Sashe 67
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ƴar sallama ta shiga cikin falon, tana shiga idanunta suka sauka akan Deen dake zaune saman kujera mai mazaunin mutun biyu ya jingina bayansa tare da ɗan miƙar da ƙafafunsa, har ta ƙarasa ciki ta tsaya daga gefe sam bai ji shigowarta ba don idanunsa na akan tv yayin da ya toshe kunnuwansa da headphones, tun bayan da ya gama waya da mom ɗinsa ya fito nan ya zauna yana buga PS wanda ya kawo daga part ɗin su, kallon controller ɗin da yake riƙe da yana motsa hannuwansa a hankali Salma ta yi kafin ta kai idonta kan FIFA, wato game ɗin ƙwallon ƙafa da yake bugawa, bayan ɗan lokaci ta ƙara yin sallama ganin alamun bai san ta shigo ba, sai dai still bai juyo ya kalle ta ba, tunanin ko bai jin ta ne ta yi tana kallon headphones ɗin kunnuwansa ta raya ƙilan wani abun yake ji shi ya sa, ta shiga tunanin yadda za ta yi masa magana can ta maida idanunta tana kallon game ɗin da yake yi, after a while ya fara ƙoƙarin gyara zaman shi, ganin kamar mutum ta gefensa ya sa shi ɗan juyowa, daidai itama Salma ta maido idonta kansa jin motsin shi, haɗa ido suka yi ya bita da kallo mai kaman na mamaki, ɗan murmushi ta shiga yi tana kifce kifcen ido, hannu ya kai ya cire headphones ɗin ganin haka ta yi saurin ce masa, "Ina wuni." Kai ya jinjina mata tare da gyara zamansa, sauke idanunta ta yi ta rasa ta ina zata fara yi masa magana saboda ƙwarjinin da yake mata, ɗagowa ta yi suka sake haɗa ido cikin yan kame kame ta ce, "Ina ta yin sallama da na zo baka ji ba." Kai ya ɗaga calmly ya ce, "Sorry, nasa headphones." Kai ta ɗaga tana ɗan murmushi, "Hajiya tana ciki, let me call her..." Ya fara ƙoƙarin miƙewa, sam ta kasa sanar da shi wurin shi ta zo, bada jimawa ba ya dawo ya ce mata hajiya tana zuwa ta ɗaga masa kai, bayan ya koma ya zauna ya ci gaba da yin game ɗin sa ba tare da ya mayar da headphones ɗin kunnansa ba, hajiya ce ta fito ta nufo cikin falon tana sanye da dogowar rigan bacci da hula, "Salma ce.." Ta faɗa bayan ta ƙaraso, Salma ta ce, "Hajiya ina wuni." Amsa mata ta yi ta ce ga wuri ta zauna ta yi tsaye, "Yau na gaji sosai saboda fitar da muka yi, shi ya sa na kwanta da wuri " Hajiya ta faɗa tana yin hamma, a hankali Salma ta ce, "Sannu.." Ta amsa da yauwa, jimm ta ɗan yi kafin da ƙyar ta ce, "Ga shi an ce a ba yaya Deen." Ta faɗa tana ajiye ledan daga gefen kujeran hajiya, kallon ledan hajiya ta yi tana ɗan murmushi ta ce, "To yau ma wani abun daɗin aka kawo ma Deeni?" Salma tana ɗan murmushi ta ce mata awara ce, godiya hajiya ta yi ta kalli Deen ta ce, "Ashe ma wurin ka ta zo Deeni." Kallon hajiya ya yi ta nuna masa ledan tana ce mashi saƙon sa ne, da alamun rashin fahimta ya kalli ledan hajiya ta ce ma Salma ta kai masa, miƙewa ta yi ta ɗauki ledan ta kai gabansa ya bita da kallo, "Awara ce aka ce in kawo maka." Ta faɗa a hankali, kai ya ɗaga sai kuma ya ce, "Thank you..." hajiya ta ce masa, "Ka sa Balaraba ta kawo maka abinci ne?" Ya bata amsa da ta kai dining area, ta ce, "Ai da ka ci dare na yi, ko da yake ga awara nan sai ka fara ci, Salma je kitchen ki ɗauko wuri sai ki zuba masa." Amsawa ta yi da to ta wuce don ta yi abun da ta ce, bayan ta dawo ta zuba masa ya ce ta kai ma hajiya sauran, hajiya ta ce, "Anya zan ci awaran nan kuwa don na gama shirin kwanciya har baki na wanke, maida masa na san zai iya cinyewa duka." Ƴar dariya Salma ta yi ganin irin kallon da ya yi ma hajiya bayan ta mayar masa da awaran, a nutse ya fara cin awaran, "Miye wannan kake kallo ne?" Hajiya ta tambaya tana kallon game ɗin da ya tsayar, ya ce mata game ne tare da ɗaukar remote ya fita daga wurin ya maida masu kallo, a tare gaba ɗaya suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa jin an yi sallama, ƙirjin Salma ne ya buga ganin wanda ya shigo cikin falon, bayan ya ƙaraso ciki hajiya ta ambaci sunansa tana murmushi, ya gaishe da ita tare da zama a gefen Deen, tun da Salma ta kalli Fahad da ya shigo bata yarda ta sake kallonsa ba, kallon Deen dake masa murmushi ya yi cikin muryarsa mai tattare da nutsuwa ya ce, "Acici...da alama wannan kafin ka koma sai ka cinye ma hajiya duk abincinta." Hajiya ta yi dariya ta ce, "Ban da nawa ma har ma da na maƙwabta, don wannan ɗin Salma ce ta kawo masa." Sai lokacin ya