← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 197

Sashe 61

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sallar issha su Imrana na a ƙofar gida wurin tuyan awara shi da Hamza, ƙamshin da ya cika ma Imrana hanci ne ya sa shi saurin ɗagowa don ya gane irin ƙamshin mutumin da ya zo rannan har ya basu kuɗi ne, aikuwa shi ɗin ya hango a tsaye ɗan gaba da su, da sauri ya miƙe ya nufe shi ya tsaya daga gaban shi ya ce, "Ina wuni, awaran za a baka?" Kai Deen ya ɗan jinjina masa yana kallon sa yau ma fuskarsa na rufe da nose mask, "To ta nawa za a baka?" Imrana ya tambaya, shiru ya yi bai ce masa komai ba, ganin haka ya sa Imrana cewa, "Ko in kira maka yaya Salma?" Sai lokacin ya ɗan girgiza masa kai, hannu ya kai cikin aljihun wandon jeans din sa ya fiddo kuɗi ya miƙa masa, da sauri Imrana ya miƙo hannu har da ɗan kakka6e su kafin ya amsa, waro ido ya yi ganin kuɗin masu yawa, a ɗan ruɗe ya ce, "Ai awaran bata kai ta wannan uban kuɗin ba, duka ma wadda ta rage bata wuce ta dubu ɗaya ba fa." Har sai da ya sa Deen yin murmushi ta cikin mask ɗin ganin reaction din da fuskarsa ta nuna, hannu ya kai ya ɗan zame mask ɗin calmly ya ce masa ya kai kuɗin gida awaran da ta rage a raba ma mutane, da sauri ya amsa da to ya juya zan nufi gida, daidai nan Salma ta fito tana ƙwala ma Imrana kira jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta yafa ƙaramin gyale a kai, da ƴar sassarfa ya nufe ta sam bata lura da Deen ba, yana zuwa gaban ta ya miƙa mata kuɗin ya ce, "Yaya Salma kin gani wannan mutumin da ya zo shekaran jiya ne ya sake dawowa ya bada wannan kuɗin ya ce in kai gida, kuma a raba ma mutane awaran da ta rage." Har sai da gabanta ya faɗi jin abun da ya ce, da sauri ta tambaye shi ina mutumin yake ya juya yana nuna mata Deen da har ya juya ya fara tafiya, bin shi da kallo ta yi a ranta tana mamakin yadda yau ma ya dawo ya basu kuɗi, haka nan sai kuma bata ji daɗin zuwan da ya yi ya iske suna yin awaran ba, wani tunani ne ya zo mata a rai da sauri ta bi bayan shi, tunanin yadda zata tsayar da shi ta yi don bai ma san ta biyo bayansa ba, "Ya Deen..." Kawai sai ji ta yi ta kira sunansa da ɗan ɗaga murya ba tare da ta shirya ma hakan ba, cak ta tsaya ganin ya dakata tare da juyowa, slowly ta ɗan matsa kamar mai tsoron ƙarasawa gaban sa, jim ya ɗan yi yana kallonta kafin ya kai hannu ya zame mask ɗin fuskarsa, da yake akwai wutar nepa wasu gidajen layin suna da hasken globe a gaban su hakan ya sa suna iya ganin fuskokin juna ta hasken da ya ɗan haska, tana kikkafta idanu ta ce, "Ina wuni.." Kai ya jinjina sai kuma ta ji ya ce, "How are u?" Ta amsa da, "Lafiya lau," Kai ya ƙara jinjinawa suka ɗan yi shiru, wani irin ƙwarjini yake mata hakan ya sa ta rasa mi zata ce masa, "Any problem?" Ta ji ya sake tambaya, cikin ƴar in ina ta ce, "Dama yanzu ƙanina ya nuna mani kuɗi ya ce kai ka bashi ya kai gida..." Ya ɗaga mata kai alamar eh, "An gode Allah Ya saka da alkhairi....da innarmu ma ta ce kada a yi awaran yau, dama jiya bamu yi ba saboda wanccan kuɗin da ka bamu, ni ce na ce mata ai da ka bamu kuɗin ba cewa ka yi mu daina yin awaran ba..ita bata so a yi ba ni ce na nuna ina so a yi.." Cike da kama kai ta yi maganar ita kanta bata ma san miye amfanin yin wannan maganan ba, ɗan murmushi ta ga ya yi calmly ya ce, "Yea, ba don ku daina bane, it's just a gift." Ɗaga kai ta yi itama yanayin fuskarta kaman zata yi murmushi ta sake cewa, "Mun gode Allah Ya ƙara buɗi na alkhairi." "Ameen.." Ya amsa ƙasa-ƙasa, shiru suka ɗan ƙara yi kafin ta ji ya ce shike nan zai iya tafiya, da sauri ta ɗaga masa kai daga haka ya juya yana ƙoƙarin mayar da mask din, har zai fara tafiya da sauri ta ce, "Ko in zubo maka awaran?" Juyowa ya yi ya kalle ta ya girgiza mata kai ta cikin mask ɗin ta ji ya ce, "Thank you." daga haka ya juya ya ci gaba da tafiya cike da natsuwa, tsaye ta yi a wurin tana ta kallon sa a cikin ranta ba ƙaramin mamaki yake bata ba, juyawa ta yi bayan ta ga ya tsallaka hanya ta nufi gida, tana shiga ta ga innarsu a tsaye a bakin baranda tana riƙe da kuɗin da alama shigowar ta dama take jira, a sanyaye Salma ta ƙarasa wurinta, da alamun mamaki ta ce, "Salma ashe yau ma zuwa ya yi ya bada kuɗin kuma kamar na shekaran jiya yauma dubu ɗari biyu ne." Kai Salma ta ɗaga ta ce, "Nima ina fita Imrana ya nuna mani lokacin bai daɗe da ya bashi kuɗin ba don bai ma kai ga barin wurin ba, shi ne na bi bayansa na yi masa godiya." Shiru innarsu ta ɗan yi kafin ta ce,"Duk sai na ji wani iri wllh, kada a ce ganin ana yin awaran ne ya sa shi sake zuwa ya bada kuɗin." Itama Salma da irin tunanin a cikin ranta, sai kuma ta ce, "Ai bayan na yi masa godiyar sai da na faɗa masa baki so a yi awaran bama ni ce na ce da ya bamu kuɗin bai ce kada mu yi sana'ar ba, shi ne sai ya ce eh kawai matsayin kyauta ne ya bamu." Jinjina kai innarsu ta yi har ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, "An gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi. Gaskiya mutumin yana da kirki ba kaɗan ba kuma bashi da girman kai wllh, Allah Ya kara masa ɗaukaka." Salma ta amsa da Amin,
"Inna yanzu a je a rabar da awaran?" Imrana ya tambaya, da sauri ta bashi amsa da eh, kallon Salma ta yi ta ce, "To shi bai son awaran? Na ji hajiya ta ce kaman yana son ta." Salma ta ce, "Ai sai da na tambaye shi in zubo masa awaran ya ce a'a." Ƴar dariya innarsu ta yi, ta ce, "In ban da abun ki Salma ta ya zaki tambaye sa haka, a tunanin ki zaki zubo masa abu ne ya riƙe ya tafi da shi?" Shiru ta yi tana ɗan murmushi itama sai yanzu ta gane shirmen da ta yi,

