← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 197

Sashe 113

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali wata mota mai kyau ta ƙaraso bakin tangamemen gate ɗin gidan ta tsaya ba tare da an kashe motar ba, ƙofar side ɗin driver aka buɗe wani gajeran baƙin babban mutum mai ɗan jiki da tumbi, fuskarsa sai naso take a haka kuma daga yanayin motar ka san a Ac ya fito, zagayowa ya yi ɗayan 6angaren da sauri tumbinsa har ɗan rawa yake yi, buɗe ƙofar gaba ya yi fuskarsa da ɗan murmushi ya tsaya yana riƙe da kofar alamar wani zai fito, sai da aka ɗan ɗauki lokaci kafin aka zuro wata ƙafa waje wadda da gani ta mace ce fara fat da ita, ƙafar na maƙale da sarƙar ƙafa wadda da gani ta zinari ce, ƙafar na sanye da wasu matsiyatan takalma masu ɗan banzan tsini irin masu igiya da ake ɗaurewa, daga baya aka zuro da ɗayar ƙafar kafin mai ƙafafun ta ƙarasa fitowa, Ma sha Allah! wata kyakkyawar mata ce wadda koda mutane marasa cikakkar lafiyar idanu suka kalle ta sai sun shaida kyawunta, fara ce sol tana da kyawun fuska sosai, a yanayin halitta doguwa ce mai ɗan dogon wuya, sanye take da wata matsiyaciyar straight gown ta haɗaɗɗan lace da duwatsun jiki ke sakin wani irin kyalli, rigar ta bayyana dirinta wanda yake mai matuƙar ɗaukar hankali, daga wurin ƙugunta ya buɗe sosai yayin da cikinta yake a ɗame kai ka ce bata cin abinci, ƙirjinta a cike yake fam cleavage din ta a bayyane fatar wurin fara tass da ita, saman kanta ta soke ɗauri da ya zauna ɗas, walwatacciyar sumar kanta da ta fi kama da tata daga yanayin halittarta wadda take baƙa wuluk mai santsi ta zubo da ita ta gaba gefe guda, yayin da sauran ke a zube bayanta wanda tsawon sumar ya wuce kafaɗunta ta kawo har ƙirjinta, tun daga kan kunnanta zuwa wuyanta da sarƙar da ke a maƙale a ƙafarta guda da kuma nose ring da ke a maƙale a gefen hancinta, sai zobban dake a wasu yatsun hannun damanta da hagu gaba ɗaya duk zinari ne, sam babu mayafi a jikinta sai wata yar ƙumbulallar purse da take riƙe da wadda da gani mahaɗin takalman kafafunta ce, wani irin masifaffan ƙamshi take bazawa ta ko ina dai ta cika mace, sai dai a yanayin shigarta ba zaka iya tantance shin musulma ce ko kuwa ba musulma ba? Bayan ta fito ta kalli mutumin da ke a tsaye kamar an dasa shi da idanunta da suke farare tass da su masu kaifi, cikin salo kamar bata son yin magana ta furta, "Thank you." Washe baki ya yi ya ce, "No ai ni yakamata in yi godiya ranki ya daɗe." Wani mayen kallo mai tada tsigar jiki ta sakar masa, ganin tana niyyar tafiya ya yi saurin cewa, "Am..ranki ya daɗe baki bani phone number ɗin naki ba da kika ce zamu yi magana daga baya." Ɗan juya idanunta ta yi ta ce ok ta manta, buɗe purse ɗin hannunta ta yi ta fiddo da wayar ta latest iphone ta miƙa masa yatsun hannunta zara-zara masu ɗauke da zaƙo- zaƙon ƙumbuna dake shafe da jan farce kalar da ya hau da kayanta, da gani ta ƙara ƙumbunan kanti, ce mashi ta yi ya saka mata number ɗinsa, still baki a washe ya ce a'a ta bashi tata lambar ba sai ta yi wahalar kira ba, ta ce masa kada ya ji komai ya bata tashi lambar, amsar wayar ya yi wadda ita kanta ƙamshi take saki, bayan ya saka ya miƙa mata fuskarsa da ɗan alamun kokonton kiran nasa da ta ce zata yi ya ce,"pls ranki ya daɗe ki cika alkawari kada a shanya ni in ta jira koma a manta da ni." Wani ɗan murmushin gefe ta yi ta ce, "Kar ka damu." Ta yi maganar tare da ɗan ɗage gira, daga haka ta nufi gate ɗin tana taku tamkar wata tarwaɗa yayin da tsagar bayan rigarta ta kawo har kan layin bayan gwiwowinta, shi kuwa mutumin bin ta ya yi da wani mayen kallo tamkar zai lashe ta, tana tunkarar gate ɗin hannunta na latsa wayarta ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga goge lambar da mutumin ya saka mata, a cikin ranta tana raya ya yi zaton ita ɗin haka take da arha, daga ya samu ta shiga motar sa ya kawo ta shike nan zai zira jiki, bai san ita tana da test a maza ba, ba kowa ne take iya yin hulɗa da shi ba, balle shi da gani ba wani wayayye bane can da suffarsa kamar wani bijimin sa, sannan da gani ba wasu shahararrun kuɗi ne da shi ba, kawai don bata son hawa taxi ya sa lokacin da ya yi mata tayin shiga motar bayan ta fito daga hotel ɗin da take ta amince har ya ɗauko ta, shi kuwa mutumin ya yi tsaye kamar gaula har sai da ya ga ta shige gidan da ya ajiye ta ta ƙaramar