Sashe 97
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Deen bai wani ci abincin da yawa ba ya ce ya ƙoshi, Ammi ta ce, "Amman ai baka wani ci na kirki ba kuma don kai aka yi shi." Da ɗan murmushi ya ce mata ya ci abinci a hotel kafin ya taho, ta ɗan 6ata rai ta ce, "To ai da gangan ka ci abinci tun da ka san nan dole za a shirya maka ko, kuma yaushe rabon ka da nan ɗin fisabillillah, kamata ya yi a ce ka sauka anan amman baka yi hakan ba, kuma sannan abincin ma ka ƙi sakin jiki ka ci, ta ya zamu ji daɗin hakan." Haƙuri ya bata ya ce ba shine ya kama hotel din ba, ya yi mata bayani, Bash ma ya ɗaura da yi masu bayani game da gasar ƙwallon da aka shirya za a yi, ta nuna ta fahimta tare da yi mashi fatan nasara, kakansa ma da har lokacin yana zaune a falon ya yi masa addu'ar nasara, Bash ya ce ai ya ga bashi kaɗai ya zo ba har da jami'ai sai a kai masu abincin su ma, Ammi ta sa Aseey ta kira mai gadi ya zo ya ɗauka masu bayan an ƙara masu abincin, mom ɗin Deen ce ta kira Ammi tana tambayar ta ko Deen ya zo ta ce mata eh gasu nan ma tare da shi a falo har ya ci abinci duk da bai ma wani ci sosai ba wai ya riga ya ci a otel, bayan sun gama wayar sai ga kiran mom ɗin tashi ya shigo wayar shi shima, ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, abun da ya zo masa a rai zata ce masa shi ɗin ta jaddada masa wato ya tambaye su buƙatun su ya biya masu ya amsa mata da to, bayan gama yin wayar a nutse ya ce masu yana son tafiya don nan da dan lokaci za su fara wasa, Ammi ta ce,"To amman dai zaka dawo ko?" Ya amsa mata da eh, duk da bai da tabbacin hakan don yana son zuwa gidan ƙanwar dad ɗinsa wato Aunty Murja da ke nan, ce masu ya yi su faɗi buƙatun da suke da su aikuwa zo ka ga washe baki da gyara zama, Ammi ce ta fara faɗin buƙatar ta, farko ta ce kuɗi take so akwai wani fili da aka mata talla tana son siya, sannan tana son zata koma wani ƙwararren private hospital a duba ta da kyau rashin lafiyan da take yawan yi to asibitin yana da tsada sosai, sannan tana son ya bata jari tana son fara yin kasuwanci mai ƙarfi yadda zata rinƙa yin wasu buƙatun ba sai an ta takura masa da mom ɗin shi ba, a ƙalla ta nuna tana buƙatar kusan miliyan ashirin, gashi duk buƙatun ma kame kame ne, Deen ya ce mi zai hana ta je Abuja maganar binciken lafiyarta tun da akwai asibitoci masu ƙwararrun likitoci, tarar hanzarinsa ta yi da sauri ta ce ai wannan asibitin ma da take son zuwa nan likitocin ƙwararru ne don har da turawa ba sai ta je har Abuja ba ya amsa mata da to, da aka zo kan Abba yana washe baki ya ce yana buƙatar kuɗi wanda zai yi gyaran gidan har da bene yake son a ɗaura, sannan kuma yana son zai je kasar su ziyarar dangin su don ya daɗe bai je ba kuma idan ya je zai yi masu alkhairi, dangin da tuni ya yafe su, taƙamaimai ma bai san inda wasu dangin nasu suke ba tun da shima a nan aka haife sa, ƙarshe ya ce motarsa ta tsufa tana bashi matsala yana son a canza masa wata, shiru Deen ya yi yana kallonsa har ya gama magana, da kamar ya share amman kuma sai ya dake ya ce, "But kwanaki mom ta amshi kuɗi a hannuna ta ce zata turo ma Ammi a gyara gida, ko bata ba ku?" A tare Ammi da Abba suka kalli juna, daga kallon da yake mata zaka gane shi bai san ma da maganar ba, murmushin yaƙe Ammi ta shiga yi cike da kama kai ta ce, "Ah...eh tabbas an yi haka, to amman kuma wani uzuri na kuɗi ya gifta lokaci, ka san uzururrukan rayuwa basu ƙarewa kuma ba shawara suke ba kafin su zo, dole da kuɗin aka yi amfani." Deen bai ce komai ba, Bashir ya gyara zama ya fara nashi bayanin, shima mota yake son a canza mashi ya faɗi kalar wadda yake so, sannan ya ce shagon shi na sayar da kayan su atamfofi da shaddoji da laces wanda Deen ɗin ne ya bashi jarin da ya buɗe shi, wai duk ya yi ƙasa saboda buƙatun yau da kullum da yake yi ma kansa da gidan nasu, gashi har yau karatun shi bai kammala ba balle ya samu aiki, karatun da shekara da shekaru ya fara shi amman gamawa ta gagara, kallon ƙarya mutum ke shirgawa iyayen nashi suka shiga bin sa da shi, mutumin da da ƙyar suke amsar kuɗi a hannunsa suma ba masu yawa ba, ba abun da ya saka a gaba sai sharholiyar shi da mata duk akan su ya ƙarar da kayan