Sashe 90
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Deen ya farka daga baccin da ya ɗauke shi mai nauyi har an gamma sallar azahar, anan ɗakinsa ya yi salla bayan ya gama ya duba wayarsa ya taras yana da missed calls ciki har da na hajiya da kuma Fahad da daddy Sa'ad, gaba ɗaya ya kira su suka yi mashi ya ya isa, Fahad ya yi mashi godiya sosai da addu'oi, bayan ya gama bin kiran da zai bi sake kwanciya ya yi don ji yake baccin bai ishe sa ba, bai daɗe da rufe ido ba ya ji an buɗe kofar ɗakin hakan ya sa shi buɗe ido, Leemarh ce ta nufo shi da faffaɗan murmushi akan fuskarta da gani bata daɗe da dawowa daga school ba don ko uniform bata cire ba, a bakin gadon ta zauna tana kallon Deen cike da farin ciki ta ce, "Ya Deen ashe ka dawo?" Kai ya ɗaga mata tare da miƙa mata hannunsa ta kama tana ta murmushi ta ce, "Ai da na san yau zaka dawo ba zan je school ba." Ya ɗage gira ya ce, "Why?" Tana ta murmushi ta ce, "Don a je da ni welcoming naka airport." Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce wani abu ba, farin cikin da yake gani akan fuskarta ya sa maganganun mom ɗin su suka dawo mashi, tana son ta tambaye shi Fahad amman haka nan take jin nauyin hakan, can dai ta ce, "Ya Deen ina Yaya Fahad?" Gyara kwanciyarsa ya yi still hannunsa na a nata ya bata amsa da a Kaduna suka rabu shi ya yi dropping nashi, shiru ta ɗan yi sai kuma ta sake cewa, "Dama ya biyo ka kun dawo nan tare." yana ɗan murmushi ya ce, "Aikin shi fa?" Dan yamutsa fuska ta yi a shagwabe ta ce, "To ai sai a daɗe kafin ya zo nan, ga shi ya zo kuma duka kwana ɗaya ya yi ko sallama da shi ba a yi ba ya tafi." Dan murmushi mai faɗi Deen ya yi zuwa yanzu ya riga ya gane tana crushing Fahad ne, "Idan kina son ganinsa sosai ba sai ki je can ba." Haɗa ido suka yi jin yadda ya yi maganar ya sa ta yi saurin kama kanta ta ce, "Ai ba shi kaɗai ba duk ina missing kowa na can an daɗe ba su zo ba." Deen ya ce mata idan suka samu hutun school sai ta je, da sauri ta ce dama niyyanta ke nan, turo ƙofar aka yi Batool ta shigo itama tana sanye da kayan makaranta, da gudu ta nufo gadon Deen na ganinta ya saki hannun Leemarh tare da tashi zaune ya ware mata hannu, hayewa ta yi saman gadon ta faɗa jikinsa ya rungume ta, cikin muryarta mai tattare da shagwaba ta ce, "Yaya Deen welcome back." Yana kallonta da murmushi ya ce, "Thank you my Batool, how's school?" Ta amsa, "Lafiya lou." Ya ce tana dai karatu sosai ko ta daga masa kai, kallon shi ta yi ta ce, "Amman dai ya Deen ba zaka ƙara tafiya ko ina ba ko?" Shiru ya ɗan yi ya kai hannu yana shafa gefen fuskarta ya ce mata zai je Kano ya yi kwana ɗaya daga nan idan ya dawo ba zai sake zuwa ko ina ba har sai lokacin da zai koma London, murmushin jin dadi ta saki ta ƙara shigewa cikin jikin sa, haka nan yake jin zancen mom ɗin su kamar gaskiya ne yan'uwansa basu samu lokacin shi ba sosai, hira ya shiga yi da su suna haka bayan ɗan lokaci aka sake turo ƙofar duk suka kai idanunsu wurin, mom ɗin su ce ta shigo ta sha ado da haɗaɗɗar applique atampa ɗinkin riga half gown da zani ta wani coge ɗaurin kallabi, gaskiya ba ƙarya Jameela ba ƙaramar kyakkyawa kuma dirarrar mace ba ce dole take murza kambunta yadda ta ga dama, kana ganinta ka ga matan Abuja masu cikakken capacity, cikin tafiyarta mai tattare da isa ta nufo cikin ɗakin, ganin su ya sa ta shiga sakin murmushi har ta ƙarasa gaban gadon ta tsaya, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da ƙamshin da jikinta ke saki mai matukar daɗi, kallon Deen ta yi ta ce, "Hakan suke bukata a wurin ka." Ya dan yi nodding kai, kallon su Leemarh ta yi da suma ita suke kallo ta ce sun ji daɗin ganin big bro ɗin su ya dawo ko duk suka ce mata eh suna murmushi, "Momy kin yi kyau." kallon Batool da ta yi maganar ta yi ta ɗage mata gira ta ce, "Thank u mah gurl." tare da kissing nata daga nan, "Shi ya sa dad ya kasa yi maki kishiya saboda yadda kike kashe shi da gayu." Wani kallo ta jefa ma Leemarh da ta yi maganar tana dariya, ɗan yamutsa baki ta yi ta ce ya ma yi, shi dai Deen ɗan murmushi kawai yake yi, ce ma su Leemarh ta yi su tashi su je su cire uniform ɗin jikinsu, bayan sun tafi ta kalli