← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 197

Sashe 46

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba dai tuwo zaku ba mutamin turai ba, koda yake watakil ya daɗe ma bai ci shi ba, ƙilan ya ji dadin shi." Momy na murmushi ta ce haka ya ce ya daɗe bai ci shi ba, ce mata ya yi to shima akai mashi nashi can dining ɗin sai su ci tare da son don an daɗe basu ci abinci tare ba, sai lokacin Fahad ya tuna da saƙon da hajiya ta bada, kallon Khaleel ya yi ya ce mashi ya je motanshi a backseat akwai basket ya ɗauko, after few minutes ya dawo hannun shi riƙe da basket ɗin, Fahad ya kalli daddy ya ce mashi ga saƙo nan in ji hajiya,

"Ni aka ce akawo ma saƙon?" Daddy ya tambaya idonsa akan basket ɗin Fahad ya ce mashi eh, gyara zama ya yi yana faɗin to bari ya ga saƙon miye hajiyan shi ta bada a kawo mashi, da sauri Binafa ta taso tana faɗin bari ta buɗe mashi, maƙe kafaɗa daddy ya yi ya ce shi zai buɗe abun shi, zama ta yi a kusa da shi yayin da ya duƙo yana kokarin buɗe warmers ɗin, yana buɗewa ƙamshin abun ciki ya dakar mashi hanci har sai da ya ɗan lumshe ido yana murmushi, waro ido Binafa ta yi tare da washe baki, Sadeeya da ta dawo falon ta matso tana faɗin bari ta ga miye aka kawo ma daddy din, "Ya Fahad anya baka yi kuskure ba bamu hajiya ta ce akawo mawa ba?" Sadeeya ta faɗa, ɗan murmushi ya yi ya ce na daddy ne, momy dake murmushi ta tambayi miye aka kawo ma daddyn? Binafa ta yi saurin cewa awara ne da chicken sauce, awaran daddy ya ɗauko guda ɗaya bayan ya dankwalo sauce ya kai baki, lumshe ido ya yi tare da furta, "Uwa mai daɗi. Allah Sarki hajiyana, Allah Ya ƙara maki lafiya da nisan kwana masu albarka." A tare duk suka amsa da Amin, rufe warmer ɗin ya yi ya fara kokarin miƙewa yana faɗin shi yama fasa cin tuwon bari ya je part ɗin shi ya ci abun da mamanshi ta aiko mashi, aikuwa da sauri Binafa ta riƙe basket ɗin tana faɗin to su fa, ɗaure mata fuska ya yi ya ce to su aka aiko ma da shi ne, suma idan suna so momynsu ta yi masu,

"Wayyo daddy, amman ya za a ce ido guba." Sadeeya dake tsaye ta faɗa, miƙewa Khaleel da Sadeeq suka yi suma suka je suka zagaye daddyn abun gwanin ban dariya,

"To wai ku ma ba tana aiko maku da abu ba ina saka maku ido ne, sai yanzu don nima an kawo mani zaku yi mani taron dangi. Ga momynku nan idan kuna so sai kuma ta baku kamar yadda nima momyna mai sona ta bani." Tura baki Binafa ta yi ta ce to ai dai suma hajiyan kakarsu ce ko, miƙa ma Sadeeya ya yi ya ce ta ba kowa tun da basu son ya ci ya ƙara ƙiba, amsar basket ɗin ta yi tana dariya ta ce, "Daddy dama ai kaza mai ƴa'ƴa bata maiƙo." Yana yar dariya ya ce kawai dai sun cika son kai. Kowa ya yaba da daɗin awaran bayan sun ci har da daddy ɗin ma, Deen da Fahad su basu ci ba cewa sukai sun ƙoshi sun ci a can gidan hajiya, Sadeeya ta ce gaskiya suma za su yi irinta gobe, momynsu ta ce to sai a kira hajiya a yi mata magana tun da dama idan suna son awaran daga can unguwarsu ake yo masu.

Bayan sun gama cin awaran, gaba É—ayansu har da daddy da Deen suka wuce dining area don cin abincin dare dama duk basu ci ba, Binafa da Sadeeq dai cewa suka yi yadda suka ci awara mai daÉ—i baza su ci tuwo ba sai dai su haÉ—a cornflakes da madara su sha, momynsu ta ce su dai suka sani da gulma tuwon ma ai special tuwo ne. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya wuce da Deen zuwa part É—insa dake a can saman bene......