ƙofa sannan ya koma cikin mota a ransa yana mai fatar ta kira sa ɗin sannan haƙarsa kanta ta cim ma ruwa, lalle da ba ƙaramin morewa zai yi ba, ya ƙarasa tunanin tare da ɗan cije lebansa, tana shiga cikin gidan suka kusa yin karo da wani mutumi mai sanye da kayan jami'an tsaro da ke niyyar fita waje, ta ra6a ta gefensa zata wuce ba tare da ta ko kalle sa ba, da sauri ya dakatar da ita da cewa, "Sannu hajiya," Ta yi masa wani kallo ta furta, "Kai ma haka." Tana niyyar wucewa ya sake cewa, "Wa kike nema ne?" Dakatawa ta yi tana mashi wani kallon rashin arziƙi ta gefe, ɗage masa gira ta yi ta ce, "Dole sai na sanar da kai wurin wanda zan je?" Shi bai ma yi zaton zai ji hausa ta fito raɗam daga bakinta ba, ɗan murmushi ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya ce, "Tabbas, don saboda haka ne aka ɗauke ni aiki ai." Ɗan yamutsa baki ta yi ta ce, "To kuwa sai dai shiga ta ta yi sanadiyyar korar ka daga aikin idan sai na sanar ma wurin wanda na zo." Ƙoƙarin wucewa ciki ta fara yi ya yi saurin shan gabanta ya ce, "Hajiya abun duk ba na faɗa bane, amman dole sai kin sanar mani wurin wa kika zo hakan aiki nane." Wani mugun kallo ta jefa masa, 6acin rai ya bayyana a saman fuskarta a fusace ta ce, "Zaka kauce daga gaba na ko sai ka ji tafin hannu na a saman kuncin ka!" Mamaki ne ya bayyana akan fuskar officer ɗin jin abun da ta ce wai shi za ta mara, wanda tun da yake aiki bai taba fuskantar irin wannan humiliation ɗin ba, ɗan jinjina kai ya yi da ɗan murmushi ya ce, "Mari kuma??" Ta ɗage gira ta ce, "Ko kana kokonton hakan ne?" Kafin ya bata amsa wani officer ya ƙaraso wurin daga cikin gidan, yana ganin matar ya washe baki ya ce, "Barka da zuwa ranki shi daɗe." Sauke idanunta ta yi a kansa fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa masa, ya ce, "Hajiya ki shiga mana." Ya faɗa yana nuna cikin gidan, tana kallon shi ta nuna ɗayan officer da ya dakatar da ita ta ce, "Wannan baƙo ne a nan?" Ya bata amsa da eh bai daɗe sosai da fara aiki ba, wani kallo ta yi masa ta ce, "Be careful, idan ba haka ba aikin ka zai su6uce maka a cikin sauƙi." Ta ɗan haɗe yatsunta ya yi sauti daga haka ta kaɗa kai ta nufi cikin gidan duk suka bita da kallo, juyowa ɗayan officer ɗin ya yi ya kalli abokin aikinsa ya ce, "Mi ka yi mata ne." Dan tabe baki ya yi ya ce, "Mi na yi mata kuwa, kawai don na ce sai ta sanar mani wurin wanda ta zo, shine har da cewa wai zata mare ni." Dariya wanccan ya saka ya ce, "To kai ma baka ga kamaninta da hajiyar gidan bane?" Ya ce, "To ko na gani ni dai ba aikina na yi ba, ko kuwa don tana kama da hajiya daga zuwanta sai kawai na ƙyale ta ta shiga bacin ba saninta na yi ba. Kawai don mutum na aiki a ƙarƙashin masu kuɗi ko mulki sai kowa nashi ma ya nemi taka shi." Wanccan da ke ƴar dariya ya ce to ya za su yi tun da ƙasar tasu ce, wajen gate ɗin suka fita suka zauna a wurin da suke zama, wanccan officer ɗin da maganar marin da aka ce za a yi masa ta tsaya masa a rai ya ce, "To su duk dangin hajiyar haka suke basu da mutunci?" Dariya ɗayan ya yi ya ce, "Wallahi kusan haka, ni dai duk wanda na sani suna zuwa gidan nan duk basu da mutunci." Tabe baki ya yi ya ce, "Allah Ya kyauta, koda yake abun ne ya yi masu yawa dole su rinƙa taka mutane yadda suka so, ga kyau ga kuɗi, yanzu ji dai wannan kamar ita ta yi kanta, saidai da gani ba tarbiyya, wannan shigar da ta yi wa zai ce musulma ce don Allah." Ɗayan ya ce, "Haka ne, itama hajiyar gidan baka ga yadda take ba masha Allah." Baƙon officer din ya sake cewa, "Yanzu ita wanccan ɗin budurwa ce ko bazawara?" Dariya ɗayan ya yi ya ce, "To wllh ban sani ba haka dai nike ganinta duk da tana daɗewa ma kafin ta zo, amman da gani ai ba sai an faɗa ba kasan ba matar aure bace, sai dai budurwa ce ko bazawara Allah masani. Ni in da zan samu waccan ai har aikina ina iya haƙura da shi wllh." Wani kallo baƙon officer ya yi masa kafin yay ƴar dariya ya ce, "To da wannan aikin naka ma waccan ba iya tarayya zata yi da kai ba balle kuma a ce baka da aikin." Gaba ɗaya suka saka dariya. Kai tsaye ta shiga cikin falon ta tsaya a tsakiya inda kujeru suke tana latsa wayarta, ta ɗan ɗauki lokaci a haka kafin wata ƴar matashiyar mace ta shigo cikin falon, hango baƙuwar da ke a cikin falon ya sa ta nufo ta, daga ɗan gabanta ta tsaya cikin hausarta da
Chapter 113 · 0% Book details