"Yanzu kina ganin ko a haɗa masa sai ki je ki kai masa?" Kai ta ɗaga ta ce eh, "To yi sauri ki je ki ga idan Imrana bai ƙarasa soya ɗanyan da ta rage ba sai ki ɗebo nan mu haɗa masa da kan mu, dama akwai sauran cefane sai a yi masa yar sauce ko?" Da sauri Salma ta ce eh ta nufi hanyar fita, without wasting time suka shiga haɗa masa awaran ita da innarsu, suna cikin yin aikin ne Salma ta roƙi innarsu idan zai yuwu a cikin kuɗin da aka ƙara basu a bada a yi ma su Habu ɗinkin makaranta ko da ba su duka ba tun da suna da yawa, murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce mata kamar ta shiga zuciyarta itama hakan ya zo mata a rai, idan babansu ya dawo zata yi mashi maganar sai a ga abun da za a ba su ya ba baban su Habu ɗin a siya masu kayan makarantar, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma Salma ba. Ba tare da an ɗauki lokaci ba suka kammala, awara mai ƙwai da sauce suka haɗa gwanin kyau a ido sai ƙamshi ke tashi, har da ɗan coleslaw suka haɗa dama suna da mayonnaise, suna gamawa Salma ta je ta canza kaya duk da yau bata zauna sosai wurin tuyan awaran ba duk Imrana ne ya yi amman saboda aikin awaran da suka gama ya sa take ganin kaman kayan jikinta sun yi dauɗa, doguwar rigar material mai mayafi ta sako wanda kayan na daga cikin irin waɗanda auntynta Kubra ke aiko mata daga Kaduna, har da turare ta ɗan faffesa duk don ta fito fess yadda Deen ɗin zai ci awaran, don a yadda yake ta tabbatar ba zai rasa ƙyanƙyami ba, bayan ta fito innarsu ta fiddo mata da awaran da aka zuba a cikin wata ƴar madaidaiciyar kula mai kyau, daga cikinta akwai irin yar farar roba mai marfi a nan aka zuba sauce ɗin, sai coleslaw ɗin aka sa a cikin wata ƴar farar roba irin ta takeaway ana ganin abun da ke a ciki,
Chapter 61 · 0% Book details