Sashe 22
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ya Fahad, ka yi haƙuri idan abun da zan faɗa maka zai 6ata maka rai, duk da this is not the first time da na fara maka magana kan hakan, kuma wannan ba shine karo na ƙarshe ba, zan ci gaba da yi maka magana akan haka har zuwa ranar da Allah zai amsa addu'ana in ga ka daina. Please ya Fahad, you really should stop using drugs, a matsayin ka na medical doctor ka san irin illar da suke yi ma lafiyan mutum, hakan kuma yana da matuƙar haɗari ga aikin ka. Ba zan boye maka ba abun yana damuna sosai bro. I wouldn't want this to jeopardize your future." Fuska a yamutse ya ƙarasa magana, shiru Fahad ɗin ya yi bai tanka masa ba idanunsa na a rufe. Koma ya yi bacci bai sani ba? Tunanin da Deen ya yi ke nan, sai dai yana kokonton in ya yi bacci saboda ya san a duk sanda zai mashi magana kan shan ƙwayoyin da yake yi bai cika tanka masa ba sai dai ya yi shiru, wani lokacin kuma yana bashi amsa da zai daina in sha Allah Ya taya shi addua. Matsawa ya ƙara yi kusa da shi a hankali ya kwantar da kansa a saman jikinsa, Fahad da yana jin duk abubuwan da ya faɗa jin shi a jikinsa ya sa shi runtse idanunsa sosai, har cikin ransa bai jin dadin ganin yana saka mutane damuwa saboda abun da yake yi, saidai duk yadda ya so ya daina abun ya ci tura saboda ya kama mashi jiki sosai.
"Ya Fahad, I think wannan teacher ɗin fa ya haukace, ya bani wannan assignment din ba daidai ba, that's why inata wahala amman ya ƙi ya yi daidai."
Kaman daga sama Fahad ya tsinkayi muryar Deen a cikin kansa, duk da ya É—an fita hayyacinsa amman komai na zuwa mashi a cikin kansa kuma yana fahimta, É—an murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa tunowa da can baya lokacin suna yara, duk aka ba Deen assignment ya kasa yi sai ya iske shi ya yi mashi wannan maganar da ya yi, da yake lokacin Fahad É—in na yawan yi mashi faÉ—a kan yadda bai maida hankali sosai akan karatu ya fi mayar da hankali akan kwallo, to shine idan ya kasa yin assignment ya kawo mashi, gudun kada ya yi masa faÉ—an sai ya fake da cewa malami ya haukace ya bashi assignment ba daidai ba,
You are the one who has gone mad, shiyasa ka kasa yin shi yadda aka koya maka." Fahad É—in ne ya faÉ—a slowly, faffaÉ—an murmushi Deen ya saki ya ji dadin yadda ya bashi irin amsar da yake bashi a lokacin, duk da a yanzu bai kama mashi kunne ba kamar yadda yake mashi a lokacin, É—ago kai Deen ya yi yana kallon fuskarsa ya ce, "I thought ka yi bacci da na yi magana na ji baka ce komai ba." ÆŠan shiru Fahad din ya yi kaman ba zai ce komai ba,
"In sha Allah na kusa dainawa. Ka taya ni da addu'a Pls" Ya ji ya faÉ—a ba tare da ya juyo ba.
"Ina yi maka addu'a a koda yaushe, ba akan wannan ba kaɗai, kuma zan ci gaba da yi maka har ƙarshen rayuwana, In sha Allah." Kai ya ɗan jinjina masa tare da ce mashi ya gode.
"Ya Fahad yaushe zaka yi aure ne? Yakamata a ce zuwa yanzu kana da mata har ma mun samu baby, ka ga nima na samu wanda zan rinƙa nunawa a matsayin yaro na." Deen ya faɗa yana ɗan murmushi, ganin Fahad ɗin na kokarin juyowa ya sa shi gyara zaman sa, bin shi ya yi da kallo da lumsassun idanunsa a hankali ya furta, "Kai nike jira ka yi mani." Yar dariya Deen ya yi ya ce, "Serious, idan kana so sai in yi maka, ko gobe ma lafiya lau za a iya ɗaura maka aure. Who's the girl you want to marry?" Hannu Fahad ya ɗan yarfa ya ce mashi babu, amman tun da shi ne zai mashi auren sai ya samo mashi matar,
"Samun matan ba matsala bane ai, na san akwai babes dake son ka, É—azun ma a wurin dinner ai na ga ka samu, a cikin gidan nan ma na ga alamun ka yi kasuwa..." Ya karasa yana sakin faffaÉ—an murmushi, shima Fahad É—an murmushi ne akan fuskarsa, ya fahimci akan Leemarh yake magana, bin shi kawai ya yi da kallo still idanunsa na É—an lumshewa yana buÉ—a su.
