure, ko yanzu aka amince mani a shirye nike." Aunty ta ɗan zaro ido sai kuma ta yi dariya ta ce da sauri haka, Dr ya ce, "Ai aunty da zafi zafi ake dukan ƙarfe, yanzun nan da na yi sanya sai kika an zo an mani overtaking." Aunty dai ta yi shiru tana ɗan murmushi, tabbas ta san idan Dr Hisham ya auri Salma ta yi dacen miji don ta san yana da kyawun hali kowa na yabon sa kan hakan, kawai abu ɗaya dangane da shi da ya sa ta ɗan ji bata goyon bayan hakan shine kasancewarsa yana da mata, duk da ta san hakan ba wani aibu bane amman kuma bata ma Salma fatan fuskantar matsalar kishiya, jin ta yi shiru Dr ya ce mata ko dai da wani abu ko kuma bata goyon bayan hakan, da sauri aunty ta ce, "No Dr. Hisham, abu irin wannan ai mutum bai zai ƙi goyon baya ba indai ba da wata matsalar ba tun da bamu san abun da Allah Ya ƙaddaro kan hakan ba, kawai dai abun da na sani shine gaskiya ba a shirya yi ma Salma aure ba duba da karatu ta saka a gaba, kuma gaba ɗaya ba wata babba bace don har yanzu ma bata ƙarasa cika 18yrs ba, ga shi ko secondary school ma bata gama ba." Dr Hisham ya ce, "Aunty ai wannan ba matsala ba ce, rashin gama secondary school ba shi ke nufin mace bata isa aure ba, kuma karatu ko a ɗakin miji ana yin sa, gashi dama abun da take son karanta is related to my profession, kin ga kasancewarmu tare matsayin ma'aurata zan taimaka mata sosai wajen samun ilimi da ƙwarewa, amman idan an fi son sai ta fara yin karatun ko ta gama sannan, lafiya lau zan iya jiranta in dai za a bani." Aunty ta yi shiru don gaba ɗaya kanta ya ɗaure ta rasa shawaran da zata yanke kan hakan, boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Shike nan Dr, Allah Ya za6a abun da ya fi zama alkhairi, yanzu abun da ya fi shine ka bayyana mata ra'ayinka a kanta, idan kun fahimci juna ta amince maka lafiya lau ko yaushe mu sai mu sha biki." Murmushin jin daɗi Dr ya yi yana shafa kansa ya ce shike nan zai gwada sa'ar shi, aunty ta kasa danne abun da ke ranta ta ce, "Amman Dr ka san kana da mata, yakamata ku fara fuskantar juna kan hakan, ka fara tabbatarwa ba za a samu matsala ba a tsakanin su idan har al'amarin ya yuwu, don gaskiya ba zan 6oye maka ba, ina jin Salma a raina sosai, ita ɗin tamkar ɗiyar dana haifa a cikina take, bana mata fatan fuskantar ƙalubalen kishiya ba kamar a yadda take da ƙananun shekaru gaskiya." Dr ya jinjina kai tare da tabbatar ma aunty cewa ba za a samu irin ƙalubalen da take nufi ba a gun matarsa duk da ya san wasu matan ba a gane suna da matsala sai hakan ya faru, amman in sha Allahu zai yi bakin ƙoƙarin ganin ba wata matsala da zata faru, kuma ko da ya auri Salma ba gida ɗaya zai haɗa su ba, idan ta kama ma har gari yana iya raba masu, aunty ta ji hankalinta ya ɗan kwanta sanin yana da halin da zai yi hakan, addu'ar Allah Ya tabbatar da alkhairi ta yi ya amsa mata, bayan ta tambaye shi shike nan zata iya tafiya ya amsa mata da eh, har ta miƙe yana ɗan shafa sumarsa ya ce, "Aunty yanzu to ya za a yi ke nan." tana ƴar dariya ta ce, "Idan namiji ya ga mace yana so ya ake yi?" ya ce, "Zai je wurinta ne ya bayyana mata tare da neman soyayyarta." Aunty ta ce, "To kai ma hakan zaka yi." ya ce to ya zo gidanta ke nan, ta amsa masa da eh tana dariya, ya ce ok zai yi hakan amman kafin ya zo pls ta fara masa sharan hanya, tana dariya ta ce to daga haka ta tafi. Washe gari da safe aunty Kubra na zaune da Salma a dining area suna yin breakfast da suka haɗa a tare, lokaci lokaci take kallon Salma a ranta tana tunanin ta in da zata fara mata maganar Dr Hisham don ta san ba soyayya ta iya ba, bayan sun gama Salma ta kwashe kayan da suka yi amfani ta nufi kitchen, sai da ta wanke komai sannan ta fito lokacin aunty na zaune akan kujera, nufo ta Salma ta yi jikinta sanye da doguwar rigar material ta rufe kanta da hula, a kujerar kusa da ita ta zauna tana mata murmushi, itama aunty Kubra shine akan fuskarta ta ce, "Akwai abun da zaki yi ne yanzu?" Salma ta girgiza mata kai ta ce a'a sai dai idan lokacin yin abincin rana ya yi, aunty ta ce, "Akwai maganan da nike son zamu yi ne." Salma ta ce to tare da tattara hankalinta akanta, a nutse aunty ta fara mata bayani game da maganar da suka yi da Dr Hisham, lokaci guda gaban Salma ya fara faɗuwa ta sauke kanta ƙasa, aunty dake kallonta jin ta yi shiru tana murmushi ta ce, "To kin yi shiru baby ni da nike son jin miye ra'ayinki kan hakan?" Shiru Salma ta yi bata ce komai ba kuma bata ɗago kanta ba, hannu aunty ta kai ta ɗago fuskarta kawai sai gani ta yi ta runtse ido da sauri, dariya abun ya ba aunty ta ce, "To miye kuma abun kunya, ki buɗe baki ki faɗa mani ra'ayinki kan hakan ai ba wani abu bane, dama matsayin ki na mace ai dole ne watarana a zo kan wannan ga6ar, don ma ba kula samari kike ba ai da tuni ma an wuce wannan wurin ƙilan ma har an haifa mani grandchild." Da sauri Salma ta sa hannuwanta ta rufe fuska, "Yanzu dai ina son in ji miye ra'ayin ki game da Dr." Da ƙyar idanunta na kallon gefe ta ce, "Ni ai aunty kin san karatu nike son yi, kuma kema ba kina ce mani kar in rinƙa kula samari ba in maida hankali akan karatu." Aunty tana murmushi ta ce, "Hakane, amman kuma hakan ba yana nufin idan Allah ya kawo saurayi na kirki a ƙi kula sa ba, duk dai a yi karatun ƙarshe dole ai a yi aure, kuma aure baya hana karatu, mace tana ɗakin mijinta ma zata iya yin
Chapter 144 · 0% Book details