← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 197

Sashe 56

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka sha kuruminka Imrana, ka taya ni addu'a in sha Allah na zama nurse na fara aiki in dai ba a siya maka ba ko ya kai nawa ni zan siya maka." Kai ya ɗaga ma Salma da ta yi maganar, Sagir ya ce, "Sai ka ce zama nurse ɗin wata tsiya ake samu zaki wani cika ma mutane baki, ni zuwa lokacin in sha Allahu ai na sha kwana, irin mashin ɗin fin guda goma ma sai na siya masa, amman ko da ina da halin ma ba zan siya ba tun da ya iya yi ma mutane rashin kunya don uban shi." Wani kallo Imrana ya jefe masa bai dai ce komai ba, a haƙiƙance Salma ta ce wllh in dai har ta fara aiki matsayin nurse siyan wannan mashin ɗin ba zai gagare ta ba, innarsu dai nata bin su da murmushi sam basu gajiya da shan chapter. Bayan sallar isha Deen da Fahad suka fito da hajiya don su zaga gari a sabuwar motan, daga baya suka wuce gidansu Fahad, daidai lokacin da Deen ya faka motan a cikin gidan sai ga daddynsu da sauran yara maza sun dawo daga masallaci, cike da farin ciki yaran suka tarbi kakarsu haka ma daddynsu ya ji daɗin ganin mahaifiyar tasa sosai, bayan sun gama gaisawa hajiya na murmushi ta ce, "Sabuwar amarya Deeni ya yi shi ne aka fito da ni ɗani." Kai daddy ya jinjina gaba ɗaya idanunsu na akan motar tun bayan da suka shigo dama ta ja hankulansu, "Ma sha Allah son, motar ta yi kyau sosai. Kamar avatr ko?" Kafin Deen ya bashi amsa Khaleel ya yi saurin cewa ita ce, hajiya ta ce, "Ni ai ban ma san motan ba, sai yau na fara ganin irinta." Daddy na murmushi ya ce mata ba a daɗe da aka fara yayin ta ba a nan, hajiya ta sake cewa, "Yayin masu kuɗi ko, don na ji ba laifi motan akwai kuɗi, a haka ma Deeni ya ce wai ba mai kuɗi bace wannan sosai." Daddy ya ce amman ya san wannan bata rasa yin hundred million koma ta fi, hajiya ta ce kusan haka don miliyan tamanin da biyar Deeni ya ce ya siya, gaba ɗayansu suka jinjina kai, "Congrats bro, ta yi kyau sosai. Allah Ya tsare " Khaleel ya faɗa yana murmushi, Sadeeq ma ya ce, "Ya Deen Allah Ya sa alkhairi Ya tsare." Da murmushi ya amsa masu da Amin, Daddy ma ya yi mashi addu'ar Allah Ya sanya alkhairi ya tsare, Sadeeq ne ya ce bari ya je ya kira su mommy da yaya Sadeeya su zo su ga sabuwan motan yaya Deen ya ruga cikin gida, ba da jimawa ba sai ga su sun fito sun nufo wurinsu, da gudu Binafa ta nufi hajiya tana faɗin, "Oyoyo granny..." Tarbe ta hajiya ta yi tana murmushi ta ce, "Oyoyo ƙawalliyana..." Fuskar momy da murmushi ta yi mata sannu da zuwa, Sadeeya ta rungumo kafaɗar hajiya tana mata sannu da zuwa,

"Wow, what a fabulous car!" Sadeeya ta faɗa bayan ta saki hajiya ta nufi motan tana kallo, "Kamar avatar ko?" Fahad ya bata amsa da ita ce, ta shiga shafa jikin motan tana zuba santi, momy dake murmushi ta ce, "Ma sha Allah son, motan ta matuƙar yin kyau sosai. Allah Ya sa alkhairi ya tsare ya ƙara arziƙi mai albarka." Duk aka amsa ma momy da Ameen, sakin hajiya Binafa ta yi tana kallon motan ta ce, "Ya Deen wannan motan mai kyau ka siya!" Kafin ya bata amsa hajiya ta ce ba tashi bace ta ta ce ta siya, wani kallo ta yi mata ta ce, "No na san ba taki bane, ai ke tsohuwa ce, ta yaya Deen ce." Jawo ta hajiya ta yi tana faɗin, "Zo nan ki gaya mini shi tsoho bai hawa mota mai kyau." Ta maƙe kafaɗa tana kyalkyala dariya haka sauran mutanen wurin,

