Sashe 117
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita don iyaye ba wasa bane, tuno irin alkhairan da suka yi masu ta shiga yi, Sophie mutum ce da har abada ba zata manta hallacin da ta yi mata ba a rayuwa kuma tana jin ta a ranta har yanzu, wanda yanzu ita Safiyyar tana a ƙasar Turkey inda ta yi karatu tana auren cousin ɗinta Lukman wanda ta zauna a gidan su, cikin tsananin 6acin rai mom Jameela ta ce, "Wallahi ki dai ji tsoron Allah Nailah, ki sani Allah baya bacci, aje a dawo watarana zai tona asirin abun da kika yi masa ne." Ɗan buɗa ido Nailah ta yi, da yanayin mamaki ta furta, "Wow! Dat's nice, aunty Jameela ke ce kike ce ma wani ya ji tsoron Allah!...hhhhh...to nima na ce Allah Ya tona ma kowa asirinsa and I dare you to say amin if you think ke ɗin you're a saint." Shiru mom Jameela ta yi tare da kawar da fuskarta gefe, Nailah ta tabe baki ta ci gaba da kur6ar lemunta, bayan ɗan lokaci ta miƙe mom Jameela ta maido idanunta kanta, "I need to use the bathroom." Kai kawai ta ɗaga mata, ta nufi hanyar part ɗin ta tana tafiya tana wani rausaya, mom Jameela ta bita da ido har ta shige, kauda idanunta ta yi ta bi wuri guda da kallo, tana sauraron zuciyarta da ke gargaɗinta kan Nailah, ta sani duk gidan su ba wanda ya kaita rashin kunya da iya rashin mutunci, so gara ta lalla6a ta su rabu lafiya. Bayan ta fito daga bathroom ɗin kai tsaye kitchen ta nufa, tun kafin ta shiga su chef Alima suka jiyo ƙamshin turarenta, kowannen su ya kai idon shi saitin ƙofa da sauri, daidai lokacin ta shigo ta tsaya daga bakin kitchen tana jifar su da kallon rashin arziƙi, duk suka shiga taitayin su, Alima ta nufo ta ta tsaya ɗan gefe da ita da ɗan murmushi ta yi mata sannu, ta tambayi ko tana buƙatar wani abu ne, tana yar yatsina ta ce mata suna da small chops? Chef Alima ta yi saurin cewa eh akwai tare da lissafo mata wanda ke akwai, ta faɗi wanda za a kawo mata falo tare da juyawa ta fita, Rashidat da tun bayan da ta shigo ta ƙame a wuri guda kamar wata soja ta ɗago bayan ta fita, chef Alima ta kalle ta tare da yin ƴar dariya ta ce, "Da alama kin tsorata da ita." Ta ɗan zaro ido ta ce, "Wllh sosai, da ta mare ni sai da na ga wani farin wuta fa...but she's beautiful." Alima ta jinjina kai tare da faɗin, "Very, very beautiful, ai duk ƴan familyn su suna da kyau gaskiya, amman duk kyaunta hajiya ta nan gidan tafi ta, kawai don ita wannan tana cikin ƴan matanci ne, ita kuma hajiya ta manyanta kuma ta haihu da yawa, but still kana gani ka san tafi wannan sis nata kyau." Rashidat ta ce, "Ni fa idanun hajiya ta nan gidan suna bani tsoro, suna yin kaman irin na matan da ke acting as snakes a movies, especially indian movies." Yar dariya Alima ta yi ta ce haka ne, itama shi ya sa da wuya ta kalli cikin idanunta, "Wai aunty Alima wannan ɗin duk nata ne?" Ta faɗa tana nuna saitin ƙugunta alamar tana nufin ƙugun Naila duk nata ne, Alima ta ce mata nata ne mana bata ga itama hajiyar gidan yadda take da su ba, Rashidat ta jinjina kai kafin ta ce, "Wasu in ka gan su sai ka ga kaman sune suka yi kan su wllh....Ah! tana jira a kai mata abu fa a falo..." Yadda ta ƙarasa maganar a zabure har sai da ya ba Alima dariya. "Yauwa gara da na tuna, ina son kuɗi ne." Nailah ta faɗa bayan ta ɗauko slice ɗin chocolate cake da fork ta kai baki, mom Jameela da ke kallonta ta ce, "Mi kuma zaki yi da kuɗi, ke da kika zo tare da alhaji mai arziƙi, na san ba ƙananun kuɗaɗe zaki samu a wurin sa ba." Bayan ta cinye cake din bakinta ta ce, "To kuɗi suna yin yawa ne? Ina da hidindimu da yawa da zan yi, kuma ina so idan muka je Dubai da baby zan yo siyayya, sannan ga iyalai na da nike son sallama kafin na tafi." Wani kallo mai kaman harara mom Jameela ta bita da shi, ta san da biyu don ta ƙunsa mata baƙin ciki ya sa ta kira Alhaji Mahmud da sunan baby, sharewa ta yi ta ce, "Wane iyalin gare ki? Na san dai ba su Ammi kike nufi ba." Tana wani murmushi ta ce, "Yea basu nike nufi ba, nima ina da nawa iyalin..." Shiru mom Jameela ta yi tana kallonta don ta fahimci inda maganar tata ta dosa, maganar kuɗin da take buƙata ta sake faɗa mata tare da adadin da za ta bata, mom ta ce, "Ni gaskiya yanzu bani da kuɗi har haka, ban daɗe da na ƙara gold ba." Wani