kai idanunsa kan Salma daidai ta ɗago suka haɗa ido nan take fuskarsa ta canza, gaishe shi ta yi ya amsa ba yabo ba fallasa tare da janye idonsa ya maida kan tv, "Akwai sauran awaran Salma ta zuba maka." Tamkar an faɗi masa wani mugun abu ya yi saurin ce ma hajiya a'a ya ƙoshi, Salma dai idanunta na a kasa duk ta sha jinin jikinta, jin motsi ya sa ta ɗan ɗago idanunta ta ga Deen ne ke ƙara awaran, haɗa ido suka yi ya yi mata ɗan murmushi don ya lura da rashin sakewarta tun bayan shigowar Fahad, itama ɗan murmushin ta yi masa ta janye idonta, bayan ɗan lokaci ta miƙe ta ce ma hajiya ta tafi, hajiya ta ce mata ai ya kusa gamawa ta bari sai ta tafi da kayan kawai, ba don ta so ba ta koma ta zauna, hajiya ta ce, "Fahad ga abinci can a kan table da aka shirya Deeni bai kai ga ci ba, ko kuma ya gama sai ku ci tare." Deen ya kalle ta ya ce, "Na ci wannan na ƙoshi." Cike da zolaya hajiya ta ce, "Kai dai, na san shima abincin ba zai rasa shiga ba, ko kunya kake ji kada Salma itama ta fahimci acici ne kai." Murmushi kawai ya yi ya ci gaba da cin awaran, wani kallo Fahad ya yi ma hajiya ganin kamar raini take ja ma Deen da ta yi maganar a gaban yarinyar, dama ya yi mamakin jin cewa ita ta kawo masa awara kuma yake ci, akan wani dalili? Da alama ransa ne ya 6aci ya sa shi miƙewa zai wuce ciki, hajiya dake kallon sa ta ce ba zai ci abincin ba? a taƙaice ya bata amsa da sai ya fito, Salma tabi sa da ido tun lokacin da hajiya ta yi magana ta saci kallonsa ta ga yanayin sa ya canza, jikinta ne ya yi sanyi don ta fahimci duk saboda saka ta a maganar da hajiya ta yi ne, ita har cikin ransa ta basa haƙuri lokacin da hajiya ta sata saidai ta fahimci ya nuna ya haƙuran ne ba har ransa ba, Deen da ya bisa da ido shima ya fahimci yanayin Fahad ɗin ya canza. Bayan ya gama Salma ta je ta tattara kayan ta kai kamar jiya ta wanke su sannan ta fito, sallama ta yi masu bayan ta saka kayan a leda hajiya ta ce ta gaishe da innarsu ta yi mata godiya, kallon Deen ta yi suka haɗa ido da ɗan murmushi shima ya ce mata ya gode ta ɗaga kai daga haka ta tafi, bayan Salma ta tafi kusan tare shi da hajiya suma suka bar falon bayan sun yi ma juna saida safe kowa ya wuce bangaren sa. Shirye shiryen bikin buɗe sabon club din Deen sun kankama, su Sagir ba zama anata shiri an yo masu jerseys na club ɗin kala biyu da takalma. Washe gari talata da yamma Salma ta shirya don zuwa gidan hajiya ta kai ma Balaraba faran da ta soya, wata coffee brown ɗin abaya ta saka a cikin irin kayan gayun da aunty Kubra ke siya mata, aikin jikin abayar mai kyau da stones kuma ta matuƙar amsar jikinta ta kuma ƙara fiddo da kyaun fatarta, yafa gyalen rigar ta yi saman kanta daga ƙasan ƙeyarta inda ta naɗe sumarta ya yi tudu, yayin da daga gaban kanta kwantacciyar sumarta dake a nannaɗe ta ɗan fito, sosai ta yi kyau idan ka ganta zaka yi tunanin ba daga nan gidan take ba ɗiyar masu kuɗi ce, bayan ta gama shiryawa ta fito, ɗakin innarsu ta nufa don ta sanar mata, haɗa ido suka yi da innarsu bayan ta ɗaga labulen ɗakin, tana zaune akan kujera ganin Salma ta fara sakin murmushi, daga gefenta Salma ta zauna itama murmushin ne akan fuskarta, innarsu ta ce, "Ka ga ƴan matana Masha Allah, ina zuwa?" Ƴar dariya Salma ta yi ta ɗan ɗaga mata ledan faran hannunta ta ce zata je kai ma aunty Balaraba fara, kai innarsu ta ɗaga mata ta ce, "Idan wanda bai san ki ba ya gan ki ba za a ta6a yarda cewa sana'ar tuyar awara da fara kike ba." Dariya sosai Salma take fararen haƙoranta sun bayyana, bayan ta dakata ta ce, "To ai dai innarmu sana'a ce ko, kuma yanzu har ƴan gayun masu kuɗi suna yin irin waɗannan sana'oin." Innarsu dake ƴar dariya ta ce, "Amman su tasu sana'ar zaki ga a wayance suke yin ta.." Salma ta tari numfashinta, "Kawai packaging ɗin abubuwan ne suke wasu su kai manyan kantuna ko supermarket, nima da sana'ar faran tawa ta kankama ai zan iya yin hakan." Murmushi innarsu ke yi tana bin ta da kallo mai cike da ƙauna, kallon ɗan plate ɗin dake gefenta Salma ta yi wanda ta zubo mata fara bayan ta gama soyawa ta ce, "Faran ya yi daɗi?" Ta ce sosai ma komai ya yi daidai, "Sai yaushe za a yi kitso? Ko kuma sai an gama gayu da shi?" Innarsu ta tambaya tana kallon kan Salma da gyalen ya zame, shiru ta ɗan yi tana mata murmushi