"Gaskiya yaron nan ka samu duniya!" Sadeeya ta faɗa tana murmushi tare da jinjina kai, "Lahira ma zai samu in sha Allah." Daddy ya faɗa duk suka amsa da in sha Allah, Deen ya ce ma Fahad ya yi testing nasu ya amsa da ok, Fahad ne ya shiga driver seat daddy na other side, baya Sadeeya da Khaleel da Sadeeq sai Binafa suka shiga suna ta santin tsaruwar cikin motar, cikin harabar gidan ya shiga zagayawa da su, Deen ya kira Fahad a waya ya ce mashi ya fita da su mana suka fita gate, after a while suka dawo itama mommy ta shiga aka zagaya da ita cikin harabar gidan, ba abun da suke sai yabo da son barka bayan sun gama ɗana motan, daga baya suka shiga cikin gidan, Fahad ya wuce part ɗinsa tare da Deen, a bakin gado Fahad ya zauna shi kuma Deen ya ɗan kishingiɗa tare da dafe forehead ɗinsa, Fahad na kallonsa ya ce ya gaji sosai ko don yau bai huta ba, yana murmushi ya bashi amsa da ai gajiyan ku san tare suka yi shi, "Yanzu zuwa wane lokaci ne za a yi launching club din?" Hannu Deen ya kai ya shafi sumar fuskarsa ya bashi amsa da shine yake son su zauna su tsara komai lokacin da yake da time, Fahad ya ce yana ganin ko zuwa gobe tun da ba aiki, Deen ya ce ok goben idan sun gama morning training zai zo, ya sake cewa "Ka ga da kaima kana harkan football sai ka zama manager ko kuma corch." Murmushi Fahad ya yi ya ce shi ai ba abun da ya haɗa shi da ƙwallo da dai abun da ya shafi bangaren lafiya ne, "Yauwa, ya maganar private hospital ɗin da kake so ka gina? Mun fara maganan baya..." Deen ya tambaya idonsa akan Fahad, gyara zama Fahad ya yi ya ce mashi maganan na nan yana son ya ƙara shiryawa ne sosai, "Amman already daddy ya baka plot so wani shiri yanzu ya rage?" With a smile on Fahad's face ya ce,"Kasan harkan gini yana bukatan a yi mishi shiri financially, idan ba haka ba sai ka ga abu ya zo yana delay." ɗan jinjina kai Deen ya yi alamar gamsuwa, sai kuma ya ce, "Idan wannan ne let's collaborate on it and get it done faster. Ka ga kai you provided the plot ni kuma sai in ɗauki nauyin aikin ginin" Wani kallo Fahad ya jefa masa sai koma ya janye fuskarsa gefe da ɗan murmushi, ya gama fahimtar Deen wato ya san idan ya nuna zai bashi kuɗi ba lalle ya amince ba shine ya 6ullo mashi ta hakan, kamar Deen ya san abun da ke a ran Fahad ya sake cewa, "Ka san nima I have the intention of building a hospital here, bari kawai mu yi amfani da wannan daman." Kallonsa Fahad ya yi da ɗan murmushi ya ce,"Amman ka san filin ba siya na yi ba?" Ɗan buɗa masa ido Deen ya yi ya ce, "But daddy ne ya baka,so ya zama naka ne ai." Fuskantarsa Fahad ya yi sosai, a nutse ya ce, "Deen, ka san aikin gini ba ƙananun kuɗi yake ci ba, ba kamar ginin asibiti dake buƙatan abubuwa da dama, ina ganin lissafin bai yi daidai ba a ce na bada fili kai kuma ka ɗauki nauyin ginawa." Ƴar dariya Deen ya yi don ya gane Fahad ɗin ya gane wayonsa, "Ba wani damuwa in sha Allah ba wani abu da zai gagara." Ya ƙare tare da ɗage ma Fahad gira, kafin ya ce wani abu aka yi sallama, "Assalamu Alaikuum..." Duk suka kai idanunsu kan kofan shigowa, Sadeeya ce ta nufo su tana murmushi, "Barkan ku da hutawa..." Deen ne ya yi mata murmushi tare da amsa mata, "Dama daddy ne ya ce a yi maku magana ku zo mu yi dinner." Fahad ya ce mata a kawo masu abincin nasu nan, ta ce,"Da hakan za a yi but sai daddy ya ce tun da duk an haɗu har da hajiya a yi dinner ɗin tare." Kai Fahad ya ɗaga, kallon Deen ta yi ta ce, "Gaskiya lil bru yakamata idan zan koma school ka fasa da ni a sabuwar motan can taka, na san zan tashi kan mutane over." Yana murmushi ya ce mata ta nemi lil bru ɗin nata sai ya kai ta, dariya ta yi ta ce, "To yaya Deen..." Shima yar dariyar ya yi kafin ya tambayi yaushe zata koma ta bashi amsa da ranar talata, ɗan jimm ya yi kafin ya ce ok zai duba yuwuwar hakan don yana da schedules ranan amman idan ma bai samu kai ta ba sai Fahad ya yi using motan su tafi tare idan zai je wurin aiki" Ta yi masa godiya tana murmushin jin daɗi, daga baya suka fita zuwa yin dinner din. Bayan an rako su za su koma gida, Fahad ya ce ma Deen akwai wani aiki da yake son yi a daren da sun tafi tare, Deen ya ce masa ba matsala gobe zai zo nan ya wuni su ƙara tattaunawa.

Salma ta gama yin shirin bacci tana niyyar kwanciya saman gadonta wayar innarsu dake a hannunta ta fara yin ringing, duba mai kiran ta yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin sunan mai kiran, É—auka ta yi ta kai wayar kunne a nutse ta fara magana, "Asslamu Alaikum..." Daga É—ayan 6angaren muryar mace ta amsa, "Wa'alaikumus salam, yaya Fiddausy barka da dare..." Yar dariya Salma ta yi ta ce, "Aunty Kubrah ba ita ba ce, baki gane muryata ba?"
Chapter 56 · 0% Book details