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

ZAINAB BATURE

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 16

Bayan sun isa part ɗin Fahad a falo suka zauna wanda madaidaicin falo ne mai ɗauke da kujeru leathers da kayan sauti da su hotunan family ɗin shi, yar hira suka ta6a kafin Fahad ya miƙe ya ce mashi bari ya je ya watsa ruwa ya rage kayan jikinsa, maida hankali Deen ya yi akan tv bayan ya kamo sport channel wato tashar dake haska wasanni, yana cikin kallon ya ji wayar shi na sanar da shi sweetheart na kira, ɗan jimm ya yi tare da lumshe idanunsa, ya san ko ya ɗaga ba lalle su kwashe ta ta daɗi ba shi da mahaifiyar tashi, sai bayan da kiran ya yanke sannan ya kai hannu ya ɗauki wayan a gefensa ya fara kokarin kiran ta, kamar jira ta ke wayan na fara yin ringing ta yi picking,

"Ai da baka neme ni ba Deen a sannan zan san ka cika ɗa, wato rainin da ka yi mani har ya kai haka! Ka tsallake ka tafi ba tare da ka sanar mana ba a matsayin mu na iyayenka, da izinin wa ka tsallake ka bar garin nan? Wai yaushe ka canja ne haka Deen? Gaba ɗaya ka daina ganin girman mu, wani ya fi mu matsayi a gun ka da zai saka ka yi abun da kasan zai 6ata mana rai, alhalin shi ko da wasa ba zai ta6a aikata abu makamancin wannan ba ga na shi iyayen. Ina wayonka da tunaninka suka tafi Nuraddeen!" Shiru ya yi tare da ɗan cize leben shi na ƙasa, daga yadda ta kira ainihin sunan shi ya fahimci ba ƙaramin harzuƙa ta yi ba don ba zai iya tuna when last da ta kira sunan shi haka ba. Sigh ya yi calmly ya ce, "I am sorry mom, ni ban yi haka don in 6ata maku rai ba, ki daina tunanin wai na canza ko na raina ku bana fatan hakan ya kasance, kuma ki daina zargin yaya Fahad ne ya sa na zo nan ba ruwansa ra'ayin kai na ne..."

"Ka ce ra'ayin kan ka ne Deen? Ra'ayin ka ne ka 6ata mana sannan ka ce wai in daina cewa ka canza?" Ta faÉ—a bayan ta katse shi,

"Ki yi hakuri idan haka da na ce baki ji daɗi ba, ina so ne in fahimtar da ke yaya Fahad bashi da hannu a tahowana nan, shi bai ma goyi baya ba da na ce zan zo nan, a tunaninsa zan bari sai na huta, ni ne na ga is better in taho nan..." Shiru ta ɗan yi da alama nazarin abun da ya faɗa take, kafin ta ce, "Har nan ya fi maka ke nan a kan gidan iyayen ka, haka kake nufi Deen?" Juyar da kan shi ya ɗan yi yana riƙe da wayan a kunnan shi,

"Mom I won't hide it from you, bana jin daɗin yadda abubuwa suke faruwa, na daɗe ban zo ba I thought zan samu complete happiness amman sai na ga ba haka ba. Yaya Fahad brother nane, yadda kuke farin cikin zuwa na shima haka ne, shiyasa ya zo wuri na ba wani abu ba amman hakan ya zama abun tashin hankali.." Shiru ya yi bai ƙarasa ba, daga yanayin voice ɗin shi ta tabbatar da gaske ne abun da ya faɗa, yar ajiyar zuciya ta sauke cikin ƙoƙarin daidaita natsuwarta tare da kwantar da murya ta ce mashi shike nan ya yi haƙuri ba zata ƙara yin abun da zai 6ata mashi rai ba. ta ce, "Yanzu yaushe zaka dawo nan don muna son ka a kusa da mu saboda mun yi missing naka sosai." Ɗan murmushi ya yi ya ji daɗin yadda ta yi mashi magana, amsa ya bata da zai ɗan kwana biyu anan saboda yana shirin buɗe club ɗin shi. "To yaushe zaka je can Kano wurin su Ammin suma?" Shiru ya ɗan yi, ba wai bai son zuwa wurin na su ba, kawai akwai abubuwan da suke mashi da baya jin daɗin su bama a zahiri ba ta waya ma, yasan idan ya ce ba zai je ba hakan zai zama wani issue hakan yasa shi ce mata zai je kafin ya koma tun da zai yi 2 weeks kafin ya tafi gaba ɗaya, ta amsa mashi da ok.

"Have u called Basma?" Ta tambaya, É—an jimm ya yi yana shakkar amsar da zai bata don shi yama manta da Basmar balle ya neme ta, sai É—azun da yamma a gidan hajiya da ya ga missed calls nata bayan ya fito daga wanka kuma bai bi kiran ba. "Nah, I wanted to be well settled sai mu yi magana da ita sosai." Amsa mashi ta yi da ok kafin ta ce mashi yanzu sai yaushe za su yi expecting nashi, ya bata amsa da zai yi kaman kwana biyar sai ya dawo, ta ce mashi to ko kawai ya wuce Kano daga nan ma, ya ce mata dole sai ya dawo nan tun da bada mota ya taho ba kuma yana son zai bi jirgi ne zuwa Kanon, saida ta jaddada mashi game da ya kira Basma sannan suka yi sallama. Bayan sun gama wayan shiru ya yi tare da É—an lumshe idonsa, yana haka Fahad ya fito ya shirya da brown din jallabiya mai gajeran hannu, a kusa da Deen ya zauna yana kallon shi ya kira sunan shi, slowly ya buÉ—e idon shi tare da kallon shi, gyara zaman shi ya yi ya ce ya fito Fahad ya amsa mashi da eh yana bin fuskarsa da kallo,
Chapter 46 · 0% Book details