← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 197

Sashe 71

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Salma ta yi ma hajiya sallama, tana fitowa harabar gidan ta hango Deen a zaune saman plastic chair da wasu mutane za su kai su biyar a gefe wurin parking space, nufar gate ta yi tana tafiya a nutse, gab da zata isa bakin gate ta ji kaman ana mata magana hakan ya sa ta waiga, daga cikin mutanen da yake zaune da su wani ya yi mata nuni da ta je da hannu, tunkarar su ta yi kanta a ƙasa tana kusa zuwa inda suke Deen ya taso ya nufo ta, daga gaban shi ta tsaya tana kallonsa da ɗan murmushi, hannu ya kai cikin aljihun jeans ɗin sa ya fiddo kuɗi ƴan dubu masu yawa ya miƙo mata, kallon kuɗin ta yi kafin ta ɗago ta kalle sa da alamun rashin fahimta, calmly ya ce, "For the..." Shiru ya ɗan yi alamun sunan farar ya shige masa sai dai ya idasa faɗa da turanci, ta ɗan girgiza masa kai ta ce ai kyauta ta kawo mashi, shiru ya ɗan yi fuskarsa a sake ita kuma tana ta ɗan murmushi, "Ai ba a yin business haka, idan kina ba mutane kyauta how will you make profit?" Ya faɗa idonsa cikin nata, still murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Ai ko wanda na bada ɗin ma riba ne." Ɗan murmushi ya yi ya ce ok ta amsa sai ta ƙara improving business ɗin, bin sa da kallon rashin fahimtar abun da yake nufi ta yi, ya gane hakan ya ce mata yana nufin kamar bangaren branding da packaging yadda business ɗin nata zai fi kar6uwa, shiru ta ɗan yi tana kallon kuɗin, ya ce ta amsa ta bar shi da abu a hannu, kallon shi ta yi tana kikkafta idanu ta ce, "To ka rage kuɗin sun yi yawa." Kai kawai ya girgiza mata alamar ba zai rage ba, ɗan langa6ar da kai ta yi tare da ɗan yamutsa fuska gyalenta ya zame baya, hannu ta kai tana gyarawa cikin marairaicewa ta ce masa don Allah Ya rage, ya yi mata wani kallo da ya sa ta yi saurin sauke idonta ƙasa, bin doguwar farar ƙafarsa dake sanye cikin baƙin LV designer sandal ta yi da kallo, ɗagowa ta yi a hankali ta kai hannu ta amshi kuɗin tare da yi masa godiya, ba tare da ya ce komai ba ya juya ya koma wurin mutanen ta bisa da kallo kafin ta juya ta tafi. Washegari da rana bayan Salma ta dawo daga makaranta, tana zaune a cikin baranda tana cin abinci, fitowa innarsu ta yi daga cikin daki ta zauna daga gefenta tana mata murmushi yayin da itama Salma shine akan fuskarta, "Dazun hajiya ta kira tana son awara." Innarsu ta fada, Salma ta gyada mata kai tana murmushi, "Wai nikam kwana biyu mutumin ki Habu bai leko ba, ina ga tun ranar juma'a bai kara shigowa ba." Bayan Salma ta cinye abincin bakinta ta ce, "Wllh nima yana raina, wama ya sani ko saboda abun da Imrana ya yi masa ne ranar shi ya sa bai sake zuwa ba." Innarsu ta ce, "Anya, ban tunanin haka, tun da ai ba lokacin ya fara masa haka ba kuma hakan bai hana sa sake dawowa." Gyada kai Salma ta yi alamar haka ne, innar ta ce Allah Ya sa to lafiya rashin zuwan nasa, "Bari idan na gama cin abinci zan je gidansu in duba ko lafiya." Salma ta fada. Kamar yadda ta fada bayan ta gama ko uniform din jikinta bata cire ba ta wuce gidansu Habu, da sallama ta shiga gidan wanda daga yanayin gidan kana gani kasan gidan iyali ne, wata yar matashiyar budurwa dake duke tana yin wanki a can gefe ta dago da murmushi tana amsa ma Salma kafin ta gaishe ta, Salma ta tambaye ta innarsu ta ce mata tana a daki, bayan ta shiga ciki sai da ta leka dakunan abokan zaman innar su Habu duk ta gaisa da su kafin ta wuce dakin su Habu, "Ah Salma ce, shigo mana." Innarsu Habu dake kishingide a bakin gado ta fada tana kokarin tashi zaune bayan Salma ta yi sallama, nuna mata bakin gado ta yi tace ta zauna, Salma bata zauna ba idanunta akan Habu dake kwance saman shimfida a ƙasa, da sauri ta nufe shi ta duƙa tare da kai hannu ta taba fuskarsa a hankali ya buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, sai fitar da numfashi yake a wahalce, da yanayin ruɗu ta ɗaga kai ta kalli innarsu ta ce, "Innarsu Habu bai lafiya ne?" Fuskarta a yamutse cike da damuwa ta ce, "Wllh Salma baya lafiya kusan fin sati." Salma ta ce, "Amman ya je gidanmu ranar juma'a." ta ce, "Eh, ai farko a tsaitsaye ya fara yin ciwon kafin ya kwantar da shi haka." Tambayar abun da ke damunsa Salma ta yi innar ta bata amsa daga zazzabi dai abun ya yi tsanani haka, "To innarsu Habu ba a kai shi