Deen ta ce an sha bacci ya ɗaga mata kai, "To ka taso food is ready on the table." Ya ce mata ba ya jin yunwa, tana kallon shi ta ce, "Ka dai taso haka nan ka je cikin ƴan'uwanka ku ci tare za su ji daɗi." Kai ya ɗaga mata alamar to ta miƙa mashi hannu alamar ya ta so, kama hannun ya yi ya sauko daga gadon ya ce zai wanke baki yana zuwa ta tafi. Gaba ɗayansu har da mom suka zauna cin abincin amman ban da dad ɗin su don bai dawo ba, ba wani da yawa ya ci ba amman ya zauna wurin har sai da ƴan'uwan nasa duk suka gama daga baya suka dawo falo. Bayan Salma ta dawo daga makaranta, sosai ta yi mamaki ganin uban kayan abincin da aka aiko masu daga gidan hajiya in ji Deen, jiki a sanyaye ta nufi dakinta, a bakin gado ta zauna tana kallon wuri guda, haka nan take jin wani yanayi a tattare da ita mai kamar na kewar Deen ɗin, kyakkyawar fuskarsa ta shiga dawo mata a rai, ji take kamar ta kira shi, sai dai sabuwar wayar tata na a wurin Sageer da ya amsa idan ta dawo zai nuna mata abubuwa kuma yanzu bata iske shi a gida ba, a hankali ta kwanta tare da rufe idanunta, kiran da ta ji innarsu na yi mata kan ta fito ta ci abinci ya sa ta tashi, bayan ta canza kaya ta nufi kofa ta fita. Su Leemarh na cikin yin hira Deen ya ce masu idan ba wani abu da za su yi su je su shirya su fita outing, sosai suka nuna jin daɗin hakan ba kamar mom ɗin su, ba tare da 6ata lokaci ba duk suka shiryo cikin kananun kaya har da shi Deen ɗin, ita mom gyale kawai ta ɗauro a saman kafaɗa suka fito, a cikin wata jeep za su fita, Omar ne ya zauna driver seat zai ja su, sai Deen a gefe, baya mom da Leemarh sai Sultan, Batool na manne jikin mom, a cikin wata ƙaramar mota security suka yi masu jagora. Duk wani babban park a Abuja sai da suka je, sun yi nishaɗi sosai wuraren ƙarfe shidda ya kai su wani babban mall ya ce kowa ya za6i abun da duk yake so, mom baki ya ƙi rufuwa dama burin ta ke nan a yi masu sai kuma nata kaɗai, siyayya bata wasa suka yi a mall ɗin ba har sai da hakan ya ja hankalin mutane kan su aka ankare da Deen akai ta yin hotuna da shi har da ma'aikatan wurin, sai bayan gama sallar magrib suka dawo gida a gajiye, a nan falo duk suka baje kayan suna sake daddubawa, suna haka dad ɗin su ya shigo ya iske su shima ya zauna yana ganin kayayyakin, cikin marairaicewa ya ce shine aka yi masa wayo aka tafi ba da shi ba kuma ba wanda ya tuna da shi balle a siyo masa komai, yadda ya yi maganar duk ya saka su dariya, Deen na murmushi ya ce mashi shima za su je sai ya za6i duk abun da yake so, dariya dad ya yi ya ce, "No son, ina maku wasa ne, ni bana buƙatar komai, nasu da ka siya masu ya isa kuma na ji daɗi sosai ina alfahari da kai, Allah Ya sa a mizanin kyautatama ƴan'uwa, Allah Ya shi albarka ya ƙara dafa maka." A tare duk suka amsa da Ameen, kiran sallar isha'i da aka fara yi ya tada su. Salma zaune a cikin ɗakinta bayan ta gama yin sallar issha, idanunta akan wayarta da tuni Sagir ya buɗe mata ya kuma nunnuna mata abubuwa, ya buɗe mata account a social media platforms ya kuma yi mata following handles ɗin Deen, dama ta iya abubuwa ba laifi duk da bata da waya, hakan ya sa abubuwan ba su yi mata wahalar iyawa ba, tun ɗazun take son kiran Deen ta yi ma shi ya ya koma amman ta kasa, haka nan take jin nauyin yin hakan, ta ɗan ɗauki lokaci tana wasi wasin yin hakan a cikin zuciyarta, ƙarshe ta yi ƙarfin halin kiran shi ta layin da ya kira Sagir, saida ta yi masa kira biyu amman bai ɗaga ba hakan ya sa ta ƙyale bata sake kira ba. Bayan dawowar su Deen masallaci suka zauna cin abinci gaba dayansu cikin nishaɗi, ko da suka kammala sake zama suka yi a babban falo suna hira a nan kuma Deen ya ce ma ƴan'uwan nashi in da mai wata buƙata ya sanar masa, Omar ne ya fara faɗin tashi buƙatar ya ce mota yake so a siya mashi a can ƙasar da yake karatu saboda sai dai ya yi order ɗin ride ko kuma ya yi amfani da ta abokai, Shiru Deen ya ɗan yi kafin ya ce mashi ya san tuƙi a irin ƙasashen suna da ka'idoji don haka ya bari zai je ya same shi idan ya koma sai ya siya mashi a yi komai, mom ta yi saurin cewa, "Yaushe har zaka samu zuwa, kai da baka da wani isasshen lokacin kanka, ina ganin kawai ka yi masa