"Idan kana son Leemarh ka shirya ma auren ta let me know, zan sanar ma dad, tun da lafiya lau ta isa aure sai ta yi completing karatunta a gidan ka." Ɗan girgiza masa kai Fahad ya yi ya ce ba soyayya suke ba kawai shaƙuwa ce,
"Da alama dai so kake in riga ka yin aure tun da ni ina da wadda zan aura, ko kuma in ce wadda aka za6a mani in aura." Yadda ya ƙarasa maganar zaka fahimci abun ba da son ranshi bane, kallon shi kawai Fahad yake yi can ya ɗaga hannu ya dafa shi ya ce, "You should not worry about that, idan Allah bai ƙaddara ita ce matar da zaka aura ba baza ka aure ta ba."
"You're right. Idan ita Allah Ya za6a mani na kar6a, Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi." Amsa mashi Fahad ya yi da Amin, suka ɗan yi shiru kafin Fahad ya ce mashi ya je ya kwanta dare ya yi gashi ya ce gobe tare za su tafi, miƙewa ya yi ya nufi ɗaya bangaren gadon, yana cikin tafiya yake tambayar Fahad gobe zai je wurin aiki ne, amsa ya bashi da ya so ya yi sammako don ya fara tsayawa wurin aikin to amman tun da tare za su tafi hakan ba zai yuwu ba, zai kira ya ƙara bada uzuri kawai sai su wuce Funtua, Deen ya ce kada ya yi haka goben idan Allah Ya kaimu da wuri za su tafi sai su fara tsayawa wurin aikin nashi kafin su wuce Funtua, Fahad ya amsa da ok, daga haka suka kwanta bayan Deen ya yi masu addu'a gaba ɗaya. Lumshe ido ya yi yana tariyo abun da ya wakana tsakaninsa da mom, a ransa yake raya gara ma ya yi tafiyar sa Funtua ya san a can zai fi samun peace of mind.
_Bossladieswriters_
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 8
Bayan mom ɗin Deen ta koma hamshaƙin katafaren ɗakinta da ya sha royal furniture kai kace wani ɗakin ƴar hamshaƙan masu kuɗi ko masu sarauta ne, a bakin gadonta da ya sha lafiyayyar katifa da shimfidar zanen gado mai kyau ta zauna, hayewa ta ƙarasa yi sama ta zauna tare da jingine bayanta da kan gado sai faman cika take tamkar zata fashe, bata da wani buri a cikin ranta face ta ga ta raba tsakanin Deen da Fahad, sam ta tsani ta gan su tare gani take kamar juya mata ɗa Fahad ke yi yana cin dukiyarsa son rai, ta ɗauki tsawon minti talatin a haka tana ta faman yin tufka da warwara, jin motsin shigowar mutum ya sa ta ɗaga ido ta kallo kofar shigowa, dad ɗin su Deen ne ya shigo yana sanye riga da wando na bacci, ya fito a babban mutum, cikin ɗakin ya nufo idanunsa akanta yana kallonta da ɗan yanayin mamaki, tun ɗazu yana a part ɗinsa yana jiranta, har kiranta ya yi a waya ba a daɗe ba ta sanar da shi tana zuwa tana yin wani abu ne, da ya ji shiru shine yanzu ya biyo bayanta don har sake kiran wayarta ya yi bata ɗaga ba, ganinta zaune ba tare da tana yin wani abu ba ya sa shi yin mamaki. Daga bakin gadon ya tsaya yana kallonta ita kuma tun da ta kalle shi sau ɗaya ta kauda idonta gefe, daga yanayin fuskarta ya gane tana cikin fushi, jikinsa ne ya ɗan yi sanyi don ya san idan tana a cikin irin halin bata saurarar shi, ƙoƙarin zama ya yi daga gefenta idonsa akanta,
"Gimbiyata, ashe kina nan zaune kin ce mani kina zuwa ina ta jira." Ko kallon shi bata yi ba sai ma ta ƙara juyar da fuska tare da ɗan tura baki, jimm ya yi yana ta kallonta, ya san in dai yana son ta saukko to dole sai ya lalla6ata,
"Ya aka yi ne my love? Mi ya faru na ga bacin rai a tattare da ke bacin bada jimawa ba mun yi magana lafiya lau. Pls tell me idan wata damuwar ce zan yi maganinta, in sha Allah." Ya ƙarasa maganar cike da tabbatar mata da abun da ya faɗa, sai lokacin ta ɗan juyo ta kalle shi amman bata saki fuska ba, hannu ya kai ya kamo nata ɗaya ta sigar lallashi ya ce mata yana jin ta minene matsalan,
"Deen ne! Ban san mike damun shi ba, sam bai jin maganata, ban isa in nuna mashi abun da nike ganin shine daidai ba ya ji, abun da ransa ke so shine zai yi!" Ta ƙarasa a hasale.