kallon ban fahimce ki ba Nailah ta jefa mata ta ce, "Yanzu sai ya ke nan?" Ɗan jimm mom Jameela ta yi ta san muddin ba ta bata kuɗin ba baza a zauna lafiya ba, ƴar ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Bari zan kira Sapnah mu ji ko zan samu a wurinta. Amman duka fa ba a daɗe ba da Deen ya je ya baku kuɗaɗe masu yawa almost 100m fa, kuma har da ke a ciki." Tana yatsina ta ce, "Lokacin da ya je ina gidan ne? Kema dai kin san idan kuɗi suka shiga hannun Ammi fitar su sai hali, sai da ma muka sayar da hali sannan na tsira da 5m kawai." Fuska a turbune mom Jameela ke kallonta, sam bata yi mamakin maganar da ta yi ta saida suka sayar da hali da Ammi ba, saboda rashin mutuncin nata har akan iyayen nasu, "Yanzu dai ke nike jira don't keep me waiting, daga Dubai ɗin ma ina tunanin zan wuce Uk." Da sauri mom Jameela ta ce, "Mi zaki je yi can?" Tana mata wani kallo ta ce, "Bangane mi zan je yi can ba? Ina da sis uwa ɗaya uba ɗaya, ga ɗiyarta wadda idan da kara kamar tawa take, sai kuma har ki ce mi zan je yi?" mom Jameela ta ɗan yi jim tana kallonta sai kuma ta ce, "Ni dai pls in dai kin san zuwa zaki yi ki hana mata kwanciyar hankali kada ki je." Ta ɗan tabe baki ta ce, "Ya ina son in je in ga muradin raina zaki wani ce kada in je." Ta ƙarasa tana wani yin dariyar rainin wayou, shiru mom Jameela ta yi kawai, Nailah ta sake cewa, "Har yanzu su daughter Leemarh suna school ne? Na ga rana ya yi." mom ta bata amsa da sai ƙarfe shidda suke dawowa suna yin har da islamiyya, "Dad ɗin su fa?" Ta bata amsa da shima bai dawo daga aiki ba, Nailah ta ce, "An daɗe ban gan shi ba, ranan kaman zan yi masa magana ta chat sai kuma wani abun ya ɗauke man hankali, may be ya dawo ina nan mu gaisa." mom Jameela ta gyaɗa kai kawai, bayan sun ƙara yin ƴar hira mom Jameela ta miƙe ta ce mata za ta ɗauko wayanta a bedroom, tana shiga ɗakinta ta maida ƙofar ta yi locking nata da makulli, nufar gadonta ta yi ta zauna tare da kai hannu ta ɗauko wayanta da ke a saman side drawer, bayan ta ɗan lallatsa ta kara a kunne, magana ta fara yi da dad ɗin su Leemarh ta tambayi yaushe zai dawo, on the other hand ya ce mata da la'asar, ta yi ɗan jimm don la'asar ɗin ta kusa, ta ce "Ok, amman pls bani son ka dawo gida yanzu, ko ka wuce guest house kawai." muryarsa da alamun mamaki ya tambaye ta lafiya da bata son ya dawo, ta bashi amsa da lafiya lau kawai wata baƙuwa ce ta yi bata son su haɗu, yar dariya mai sauti dad ya yi cike da zolaya ya ce, "Hala budurwa ce ko bazawara, baki son in ganta ko na sama maki abokiyar zama." Ta wani ɗaure fuska ta ce, "Da yake abun da ke a ranka ke nan ko, to ba wannan ne dalili ba, wata friend ɗina ce wadda mijinta ya rasu, kwanaki ba na baka labarinta har ta nemi in tallafa mata saboda an barta da marayu tana da yara ukku, wadda har na faɗa maka game da ita ka bada kudi na bata." Ya ɗan yi jimm alamar tunani kafin ya ce mata ya manta cause mutanen da yawa, ya tambayi yanzu to mi ya faru, ta ce, "Ita ce wai kuma ta zo tana neman wani tallafin, tana ta wani lissafo buƙatun yaranta sai ka ce basu da dangin uba, shine na ce mata ka yi tafiya." Ya ce, "Ok na fahimta, amman ai da an tallafa matan tun da ko ba komai friend ɗin ki ce, kuma kin san yadda nauyin kula da yara yake, sannan ba lallai idan dangin mahaifin nasu suna kulawa da su ba." Fuskarta a ɗaure ta ce, "Kai baka san irin mutanen ba, wani lokacin kawai rashin godiyan Allah ne da iya maula, kai da ka ganta ka san basu wani cikin hali tun da har aiki fa tana yi, yanzu da an ƙara tallafa mata to an sake bata daman da za ta ƙara dawowa ne." Ya ɗan sauke gajerar ajiyar zuciya ya ce ya fahimta tare da tambayar ta yanzu to har sai yaushe zai dawo gidan, ta ce zata kira sa a waya idan ta tafi, ya amsa da ok tun da hakan take so, cire wayar ta yi bayan sun gama, ta zuba ma wuri guda ido ta haɗe rai, ba wai tana zargin Nailah ɗin bane kan mijinta, kawai ta ji bata son ya dawo ya ga Nailah da wannan ƴar iskar shigar da ta yi, ko ita da take mace sai da shigar ta ɗauki hankalinta balle kuma namiji, a yadda yanzu duniyar ta lalace fitintinu suka yi yawa komai zai iya faruwa, ta ƙarasa tunaninta tare da ɗan girgiza kanta, kamar ta kira Sapnah ta sanar mata