asibiti bane?" Hannu ta ɗan yarfa ta ce mata an kai shi chemist aka bashi magunguna daga baya da jikin ya yi tsanani har da ƙarin ruwa mai chemist ɗin ya zo gida ya saka masa amman jikin dai ba sauƙi abun sai ƙara gaba yake, cike da damuwa Salma ta kalli Habu wanda duk ya rame ƙasusuwan jikinsa duk sun fito, "Innar su Habu ai da an kai shi babban asibiti an duba shi sosai." Ɗan juyar da kai ta yi nan da nan idanuwanta suka canza cikin karewar murya ta ce, "Wllh Salma nima hakan na so to amman ba hali, ko ƙarin ruwan da aka saka masa bashin kuɗin na samo, na yi ma babansu magana shima ya ce mani bai da kuɗi sai ya samu, kuma dama ba Habun ne kaɗai bai lafiya ba su ukku ne kwance kawai dai ciwon na shi ya fi yin tsanani..." Ɗan dakatawa ta yi tana share ƙwallan da suka tarun mata, ta ci gaba, "Abun ne sai addu'a kawai Salma, har bashi na nema amman ban samu ba kowa sai ya ce bai da kuɗi, waɗanda ke ɗan baka har sun zo sun fara gajiya saboda rashin cika magana. Wllh har bincikawa na yi ko zan samu abun da zan sayar in kai sa asibitin amman babu wani abun kirki duk na siyar saboda halin rayuwa." Salma da tausayi idanunta har sun kawo ruwa, cike da damuwa tace, "Amman innarsu Habu da kin yi ma innarmu magana na san zaki samu kuɗin a wurinta." Ɗan rausayar da kai ta yi ta ce, "Wllh Salma kunya da nauyi ya sa ban je wurinta ba, ganin duka ranar lahadi babanku ya ba babansu Habu kuɗi masu yawa ya ce a mayar da su makaranta, kuma yana bashi kuɗin bai tsaya 6ata lokaci ba gudun kada su salwanta don da an samu kuɗi ta abinci ake, hakan ya sa ya je ya siya masu duk abubuwan makarantar da ake buƙata, har ya samu ragowar da muka ɗan ci abinci kwana biyu." Shiru Salma ta yi idanunta akan Habu da ya kama mata hannu, cike da tausayawa ta ce, "Sannu Habu ɗan gidana, Allah Ya baka lafiya." Kai kawai ya ɗaga mata, miƙewa Salma ta yi ta ce ma innarsu Habu tana zuwa ta nufi ƙofa ta fita. Sosai innarsu Salma ta shiga damuwa jin halin da ta zo ta faɗi mata Habu na ciki, sam bata ji daɗi ba da innar tasu bata zo ta sanar masu ba har jikin nasa ya yi tsanani haka, shiryawa Salma ta yi cikin doguwar rigar material ta ɗaura yar madaidaiciyar baƙar hijab roba, innarsu dake kallonta bayan ta fito ta tambaye ta wane asibitin zata kai shi ta ce mata babban asibiti, shiru ta yi tana kallonta ganin duk ta shiga damuwa dama haka take da tausayi, tana dawowa gidan bayan ta sanar ma innarsu rashin lafiyan Habu ɗin ta ce zata je ta kai shi asibiti, innar tasu ta ce bari ta ɗauko mata kuɗi, Salma ta ce ta bari ta riga ta ɗauka cikin wanda Deen ya bata, wayarta ta ba Salma ta ce mata ta je da ita duk halin da ake ciki sai ta kira ko da Sagir ne ta sanar masa ta ce mata to tare da ce mata sai ta dawo. Rungume Habu ta yi bayan ta shiga keke nepep sun hau hanya, lokaci bayan lokaci take ɗago fuskarsa ta ce masa sannu ya ɗaga mata kai, bayan sun yi nisa ta ga ya juyo yana ta kallonta, ta yi mashi ɗan murmushi ta ce, "Sannu Habu." Ya ɗaga mata kai sai kuma ta ji daƙyar ya ce mata yunwa yake ji, tambayar shi ta yi to mi yake son ci ya ce mata yoghurt, ɗago kai ta yi ta ce ma mai keken, "Malam don Allah idan ka ga wurin da ake siyar da yoghurt ka ɗan tsaya da mu zan siya masa." Mutumin ya amsa mata da to, yar tafiya kaɗan suka ƙara ya tsaya da su bakin wani shago Salma ta siyo masa yoghurt ɗin na roba, bayan sun ci gaba da tafiya da kanta ta rinƙa bashi a baki yana sha, "Ke ma ki sha..." Ya faɗa yana nishi bayan ya sha da ɗan yawa, tana murmushi ta ce mashi ta ƙoshi ya shanye duka, ya ɗaga mata kai ta ci gaba da bashi. Bayan sun isa babban asibiti cikin sa'a Salma ta samu ganin likita da wuri da taimakon wata nurse mai kirki, awo aka rubuta mata shima ba 6ata lokaci aka yi mata don mai yin awon yana ganin Salma ya ƙyasa, bayan ta kawo ma likitan result nan ya tabbatar mata da typhoid da malaria ne suka kama shi sosai don har bai da jini a jikinsa, nan ya buƙaci jini leda biyu da za a saka masa da gaggawa, Salma duk ta ruɗe ta ce a saka mashi nata idan zai yi, likitan mai kirki yana murmushi ya ce mata an fi buƙatar namiji ya bada, ƙarshe Sagir ta kira ta sanar da shi halin da ake ciki ya tambaye ta irin jinin Habu ɗin ta faɗa masa, ya ce lafiya lau zai iya basa, jin leda biyu ake so ya ce mata bari ya zo tare da abokinsa
Chapter 71 · 0% Book details