shagon, gashi akwai son yin ƙarya cikin abokai, koda yaushe yana nuna shi ɗin wani ne yana tutiya da yayarsa tana auran ɗan majalisa a Abuja sannan ɗanta shahararren ɗan kwallon duniya ne, ga kuma wata yayar tasa da ke auren babban injiniyan fasaha da ya mallaki company a ƙasar waje. Shima babansu ba abun da ya saka a gaba sai neman mata da shaye-shaye duk anan yake 6annatar da kuɗi har caca yana yi, ku san duk halayyarsa ce Bash ya ɗauko, a 6angaren Ammin su kuwa ita wannan shahararriyar mai bin bokaye ce, komi ƙanƙantar matsala sai ta kai wurin boka, ita a wurinta ta yi imanin dukkanin hasken da take gani a rayuwarta to sanadiyyar aikin da ake mata ne, duk a wurin bokaye kuɗaɗenta ke tafiya, gashi ta iya wulaƙanta mutane musamman talaka, sannan akwai ta da son nuna ita wata ce, da tsiya ta kutsa kanta tana abota da matan masu kuɗi da manyan ƴan siyasa da kuma mata ƴan duniya. Da aka zo kan Aseeya ta faɗi abun da take so cewa ta yi sabuwar iphone da aka yi take so ya canza mata sannan wai duk kayanta sun tsufa tana son ta yi canjin wardrobe, Ammin su har da ce mata ita ke nan buƙatar da zata faɗa ga harkar ɗawainiyar karatun ta Aseey ɗin ta ce ta manta, bayan su da suke a gida sun gama faɗan buƙatun su har da na Adam autan su da baya nan a cewar su yana makaranta shima sai da aka zayyano nasa buƙatun, sannan Ammi ta ɗaga waya ta kira Nailah da suka ce itama ta yi tafiya, bayan ta sanar mata game da zuwan Deen ta ce ta faɗi buƙatar ta a sanar masa, ta saka aka ba Deen wayar suka gaisa ta yi mashi an zo lafiya, daga baya kai tsaye ta ce mashi miliyan goma take so ya tura mata zata yi wata buƙata ya amsa mata da ok, a ƙalla buƙatun da suka kawo masa sun yi na kusan miliyan ɗari, kuma bai isa ya ce ba zai yi ba ya san suma za su kafa hujja da abubuwan da ya je ya yi a Funtua tun da ya san sun gani, kuma zai fuskanci 6acin ran mom ɗin sa in bai yi ba, tambayar su ya yi a account ɗin wa za a saka kuɗin, da sauri su dukansu kowa ya ce a tura mashi a account ɗin sa sanin halin junan su akan kuɗi. Bayan ya sallame su ya yi masu sallama dukansu suka rako shi harabar gidan sai faman washe baki suke kakar su ta yanke saƙa an cika masu account da kuɗaɗe, shima maigadin su saida ya bashi kuɗi masu yawa ya yi ta masa godiya, ku san a tare Bash da Abbansu suka kai hannu cikin rawar jiki don su buɗe ma Deen mota, bayan ya shiga ya ƙara yi masu sallama suna ta yi masa godiya da addu'oi, Bash na ce mashi sai sun haɗu a stadium daga haka motocin suka bar harabar gidan. Deen na zauna a bayan mota ya ɗage kansa sama bayan sun hau hanya, sam bai ji komai ba da kuɗin da ya basu, sai dai har cikin ransa baya jin daɗin wasu abubuwan musamman yadda suke yawan kawo masa buƙatu idan ya biya masu kuma basu tattalawa, sam dangin dad ɗinsa ba su yi masa hakan, a gaba ɗaya familyn su bashi da wanda suka shaƙu sosai suke matuƙar ƙaunar juna irin Fahad, amman bai ta6a buɗe baki ya tambaye shi wani abu ba, haka ma sauran en familyn dad ɗinsa ba wanda yake tambayar sa kuɗi sai dai idan shi ya yi masu alkhairi, ko hajiya bata tambayar sa abu sai dai ta kawo masa shawarar ya yi ma wasu alkhairi cikin dangin dad ɗin sa idan da buƙatan haka, ko lokacin da zai baro funtua da ƙyar daddy ɗin su Fahad da momynsa suka amshi kuɗin da ya tura masu, duk da haka sai da daddy Sa'ad ya rage wasu ya mayar masa a cewarsa kuɗin sun yi yawa. Bayan wani lokaci ya sauke kansa ƙasa ya duba agogon da ke ɗaure a hannunsa, ya so a lokacin ya ziyarci Aunty Murja, sai dai ganin lokaci ya ja ya sa shi fasawa sai wani lokacin. Misalin ƙarfe ukku da rabi aka zo ɗaukar Deen zuwa babban stadium ɗin garin da anan ne za a yi gasar, ya shirya tsaf yana sanye da jersey ta club ɗin da zai wakilta, yadda aka shirya tournament ɗin iya clubs na cikin gida ne za su yi, amman daga baya wasu clubs na wasu jahohin suka shiga hakan ya ƙara faɗaɗa gasar. Ɗumbin mutane masoya ƙwallon ƙafa da ma waɗanda ba sa harkar ƙwallon kawai don su ga wasan Deen ne suka halarta, wasu mutanen ma daga wasu jahohin suka taso suka zo don su kalla, su kan su mashiryan gasar basu yi tunanin gasan zata yi haka ba, yayin da aka fara wasan ba ka jin komai sai hargowar